Rasha da Afrika ta kudu suna da kyakkyawar dangantaka / Hoto: AP

Daga Elsie Eyakuze

Yayin da yakin da ake gwabzawa a Ukraine ya shiga shekara ta biyu, an yi ta muhawara akai-akai kan wannan batu tsakanin mutanen da dama da nake abota da su a shafukan sada zumunta na yanar gizo.

Ire-iren wannan gardama kan ja layi mai karfi game da wane bangaren ne ‘mai gaskiya’ a cikin wannan rikici, lamarin da bai dace ba.

An yi ta amfani da kalmar 'yakin basasa’ tsakanin manyan kasashe biyu sosai a 2022. Masanin tattalin arziki Jeffrey Sachs ya yi tashe a watan Maris sakamakon yadda ya bayyana ra'ayinsa game da manufofin Amurka da yanayin siyasar China.

Afirka ta Kudu da ke kusa da gida ta ‘dan ja hankali lokacin da ta halarci atisayen hadin gwiwa na sojin ruwa da Rasha, inda jama'a da dama suka nuna goyon bayansu.

Rashin tsayawa a tsaka-tsaki na kasar Sin da Indiya da ya yi ta tasowa, amma ba sosai ba.

Wadannan tattaunawar da nake magana a kansu duk a tsakanin ’yan Afirka ne, duk da cewa yakin da ke faruwa a Ukraine ya yi nisa da yankin Arewacinmu.

Nisan da har wasu ke raha cikin duhun kai da cewa mun tsira idan har lamarin ya kai ga matakin amfani da makamin nukiliya.

Wannan ba gaskiya ba ne, amma yana haifar da damuwa game da hadarin da ke tattare da rikice-rikicen da ke faruwa.

Yakin da ke tsakanin Rasha da Ukraine ya haifar da tashe-tsashen hankula\ Hoto: AFP

Duk wadannan maganganu suna bayyana ne saboda yankin Afirka da al'ummarta su ma suna fama da yakin basasa.

Tambaya kan mene ne illar da yakin Ukraine ke da shi a kanmu, shi ne abin da muke cigaba da tattaunawa akai, fiye da abin da ke faruwa a Afghanistan da Iran da har da watakila kasar Kongo.

Idan aka zo batun huldar kasa da kasa, kasashen Afirka biyu kawai ake samu. Akwai Afirka da nake kira gida, kasa mai fadi da ke cike da tsarin al'adu da yanayin muhalli da harsuna da gogewa.

Ta kunshi mutane 'yan uwa da abokan arziki da masu sha'awar kwallon kafa da kuma masu bayyana damuwa game da tsadar man fetur da ke shafar al’amuran kasuwanci na yau da kullun.

Sannan kuma akwai Afirka ta labarai da tattalin arziki da "dangantaka masu muhimmanci," wanda shi ne abin da aka fi gabatarwa.

Ana danganta kasata bisa ga ma’aunin kudaden shiga na GDP na kowane mutum, ko abin da ya ajiye na ma’adinan tanzanite ko zinare da kadadar filayen noma da kuma irin manyan gidaden da mutum ke da su a bakin teku.

'Albarkatu' shi ne kalmar da ake amfani da ita. Afirka tana da wadata a “albarkatun kasa” masu tarin yawa, kuma albarkatu suna cin karo da son zuciya iri daban- daban

Duk Lokacin da na ji ana yawan magana game da albarkatun Afirka da kalmar da ake hada su tare, "mai yiwuwa", ba tare da jin labarin 'yan Afirka da kansu ba, wani karin magana ke zuwa min zuciya: kasashe ba su da abokai; mabukata kawai suke da su.

Arzikin Mai da iskar gas na daga cikin albarkatun da Afrika ke da su da ke matukar janyo hankulan kasashen Turai zuwa nahiyar\ Hoto: Getty

Tarihin Afirka ya kasance misali na hakika kan wannan lamarin tun shekaru aru-aru, ko a cikin batun da ke cewa ‘nahiyar Afirka na habaka,’ ina tsammanin muna da masaniya kan cewa har yanzu wannan muradi ya dara dangantaka ta kawance da ke janyo iko wajen sarrafa albarkatun kasa ta hanyar saka hannayen jari daga kasashen waje.

Ko kuma tsoma bakin kasashen waje da ke zama wani bangare a zahirance a wannan zamani ga al'ummar da ake hako arzikinsu akai-akai.

Don haka wadannan abubuwan da aka ambato a sama sun bayyana yadda yakin Ukraine ke fayyace abin da ya kamata a yi la’akari da shi dangane da cigaban Afirka. Wasu dangantaka kamar irin kasashen Turai da Amurka an fahimce su.

Ko da a ce mulkin mallaka ya zama al'ada a wannan zamani, an gina shi ne a kan mulkin daular da ta gabata.

China ta nuna kanta a matsayin kasa wace ta fita daban wajen tsayawa da kafafuwanta.

Ta hanyar musayar lamuni mai karamci sannan tana da wadatattun filaye da manyan ababen more rayuwa a kasashe da dama, wanda hakan ke zama barazana da kuma rage ikon kasashen da suka yi wa wasu kasashe mulkin mallaka.

Har ila yau, yadda kasar China ke tafiyar da yankunan da take dauka nata, ya sanya ayar tambaya game da rashin burinta na sarauta.

Indiya, wacce ke da tasiri ta kowane fanni da alama ta gamsu da dangantakar tattalin arziki da ta dora kan harkokin kasuwanci da ayyuka da take yi, lamarin da ya nuna cewa ba ta fuskantar wata barazana ko kadan.

A cikin makon nan ne dai ta sanar da kulla huldar kasuwanci da kudin Rupee da kudaden cikin gida na kasashe da dama, yunkurin da ya matukar rage karfin dalar da Amurka ke da shi a tattalin arzikin duniya.

Mataimakiyar Shugaban Amurka tare da shugaban Afrika ta Kudu

Wani batu da ya bayyana karara a shekarar 2023 shi ne yadda ake gasa da kokarin samun sauyin kasashen da suke da karfin fada a ji a duniya.

Lamarin dai ko shakka babu na nuna cewar kai tsaye ana kalubalantar matsayin Amurka sannu a hankali, daga kasashen da suke neman yin kafada da kafada da ita.

Wannan batu dai ya shafi hatta kasashe masu karamin karfi musammman na nahiyar Afirka, da suke da alaka da manyan kasashen na yanzu, inda baya ga zuba jarin da kasashen China da Indiya ke yi.

A halin da ake ciki an samu wasu daga cikin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da suke zuba hannun jarin na su a kasashen na Afirka wadanda kai tsaye suke da alaka da addini da al'adu, ko kuma alakar kasuwanci kadai

A bisa al’ada dai, kowace kasa na maraba da samun damar fadada abokan huldarta na kasuwanci. Sai dai akwai a kan samu shakku dangane da kulla sabbin yarjejeniyoyi saboda nazarin abinda ka je ya zo.

Ana daukar Afirka a matsayin nahiya mafi talauci da kaskanci a duniya ta fuskar siyasar kasa da kasa, duk da cewar nahiyar ta kasance mai wadatar albarkatu tare da matasa, gami da karuwar yawan jama’a cikin sauri. Lallai muna sane da wannnan kalubale.

Irin wannan wayar da kan jama'a na taimaka wa wajen kara ilimantar da matasa.

Ana kuma samun karin yunkuri na damuwa da halin da ake ciki domin cigaban kasashe da ma nahiya gaba daya, musamman a yankin kudu da Hamadar Saharar Afirka.

Wani batu da ke daukar hankali kuma shi ne yadda rarrabuwar nahiyar zuwa yankin kudu da Sahara da kuma yankin Sahel ya haifar da kalubale ga batun hadin kan kasashen nahiyar.

Duba da sarkakiyar alaka da kasashen Afirka ke da ita tsakaninsu da sauran kasashen duniya, a halin yanzu akida ba batu ba ne mai muhimmanci. Ko da yake yana iya ma zama abin muhawara musamman a tsakanin masu ra’ayin rikau, na ‘yan mazan jiya ko kuma masu sassaucin ra'ayi.

Abubuwan da ya kamata afrika ta Yi amfani da su maimakon imanin da kasashen afrika ke da shi dangane da tsare taren su, dalilin da ya sa afrika ke daukan bangare, musamman abinda ya shafi rikicin cikin gida da salon tafiyar da mulki zai iya bayar da sakamako mai ban mamaki

Idan da Afrika zata fifita Afrika fiye da saura da duniya zata daukaka manufarta fiye da yadda ake gani a yanzu,

Wannan shi ne abinda Shugaban Ukraine Volodymyr zelensky ya gano shi ne dalilin da ya sa aka hana shi gabatar da jawabi a taron kungiyar Afrika AU.

Kuma hakan manuniya ce a yadda aka yi ta samun mabanbantan ra'ayoyi daga kasashen Afrika a zaman zauren majalisar dinkin duniya a kan Rasha, da kuma yadda wasun su suka rungumi matakin kaucewa nuna bangaranci.

Dalilin dake Kara gasgata kalaman na sugaban a kan su.

TRT Afrika