Afirka ta kafa tushen samun ci gaban zamani. / Hoto: AP  

Daga Mengesha Michael

Wani ɗan jarida kuma mai aikin bincike Henry Morton Stanley daga yankin Welsh ya yi wa Afirka lakabi da "Nahiya mai cike da Duhu" kana ya bayyana nahiyar a matsayin wacce ke cike da mamaki.

Ba kowa ba ne yake da masaniya kan yankuna da al'adunta masu yawa musamman ma wadanda suka fito daga kasashen wajen har sai da aka kai ƙarshen ƙarni na 19.

A mafi yawan lokuta akan ba da tarihin labarin Afirka da nahiya da ke cike da yaƙe-yaƙe da wahalhalu da gwagwarmaya, sai dai akwai tarin wasu labarai da ba a cika faɗarsu ba.

Duk kuwa da cewa Afirka na riƙe da tarihin nasarorin fasahar ɗan'adam mafi daɗewa a duniya wanda ya shimfida gagarumin jigo a ci gaban fasaha.

Yana da muhimmanci a san tarihin Afirka da kuma amfani da damarmakinta da ba a taɓa su ba don samun kyakkyawar makoma yayin da muka tsunduma cikin tafiyar ci gaban duniyarmu ta fuskar zamani.

Tsohuwar hikima

Tun a zamanin farko, Afirka ta kafa tushen wayewar ɗan'adam.

Kakanninmu na tsofaffin al'ummomin Afirka su suka fara ƙirƙirar abubuwan da har yanzu suke da muhimmaci a wannan lokaci.

Idan aka yi la'akari da ƴan Masar waɗanda suka ƙirƙira littattafan ilimin lissafi da ke ɗauke da dabaru da har yanzu suke da mahimmanci ga tsarin iliminmu.

Iliminsu na juzu'i da tsarin dabarun lissafi da fahimtar lissafin algorithmic kamar pi da hazakar gine-gine kamar na ginin dala duk sun bayyana tarin basirar Afirka da ci- gaban kere-kere da fasaha tun a shekarun da suka gabata.

Afirka ta kasance gidan farkon ga misalan ilimin taurari da lissafi.

Watakila ginin farko da mutum ya yi, shi ne da'irar dutsen kalandar ɗan Adam a Afirka ta Kudu.

Kimanin shekaru 44,000 da suka gabata, ana amfani da sanduna da ƙasusuwa da aka tara a madadin na'urorin issafi.

Kazalika, al'ummar Dogon na kasar Mali sun kasance masu zaburarwa a fahimtarsu ta sanin sararin samaniya, wanda har zuwa yanzu ke zama kalubale ga fahimtar zamani.

A wasu sassa na daban, kamar na noma da na likitanci, ana daukar Afirka a sahun gaba.

A fannin magunguna da ire-iren tsiran gargajiya na Afirka da ake amfani da su a zamanin da a yanzu haka sun samu karbuwa daga likitocin wannan zamanin kuma ana ci gaba da amfani da su.

Al'ummar Akan da ke yankin yammacin Afirka sun yi nasarar samun ilimin allurar rigakafin cutar sankarau.

Boyayyen gado

Sabanin wasu ra'ayoyin da suka sha ban-ban, kafin zamanin mulkin mallaka Afirka ta kasance babbar cibiyar ƙirkire-ƙirkire.

Bazuwar manyan ayyukan noma da dabarun aikin ƙarafa da kuma tsare-tsare gine-gine masu daukar hankali, kamar kere-keren kwale-kwale da mutanen Mali da Songhai su ke yi.

Kwale-kwale da kan iya jure kifewa cikin teku waɗanda suka yi daidai da girman kwale-kwalen Viking, suna da matukar mahimmanci wajen kamun kifi da kasuwanc da sadarwa a iyakar bakin tekun da koguna.

Duk da waɗannan ci gaba da aka samu a lokutan baya, zamanin mulkin mallaka ya haifar da wani rikitacciyar yanayi a sauyin da aka samu na fasaha.

An gabatar da ayyukan fasahohi kamar na telegrap da hanyoyin jiragen ƙasa da jiragen ruwa da kuma bindigogi.

Amma akan yi amfani da waɗannan fasahohi ne cikin dabaru kuma galibi akan yi amfani da su wajen janyo tsaiko ga ci gaban ƴan asalin ƙasar.

Samun waɗannan fasahohi na waje ya kawo cikas ga al'adun gargajiya, wanda ya haifar da rikice-rikicen zamantakewa da na tattalin arziki.

Yayin da zamanin mulkin mallaka ya shaida kafuwar wasu fasahohi, dukka tasirin hakan ya haɗa ire-iren sata da barna da kuma daukar wasu hanyoyi wadanda suka share fage ga tarin matsaloli da damammakin da aka yi ta fuskanta a zamanin mulkin mallaka.

Bayan samun 'yancin kai, Afirka ta fuskanci ƙalubale da kuma damammaki, wadanda suka yi tasiri a fagen fasaha.

Bayan mulkin mallaka, sabbin kasashe masu cin gashin kansu sun tsunduma cikin gina ingantattun ababen more rayuwa da fasahar kere-kere.

Kasashe da dama sun samu gagarumin ci gaba wajen inganta fannin ilimi da kirkire-kirkire, tare da samar da kwararru masu hazaka.

Ko da yake, rarrabuwar kawuna a fannin tattalin arziki da rashin zaman lafiyar siyasa sun haifar da cikas ga yaduwar ci gaban fasaha.

A 'yan shekarun nan, yayin da ci gaba ta bayyana, magance batutuwa kamar rabuwar fasahar zamani da kuma tabbatar da an samu damar amfani da fasaha duk sun kasance muhimman aikin da ke gaba wajen buɗe mukulin damammakin fasaha a Afirka.

Tsarin ci gaban fasaha na ''Leapfrogging''

Tsarin Leapfrogging yana nufin haɓaka ci gaba ko tsallake tsoffin matakan ko na al'adun ci gaba fasahohi.

Ci gaban fasahar Afirka shaida ce ga irin gagarumin tsarin ci gaban fasaha.

'Ya zuwa shekarar 2021 an samu yaduwar wayar salula a yankin kudu da hamadar Sahara da kusan kashi 46 cikin 100/ Photo: Reuters

Tafiyar nahiyar, musamman ta fuskar sauye-sauyen fasahar zamani kamar fasahar wayar tafi da gidanka, na nuna fikirar samun ci gabanta fiye da matakanta na ci gaban gargajiya.

Yayin da amfanin wayoyin zamani na tafi da gidanka suka ɗaɗa yaduwa, hakan ya kuma taimaka wa sauran masana'antu waɗanda ke shirin samun haɓaka ta fuskar tattalin arziƙi.

Bisa kididdigar ma'unin leadfrog a Afirka wadda ta tantance tsarin tattalin arzikin fasahar zamani, kasashe Kenya da Afirka ta Kudu ne ke kan gaba a sauyin tsarin fasahar zamani, sai Nijeriya da Masar da Rwanda da kuma Habasha wadanda ke biye musu.

Kowace ƙasa daga cikinsu dukka na da nata ƙarfin da kuma ƙalubale na musamman akan tafiyar fasahar zamani.

Kenya da Afirka ta Kudu suna da burin haɓaka wasu sassa na musammam kamar ƙirƙirar ayyukan fasaha don samun damar gasa a kasuwannin duniya.

A na su bangaren Ƙasashe, suna mai da hankali ne wajen haɓaka ginshiƙai kamar gina abin dogaro da samar ingantattun ababen more rayuwa da kuma dogaro kan ƙudaden da ake biya na fasahohin zamani da samar da ayyukan gwamnati na fasaha, da samun damammaki ta intanet da inganta ƙwarewa da zuba hannyen jari a fannin wutar lantarki da kuma intanet

Riba da rashin amfanin sauyin fasaha a Afirka

Wataƙila abu mafi mahimmanci a cikin wannan sauyi da aka samu shine yunƙurin Afirka na rungumar canji.

Ba kamar sauran bangarorin tattalin arziki da aka kafa ba, Afirka ta yi marhabin da fasaha, musamman kuɗaɗen wayar hannu, wanda ke ba nahiyar damar tafiyar da ci gaban tattalin arzikinta.

Sauyi ya haifar da gagarumin ci gaba cikin sauri, a manhajojin bankuna ta wayar hannu da ya kawo sauyi a tsarin hanyoyin samun makamashi da ke haskaka gidaje da na kiwon lafiya da aikin gona tare da dorewar wasu hanyoyin.

Hakan ya samar da guraben ayyukan yi tare da bunƙasa ci gaba da buɗe hanyoyin kasuwann da farashi, da dai sauransu.

Duk da haka, a wuraren da aka fara samun kamfanoni masu tasowa kamar a Afirka, 'yan kasuwa ba su da wani abin jin daɗi za zai kawo musu cikas ko ya haifar da hargitsi saboda babu wasu masana'antu da aka kafa da za su yi haka.

Yayin da ci gaba ta bayyana, yana da mahimmanci a yi la'akari da matsalolin zamantakewar tattalin arziki da rashin shugabanci a Afirka.

Kazalika waɗannan ƙalubalen sun haifar da batun yawan fitar ƴan Afirka zuwa wasu kasashe don samun rayuwa mai inganci wanda hakan ke barazana ga tarin al'barkatun Afirka.

Domin yin amfani da basirar jama'arta, dole sai Afirka ta mayar da hankali kan bunkasa tattalin arzikinta da kiwon lafiya da aikin noma da samar da ababen more rayuwa da kuma tsarin mulkinta don hana kwararru masu hazaka yin hijira don samun ingantacciyar rayuwa da dama a kasashen waje.

Hasashen abubuwan da ke gaba

Ci gaban Afirka a halin yanzu ya sanya ta a matsayin kasuwar da ba a iya amfani da ita ba, kuma masu zuba jari tabbas suna kallon nahiyar a matsayin sarari na kirkire-kirkire da habakar fasahohi

ƙasar Kenya da Afirka ta Kudu da Nijeriya da Masar da Rwanda da kuma Habasha ne suke jagorantar sauyin fasahar zamani bisa ga ma'aunin Leadfrog na Afirka. Hotuna: Hotunan Getty

Tabbas kamfanoni masu zaman kansu za su samar wa Afirk ci gaba a yayin da nahiyar ke ci gaba da sauya tsarin a lokutan da suka dace.

Haɓaka haɗin gwiwar tsakanin Afirka da fitattun ƙasashen kungiyar BRICS ya ba da fa'idodi masu ban sha'awa ga ci gaban tattalin arziki da fasaha, waɗanda suka haɗa da yarjejeniyoyin gina makamashi mai ɗorewa da masana'antu da ayyukan noma da ingantattun tsarin hukumomi da kasuwanci, da kuma haɗin gwiwar wasu bangarori daban-daban.

Wannan yana nuna yadda nahiyar ke saurin samun karbuwa da kuma himmarta ga tsarin ci gaban tattalin arziki .

Marubucin, Mengesha Michael ɗan jaridar Eritrea ne sannan kuma ɗan kasuwa kana marubuci mai zaman kansa kuma mai ƙirƙirar shirye-shirye.

Togaciya: Ra'ayi da marubucin ya bayyana ba dole ba ne ya zama daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.

TRT Afrika