Tantin 'yan gwagwarmaya da ɗalibai masu zanga-zanga a Jami'ar George Washington University

Daga Moataz Salim

Yayin da ɗalibai a faɗin Amurka ke komawa makarantu a kakar bana, ɗalibai da yawa suna fuskantar sabbin takunkumAi a ɓangaren 'yancin yin taro, da zanga-zangar lumana da bayyana ɓacin ransu da jami'o'insu da ke goyon bayan Isra'ila.

A tsakiyar birnin Washington, DC, jami'ar da nake tana tsaka da cin zarafin ainihin manufofin 'yancin tofa albarkacin baki, wanda ta daɗe tana ɗaukakawa.

Ƙarƙashin jagorancin shugaba Ellen Granberg, Jami'ar George Washington University (GWU) ta fara harar ɗalibai masu gwagwarmaya kan Falasɗinawa, da Larabawa da Mususlmai. Wannan jami'a, wanda ke iƙirarin zama tushen 'yancin masu karatu, a yanzu ta koma cibiyar da ke muzanta waɗanda ke zanga-zanga kan kisan ƙare-dangin da ke afkuwa a Gaza.

Abin da jami'ar GWU ta yi zuwa yanzu ya haɗa da kame tarin mutane, da dakatar da reshen ƙungiyoyin Ɗalibai Masu Kare Adalci a Falasɗinu ta SJP, da Muryar Yahudawa Masu Son Zaman Lafiya ta JVP. Kuma suna ɗaukar matakin ladabtarwa kan ɗalibai ciki har da ni.

GWU na goyon bayan Isra'ila

Ta hanyan abin da take, jami'ar ta nuna matsayarta game da kisan da ake kullum, da ynwatarwa, da ƙasƙantar da Falasɗinawa da Isra'ila mai ra'ayi Zionism take yi. Ƙin da Jami'ar GWU ta yi na cire hannun jari daga kamfanoni da ke da hannu wajen ba da kuɗin makamai aikata wannan kisan ƙare-dangi ya ƙara nuna goyon bayanta ga Isra'ila.

A watannin baya-bayan nan, mutuncin jami'ar a fannin samar da yanayi da ba ya muzgunawa da nuna wariya kan al'ummata, ya ƙara ƙazanta.

A farkon wannan wata, Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulman Amurka Council on American-Islamic Relations (CAIR), ta ayyana jami'ar GWU a matsayin "cibiya da ke da babbar matsala" saboda muzgunawa "Falasɗnawa, Musulmai, Larabawa, Yahudawa, da sauran ɗalibai, malamai, da ma'aikata" waɗanda ke adawa da kisan kiyashin da ake wa Falasɗinawa a Gaza.

A wannan rahohon, CAIR ta ba da cikakken bayani kan yaɗuwar take 'yancin magana da kuma ƙaruwar nuna wariya ga Falasɗiwa da ƙyamar Musulunci cikin jami'o'i a jihohi 30 na Amruka, inda jami'ar GWU ta zo kangaba cikin ukun farko wajen zama "mafi munin halayyar ta da hankali" da ita da jami'ar Emory da UCLA.

Yanayin da ake ciki a jami'ar GWU ya yi ƙamari sosai har ta kai Daraktan Bincike da Raji ta CAIR, Corey Saylor, ya gargaɗi ɗaliban da ke son shiga jami'a su duba wasu makarntun daban, inda ake da 'yancin faɗbin ra'ayi kuma ake mutunta 'yancin ɗalibai.

Tsawaitar wariya

Wannan ba sabon abu ba ne. Tun kafin zanga-zanga kan Gaza, jami'ar GWU tana da mummunan tarihi na ƙuntatawa Falasɗiwa. Ranar 11 ga Mayun bara, Ma'aikatar Ilimi ta Amurka ta fara bincike a hukumance kan ƙorafi kan dokar Title VI, wanda ake zargin jami'ar GWU ta nuna wariya kan ɗalibai Falasɗinawa.

Sannan a Nuwamban 2021, ƙungiyar Palestine Legal, wadda ke rajin kare mutane da ke goyon bayan haƙƙin Falasɗinawa, ta kai ƙorafin taka haƙƙin jama'a a jami'ar GWU saboda jami'ar ta soke tsari mai kyau ga ɗalibai Falasɗinawa da sashenta na Ofishin Gwagwarmaya bayan da ƙungiyar Hillel, mai kare Israila a jami'a ta shigar da ƙorafi.

Sokewar ta haramtawa ɗalibai Falasɗinawa, ya samu rauni yayin da yake karatu daga Gaɓar Yamma, damar samun tallafin lafiyar ƙwaƙwalwa bayan gamuwa da bala'i.

Cikin awa 24 da tallata yanayi mai kyau, manyan jami'ain jami'ar GWU sun saka baki inda suka rufe ta, wanda ya bayyana tsabagen rashin daraja walwalar ɗalibanta Falasɗinawa.

A wani misali a bara, Dr. Lara Sheehi wani tsohon farfesan ilimin ƙwaƙwalwa a jami'ar GWU an kai masa hari, a wani taron kan intanet da ɗalibai masu son Isra'ila saboda kare haƙƙin Falasɗiwa.

Ina ajin da Sheehi yake koyarwa lokacin da ɗalibai da dama da suka yi maganar nuna tsanar Falasɗinawa, kamar alaƙanta duka Falasɗinawa farar hula da sojin Isra'ila suka kashe da cewa 'yan ta'adda ne. Amma ba a ji labarin wani hukunci kan masu maganganun.

Irin wannan yanayi na ƙiyayya da rashin haƙuri da jami'ar GWU ta bari yake yaɗuwa ba abin da za a ƙaryata ba ne.

Tantin masu zanga-zanga kan Gaza

A Afrilu, ɗalibai sun kafa tantuna don Gaza, inda suka buƙaci jami'ar ta soke zarge-zarge da aka ƙala wa ɗalibai masu shirya tarukan goyon bayan Falasɗiwa; ta kare 'yan maganar nun son Falasɗiwa a jami'a; ta cire hannun jari daga kamfanonin da ke sayar da fasaha da makamai ga gwamnatin Isra'ila; kuma nan-take ta fito da bayanan duka waƙafi da zuba jari; kuma ta kawo ƙarshen haɗn-gwiwar kartu da Isra'ila.

Maimakon amsa buƙatun, Shugabar jami'ar Granberg da hukmar jami'ar ta zaɓi kawo jami'an 'yan sandan birnin DC, tare da taimakon Magajiyar garin DC Muriel Bowser, inda suka kai farmaki kan tantunan.

Farmakin 'yan sandan ya yi muni, kuma ɗalibai Falasɗinawa da Musulmai su aka fi gallazawa. Ni kaina ɗan sanda ya buge ni kuma an fesa min barkonon tsohuwa lokacin da ake tarwatsa mu.

'Yan sanda sun kuma raunata sauran ɗalibai da jama'ar gari kuma sun fesa musu barkono. A yayin wannan farmaki, jami'ar GWU ta aika bayyanannen saƙo: ta zaɓi amfani da ƙarfi kan ɗalibai, maimakon cire hannun jari daga kamfanonin da ke da hannu a kisan kiyashi.

Baya ga wannan tsagerancin zaluncin, tun da fari jami'ar GWU ta haramta wa ƙwararru da masu sa ido kan shari'a ka da su isa ga wajen, inda suka illata tsaro da 'yancin mutanen da ke wajen.

Bayan farmaki kan tantunan, jami'ar GWU ta kekketa tabarmun sallah na ɗalibai da kuma Ƙur'anin mai fassara, wanda ke nuna tsabagen raina 'yan addini na ɗalibanta.

An kame mutane 33 yayin wannan mummunan farmaki, har da aƙalla ɗaliban GWU takwas, da tarin ɗalibai daga wasu jami'o'in da ke yankin birnin DC da jihohin Maryland da Virginia, da sauran al'ummar gari.

Da yawa suna fuskantar hukuncin shari'a ƙarƙashin jami'ar — "haramta shiga" jami'a na tsawon wata shida, wanda ke hana su shiga ɗakunan karatu da na cin abinci, da ma jirgin ƙasa.

Baya ga laifukan da ake zarginsu, ɗaliban suna fuskantar ladabtarwa daga jami'ar, wanda ke ƙara nuna rashin tausayin jami'ar GWU da salon azabtarwa kan wanda suke adawa da hannunta a kisan ƙare-dangi.

Bayan kame mutanen, Mara Verheyden-Hilliard, babban daraktan ƙungiyar Partnership for Civil Justice Fund, wanda ƙungiyarsa take wakiltar aƙalla ɗalibi guda, ya faɗa a wata sanarwa: "Ƙarar sun saɓa wa hankali game da zanga-zanga … siyasa ce tsagwaranta wadda manufarta shi ne toshe bakin ɗalibai saboda sun yi adawa da kisan kiyashi a Gaza."

Mark Goldstone, wani lauyan da ke wakiltar ɗalibai da yawa, ya yi tir da hukuncin haramta shiga jami'a, lokacin da yake magana da jaridar Washington Post "ya yi tsauri, da faɗ, kuma babu hujja."

Ana ci gaba da danniya

Saboda tsoron sake faruwar zanga-zangar neman cire hannun jari, ranar 21 ga Agustan 2024, GWU ta dakatar da reshen ƙungiyoyin ɗalibai na Students for Justice in Palestine (SJP) da Jewish Voice for Peace (JVP). Wannan danniyar da hana saɓa ra'ayi wani misali ne na aniyar jami'ar ta rufe bakin waɗanda ke magana kan hannu jami'ar a kisan kiyashi.

Ina tuna yadda na ji jami'ar ta yi watsi da ni, saboda nuna ko in kula da kin yarda da hannunta a kisan ƙare-dangin da ake wa jama'ata, da kuma shirun da malaman jami'a da sauran ɗalibai suka yi.

Na rasa 'yan uwa 161 sakamakon kisan kiyashin Gaza. Saboda gwagarmayata kan Gaza da Falasɗinu, 'yan sanda sun muzguna min bisa umarnin jami'ar GWU.

Yayin da nake rubuta wannan, ina fuskantar shari'a duk da cewa na yi hutu har zuwa watan Janairu. Yunkurin jami'ar na danne muryoyin daliban Falasdinawa ba zai yi nasara ba.

Duk da matakan da suka dauka na ladabtarwa, dalibai da al'umma sun yi maci a harabar makarantar GWU a wannan watan domin nuna cewa ba za a yi shiru da yakin neman adalci da kawar da kisan kare dangi ba.

Shawara don gaba

Ba a bayyana abin da zai biyo baya ba, amma abu daya ya tabbata: daliban da ke GWU, kuma watakila wadanda har yanzu ba a kai ga daukar matakin hukunta su ba, za su ci gaba da matsa wa jami’ar lamba kan ta daina kawar da kai daga kisan kare dangi mulkin mallakar 'yan kama wuri zauna.

Daruruwan al’umma ne suka halarci wannan sabon gangamin, wanda ke nuni da cewa al’ummar DC da yankin DMV da ke yankin na cikin kulle-kulle tare da daliban da ke fafutukar ganin an kawar da su daga kisan kiyashi.

Duk da kyakkyawan fata na a wannan yakin, na bar muku da gargadi: Ga Falasdinawa, Larabawa, da dalibai Musulmai suna la'akari da GWU a matsayin zabi na iliminsu, shawarata mai sauƙi ce: kada ku yi. GWU wuri ne mai haɗari ga waɗanda suka kuskura su yi magana game da rashin adalci.

Munafuncin jami'ar, da watsi da ka'idojin 'yancin fadin albarkacin baki, da hadin kai wajen kisan kare dangi, sun sanya ta zama wani yanayi mai ƙyama ga duk wani dalibi mai kima da kuma hakkin dan'adam.

Marubucin, Moataz Salim babban ɗalibi ne ɗan Falasɗinu daga Gaza da ke birnin DC Gaza, wanda ke gwagwarmayar kawo karshen kisan ƙare-dangi da 'yantar da Falasɗnawa. Ya fara aiki da CODEPINK tsawon wata 3 don zama muryar al'ummarsa. Kuma ya shiga harkar gwagwarmaya a jami'a da cikin al'umma, inda ya ba da wata 10 don ƙwato 'yancin Falasɗiwa.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar tunani ko ra'ayoyin tsarin iditocin TRT Afrika ba.

TRT World