A ranar 29 ga Oktoba, 2024, mazauna kudu maso-gabashin Spaniya suka wayi gari da matsananciyar ambaliyar ruwa da ta yi ajalin sama da mutane 220, tare da janyo asarar dukiya.
Wadannan ambaliyar ruwa, da mamakon ruwan sama ke janyo wa, wanda ya kai yawan waanda aka samu a shekaru da dama, ba su ne irin su na farko a Turai ba, kuma ba za su zama na karshe ba, a yayin da dumamar yanayi ke addabar duniya da zafin da ba a taba tsammani ba.
Duniyarmu na fuskantar sauyin yanayi da ba a taba gani ba, wanda ya haura layin da aka shata na shiga hatsari kuma aka dade ana gargadi a kai daga malaman kimiyya.
Rahotannin baya-bayan nan na nuni da cewa dumin da duniya ta yi ya haura matsakaicin dumi na duniya na 1.5 a ma'aunin cenlcius idan aka kwatanta da zamanin baya kafin a samar da masana'antu (1850 zuwa 1900).
A yayin da wannan kari na iya zama dan kankani ga jama'a da dama, hakan na nufin wani matakin sauyi da ke barazana ga makomar dan adam da wanzuwar duniyar baki daya - wannan matsala za ta janyo cikar tekuna, ibtila'o'i da asarar dukiya da dama.
Wani rahoto da aka fitar a watan da ya gabata daga Kungiyar Kula da Yanayi ta Duniya ya bayyana cewa gurbatacciyar iskar da ake fitarwa ta kai wani yanayi mara kyau a 2023, wanda ke nuni ga ci gaba da karuwar dumin da duniya ke yi a shekaru da yawa masu zuwa.
Iskar carbon dioxide, wadda ke kan gaba wajen dumamar duniya, na taruwa a cikin shigifa da yawan da ba a tsammata ba a tarihin dan adam, inda a sama da shekaru 20 ta karu da sama da kashi 10.
Wannan kari ya samu ne saboda hayakin da masana'antu ke fitarwa. Wannan yanayi mai ban tsoro na nuni da cewa duniyarmu na neman kai mu ga inda ba a dawo wa, zuwa ga mummunan halin gurbatar yanayi.
Tuni masana kimiyya suka yi hasashen cewa shekarar 2024 za ta zama mafi zafi a tarihi.
Ayyukan Sauyin Yanayi na Copernicus, wani bangare na Shirin Copernicus na Tarayyar Turai, ya sanar cewa watan Yulin 2024 ne mafi zafi a tarihin yau, inda matsakaicin zafi a duniya ya karya tarihi da zama daraja 17.15 a ma'aunin celcius.
Hauhawar darajar zafi a matsakacin ma'auni alamu ne na hatsari, wanda ba iyakacin mafi yawa da mafi karanci ba, har ma da yadda ake samun ci gaban barazanar yanayi.
Wadannan sun hada da tsananin zafin da aka fuskanta a lokacin bazara bana a Amurka, mummunar ambaliyar ruwa a kudancin Turai, da mummunar gobarar daji a Kudancin Amurka.
Kuma mutane ne a duniya ke illatuwa da wannan tsananin sauyin yanayin, inda kasashe masu taso wa suka fi illatuwa da tasirin.
Wani nazari a baya-bayan nan da Kwalejin Imperial ta Landan ta yi cewa sama da rasa rayuka 570,000 aka samu sakamakon sauyin yanayi tun 2004.
Farin da aka samu a 2011 a Somalia, da ta yi ajalin rayuka 258,000 saboda yunwa da dumamar yanayi, wannan ibtila'i.
Kasashen da ke bacewa
Masanan kimiyya sun amince cewa ci gaba da ayyukan masana'antu da fitar da iskar gas mai guba da ba a sanya idanu a kanta za su kara yawan dumamar duniya zuwa ga daraja 2.7 a ma'aunin celcius nan da karshen wannan karni.
Wannan mummunan yanayi na dauke da sakamakon marar kyau, ciki har da yiwuwar nutsewar kasashen da suke a tsibirai a cikin teku; irin su Bangaladash, Maldives, da Alexandria, na gabar tekun Masar, saboda yadda teku ke kara cikowa.
Hakan kuma na barazana ga samar da abinci, lalata zamantakewa da rusa tattalin arzikin duniya.
Abin takaici, 'yan adam ne ke shan wahala saboda illata yanayi da ake yi ta hanyar mummunan amfani da albarkatun da ake da su.
Masanan kimiyya na alakanta tsanantar gurbata yanayi ga yawaita fitar da gurbatacciyar iskar gas da ke taruwa a shigifar duniya, tana janyo dumamar duniyar.
Wannan yanayi mai halakarwa ya sanya Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres nanata gargadin cewa duniyarmu na gaf da kaiwa wani mataki na zuw akarshe, yana alakanta hakan da "wutar yanayi".
Ya bukaci da a dauki matakan yaki da halin da ake ciki cikin gaggawa - wanda - inda za a rage yawan iskar carbon, da mayar da muhalli halin za da za a iya zama a cikin sa.
Ya jaddada cewa akwai bukatar hada hannu tsakanin kasashe masu taso wa, a mayat da hankali ga daina amfani da man da ke fitar da hayaki.
Kazalika, ya yi kira ga samun gamsasshen tallafin kudade don taimaka wa kasashe matalauta su rage fitar da burbataccen hayaki tare da saba wa da tasirin da ba za a iya kawar da shi ba.
Alkawarurruka da manufofi
Duk da kokarin kasashe na aiki da Yarjejeniyar Paris da ke da manufar rage dumamar duniya zuwa ga kasa da draja 1.5 a ma'aunin celcius don magance mummunan tasirin sauyin yanayi, gibin da ke tsakanin alkawarurruka da manufofin da aka gani a kasa na ci gaba da fadada kowacce shekara. Martanin kasashen duniya na zama mai bakanta rai da rashin isa wajen magance kalubalen da ake fuskanta.
Wani cikas na baya-bayan nan shi ne kudirin yarjejeniyar kudi da fadar shugaban kasar Azaerbaijan ta samar a wajen taron COP29 da aka yi.
Yarjejeniyar ta bukaci kasashe masu arziki, da tarihi ya bayyana su ke da alhaki kan rikicin sauyin yanayi saboda masana'antun da suke da su, su bayar da tallafin dala biliyan 250 kowacce shekara nan da 2025 don taimaka wa kasashe matalauta su yaki tasirin sauyin yanayi.
Sai dai kuma, wannan kudiri ya fuskanci suka daga dukkan bangarori, a yayin da ya nemi a biya kudin da yake kasa da dala biliyan 400 da ake nema kowacce shekara don yakar sauyin yanayi.
Wadannan manufofi ba rashi adalci suke yi ba kawai, har ma da wasa da rayukan miliyoyin jama'a, musamman a yankuna masu rauni irin su Afirka da kananan tsibirai.
Mafitar da ake sa ran samu
Har yanzu akwai fata nagari wajen kawar da mummunan tasirin sauyin yanayi. Majalisar Dinkin Duniya ta yi karin haske da cewa cigaban da aka samu na kere-kare a yau na iya rage fitar da iska gurbatacciya nan da 2030 da 2035. Kwararru na jaddada cewa dole ne fitar da iskar carbon gurbatacciya a duniya ya ragu da kashi 45 nan da 2030 da kuma zuw akarshe baki daya nan da 2050.
Muhimman matakai sun hada da aiwatar da Shirin Sabo na Kasa, dakatar da sabbin ayyukan da za su fitar da fossil nan da 2030, daina amfani da gawayi nan da 2040, da tabbatar da kasashe masu arziki sun bayar da kudaden da suka kamata.
Mafita ta hada da sake dawo da dazuka, kare al'ummu masu rauni, inganta tsarin bayar da gargadi da wuri da wayar da kan jama'a ta hanyar halayya mai dorewa.
Cim ma wadannan manufofi na bukatar aiki tukuru daga daidaikun mutane, gwamnatoci da kungiyoyi ma.
Rikicin sauyin yanayi ba wai matsala ce ta muhalli ba, ta zama jarrabawa ga bil'adama da kokarinmu na hada kai da aiki tare.
Rikicin da muka fuskanta yau zai zama kira, da ke kira gare mu da mu dauki mataki nan da nan. Tambayar a yau ita ce: Mun shirya daukar nauyin, ko za mu ci gaba da nade hannaye muna kallo duniyarmu na narke wa ta yadda za a kare baki daya.?