Daga Kristian Alexander
Akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin lafiyar hankali da yaƙi, kuma hakan yana tasiri sosai kan mutanen da suke cikin yanayin yaƙin har ma da waɗanda ke kallon abin da ke faruwa daga wasu wuraren nesa da inda ake rikicin.
Munanan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza da kuma tsawon lokacin da aka ɗauka ana hakan wanda ke ritsawa da fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba, na yin mummunan tasiri a kan lafiyar ƙwaƙwalwar al'ummar.
A wani rahoto na ƙungiyar agaji ta Save the Children mai cibiya a Landan, wacce take kare hakkokin yara, an bayyana irin mummunan yanayin lafiyar ƙwaƙwalwar da yaran Falasɗinu ke fuskanta sakamakon illar da yaƙin ya jawo musu.
Binciken mai taken 'Tranpped: The impact of 15 years of blockade on the mental health of Gaza’s children’ wato 'Tasirin da ƙawanyar shekara 15 da aka yi wa yankin Gaza ke yi a kan lafiyar ƙwaƙwalwar yaran yankin', ya yi cikakken bayani kan illar da wannan takurar da aka yi wa Gaza tun shekara ta 2007 ke yi kan rayuwar yaran, da kuma yadda yanayin lafiyar ƙwaƙwalwarsu ya taɓarɓare sosai.
Dage takunkuman da ƙawanyar zai rage tashin hankali da fargabar da waɗannan yara ke ciki, amma duk da haka ana buƙatar wasu abubuwan don sake gina tsarin da zai taimaka musu wajen shawo kan yanayin fargaba da suka samu kansu a ciki tsawo lokaci.
Mummunan yanayi
Wata maƙala da aka wallafa a cikin mujallar World Psychiatry da ya yi bayani a kan illar yaƙi a kan lafiyar ƙwaƙwalwa, an gano cewa "batun yaƙi yana da muhimmanci sosai a tarihin ɓangaren lafiyar hankali ta hanyoyi da yawa."
Ana bayyana firgicin da mutane ke shiga sakamakon yawan jin ƙarar bama-bamai a matsayin cutar (PTSD), kuma yana ɗaya daga cikin matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa da ke shafar mutanen da ke rayuwa a yankunan da ake rikici.
Alal misali, a Gaza mutane na yawan kasancewa cikin fargaba sakamakon yawan jin ƙarar jiniya da fashewar bama-bamai da harbe-harbe.
A kowane minti sai an samu iyalan da suke tserewa. Sukan shiga cikin hadarin yaƙi ko kuma a lalata musu gidaje. Wannan yaƙin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa yana haifar da haɓakar sinadaran damuwa irin su cortisol, waɗanda ke da mummunan tasiri a kan yadda mutum yake yanke shawara. Fargaba da tsananin damuwa ta yau da kullum su ne cututtukan da suka zama gama gari tsakanin waɗanda suke cikin uƙubar yaƙi.
Mutuwa na daya daga cikin abubuwan da suka fi tayar da hankali da mutum ke fuskanta, kuma yakin Gaza ya sa kullum dumbin mutane sun mutu. FArgaba da damuwar da ake cikin sakamakon mutuwar ƴan'uwa da dangi na iya haifar da baƙin ciki da zulumi sosai ga mutane.
Bugu da ƙari kuma, yaƙin da ake ci gaba da yi a Zirin Gaza yana ci gaba da ta'azzara, yayin da kowane sabon tashin hankalin ta ƙara taɓarɓarar da yanayin firgici da ake ciki. Mutanen da suka tsira daga yaƙin na iya fama da tashin hankali da ɗacin zuciyar da zai sa su shiga cikin uƙuba da rashin jin dadin rayuwa.
Kai ko da waɗanda ke bibiyar abubuwan da ke faruwa daga wasu sassan duniya za su iya cikin halin tsananin damuwa. Yawan kallon hotuna da bidiyoyi na yadda ɓarnar take ka iya jawo musu wani nau'in cutar damuwar.
Yanayin ciwon zai ɗauki alamun cutar PTDS kuma zai iya shafar duk wani da yake bibiyar lamarin sosai. Tashin hankalin da ake shiga saboda rashin samun damar kai taimako ko agaji ko tserar da mutanen da ke cikin yanayin ka iya ƙara ta'azzara halin da mutanen da ba a wajen yaƙin ba za su shiga.
"Shi kansa bibiyar lamarin abu ne mai wahalar gaske... kuma zai iya zama silar jawo cutar matsananciyar damuwa idan har ba kula ba sosai," a cewar Dr. Hala Alyan, wata ƙwararriyar likitar ƙwaƙwalwa ƴar asalin Falasɗinu da ke zaune a Amurka, da ta ƙware a fannin magance firgici.
"Musamman a wannan yanayin, lokacin da mutane suke jin ba a taimaka musu sosai bayan suna buƙatarsa, to sukan shiga cikin matsala ta lafiyar ƙwaƙwalwa sosai.
Ganin irin wannan na faruwa ne ke sa wasu su zama masu fafutuka ko buɗe ƙungiyar agaji, duk a ƙoƙarin yin wani kyakkyawan tasiri. Sai dai duk da haka shi ma irin wannan ƙoƙarin kan jawo matuƙar gajiyawa da shiga damuwa idan har ba a samu irin tallafin da ake so ba.
Yaƙin da ba a yi irinsa ba
Ƙawanya da taƙaita zirga-zirga da aka yi a Gaza ya sake jawo wata gajiyawar da damuwa. Yankin na ɗaya daga cikin mafiya cunkoso a duniya, kuma wannan ƙawanyar da hare-haren da ake yawan kaiwa na sake saka mutane cikin tasku da jin cewa sun maƙale.
Mafi yawan al'ummar Gaza ƴan ƙasa da shekara 18 ne, kuma da yawansu ba su da ƙarfin halin jure wa irin wannan yaƙi mai tsawo. Idan aka sake jan lokaci ana yaƙin nan, to zai iya yin mummunan tasiri a kansu.
Yaƙin basasar Syria da yaƙin Bosnia na 1992-1995, da kisan ƙare dangi na Rwanda a 1995 sun yi kamanceceniya da abin da ke faruwa a Gaza a yau. A duk wadannan rikice-rikicen, an kai har-haren bam a gidaje da makarantu da asibitoci.
Wannan asarar ababen more rayuwa na farar hula na kawo cikas ga rayuwar yau da kullum ta ‘yan kasa, kuma idan aka dade ana karya ƙa'ida, to da wuya a faro komai daga farko. Duk wani yaƙi kuma yana haifar da ƙaura kuma ta haka al'ummomi ke wargajewa.
Tasirin da yaƙin ke yi ga lafiyar ƙwaƙwalwa na dogon lokaci ya dogara ne da abubuwan da mutum ya gani. Tsananin yaƙi da tsawon rai, da kuma yawan mace-macen da aka samu duk abubuwa ne da ka iya ta'azzara lamarin.
Wani bincike na 2019 kan yakin Bosnia ya gano cewa "an shafe shekaru sakamakon yaƙin na tasiri a kan lafiyar ƙwaƙwalwar mutane."
Victoria Uwonkunda, wacce ta tsira daga kisan kiyashin Rwanda, ta bayyana wa BBC yanayin da ta shiga sakamakon “cutar da ba a iya gani” a shekarar 2021. “Tana haifar da firgicin da ka iya zuwa a kowane lokaci kuma hakan na sa wa na yi ta kokawa da numfashina. Yawanci gumi mai sanyi kan lulluɓe ni idan abin ya lafa, bayan na sha fama da komawa hayyacina.
Ba wannan ne karo na farko da mazauna Gaza ke fuskantar yaƙi ba. Wasu da dama da suka shaidi yaƙin da aka yi a Gaza tsakanin shekarar 2008 zuwa 2009 ko kuma na 2014 sun yi ta samar da dabarun kare kansu daga faɗawa cikin cutar tsananin damuwa, amma wannan yaƙin na yanzu ka iya tayar wa da masu fama da cutar PTDS ita.
Idan likitoci ma suka zama masu neman a duba su
Yaƙin da ake yi a Gaza a yanzu ya lalata tsarin kiwon lafiya. An rusa asibitoci sun zama ɓaraguzai, kuma an toshe hanyar shigar da kayayyakin asibiti a daidai lokacin da bukatar ayyukan kula da lafiyar ƙwaƙwalwa ta yi ƙamari.
Likitoci da sauran ƙwararrun kiwon lafiya, da ma’aikatan jinƙai suna aiki a cikin yanayi mai haɗari a cikin tsarin da ba a zuba masa kuɗi da yawa ba.
Rikicin na yanzu ya ƙara tsananta waɗannan buƙatu, inda masu kula da lafiyar ƙwaƙwalwa suke fuskantar ƙalubale biyu, na jure wa damuwar da su kansu ke ciki da kuma ta waɗanda suke kula da su.
Médecins du Monde, wanda kuma aka fi sani da Doctors of the World, ƙungiyar agaji ce ta ƙasa da ƙasa da ke aiki don ba da kulawar lafiya ga al'ummomi masu rauni.
Kungiyar ta yi gargadin cewa Falasdinawan suna fama da manyan batutuwan da suka shafi taɓin hankali, tare da wani kaso mai tsoka na jama'a, musamman yara, da ke matukar bukatar kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa da ayyukan tallafi na zamantakewa.
Tsagaita wuta zai haifar da yanayin da ƙwararrun masu kula da lafiyar ƙwaƙwalwa za su iya yin aiki cikin 'yanci da aminci, da samun damar faɗaɗa ayyuka da isar da saƙo ga masu bukata.
Abubuwan da suka faru daga bayan rikice-rikice a yankuna irin su ƙasashen Balkan da Ruwanda, sun jaddada muhimmancin yin ayyukan kula da lafiyar ƙwaƙwalwa da jin dadin jama'a cikin hanzari bayan dakatar da tashe-tashen hankula.
Waɗannan ayyuka dole ne su kasance ana yin su kuma a tabbatar mutanen da ke buƙata na samun kulawar da ta dace ta wannan ɓangaren, musamman ma yaran da abin ya shafa.
Marubucin, Kristian Alexander, Darakta ne na wata Cibiyar Bincike kan Tsaro da Ta'addanci a Duniya. Shi mai ba da shawara ne a Tattalin Arziki na Ƙasashen Gulf, mai ba da shawara kan yanayin ƙasashe, kuma mazaunin Washington ne. Ya yi aiki a matsayin Mataimakin Farfesa a Kwalejin Ilimin Dan'Adam da Kimiyyar zamantakewa a Jami'ar Zayed da ke Abu Dhabi, UAE.
Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya yi daidai da ra'ayi ko ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.