Daga Sylvia Chebet
Ɗaya daga cikin yanayin rayuwa mafi muni a Jamhuriyar Dimoƙradiyyar Congo (DRC) da mace ko yarinya wadda ke gudun hijira ke fuskanta shi ne barazanar yiwuwar cin zarafi.
Yayin da tashe-tashen hankula daga 'yan bindiga ke ci gaba da mamaye yankin gabashin ƙasar mai fama da rikici, miliyoyin 'yan Congo sun haɗa kai wajen kafa sansanoni wucin gadi a Goma da Kivu, sai daga baya suka fahimci ba mafaka a wurare.
"Dubban mutane suna zaune ne a cikin matsugunai da aka gina su da leda. Wadannan gine-ginen ba su da kofofin da suka dace, wanda ke nufin mata da yara da ke zaune su kadai a ko yaushe suna cikin haɗarin fuskanatar kutse.
"Yanayin rashin tsaro a wuraren yana haifar da damuwa," kamar yadda Christopher Mambula, shugaban shirye-shirye a ƙungiyar Medecins Sans Frontieres (MSF) ya DRC ya shaida wa TRT Afrika.
A wani sabon rahoto, bayanan da MSF ta fitar sun ce tawagarta tare da Ma'aikatar Lafiya ta DRC, suna jinyar mutum fiye da biyu da aka ci zarafinsu da kuma waɗanda suka kuɓuta a duk sa'a ɗaya fadin ƙasar a shekarar 2023.
Rahoton mai taken ''Muna ƙira ga taimako’’ an samo shi daga wasu ayyuka 17 da ƙungiyar agaji da ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta kafa a wasu lardunar Kongo guda biyar - Kivu ta Arewa da Kivu ta Kudu da Ituri da Maniema da kuma Kasai ta tsakiya.
MSF ta ce adadin mutanen da aka samu a shekarar ya kai — 25,166 - shi ne mafi yawa da aka taba samu. A shekaru uku da suka gabata, tawagar MSF ta yi jinyar kusan mutane 10,000 da aka ci zarafinsu da kuma waɗanda suka kuɓuta daga cin zarafi ta hanyar lalata da su a ƙasar.
A cewar sabon rahoton, kashi 91 cikin 100 na waɗanda suka fuskanci cin zarafi ana ba su kulawa a sansanonin da ke kusa da Goma, da ke babban birnin Kivu ta Arewa.
Tun daga ƙarshen shekarar 2021 ne ake ta gwabza fada tsakanin 'yan ta'addan ƙungiyar M23 da sojojin Kongo da kawayensu, lamarin da ya tilasta wa dubban daruruwan mutane barin matsugunansu tare da nesanta su da al'ummominsu.
Sakamakon haka, matsugunan gudun hijira sun ƙaru sosai a shekarar 2023, yanayin da ya dagula lamuran tsaro.
Yayin da MSF ta yi ta samun ƙaruwar mutanen da ke samun kulawa a 2023, yanayin ya ƙaru sosai a watannin farko na shekarar.
A Arewacin Kivu kadai, an samu kashi 69 cikin 100 na jimillar waɗanda suka yi jinya a shekarar 2023 a faɗin larduna biyar da ke fama da rikici tsakanin watan Janairu zuwa Mayu.
''Bisa ga shaidar marasa lafiya, kashi biyu cikin uku daga cikin su an kai musu harin bindiga," in ji Mambula.
''Yawanci waɗannan hare-haren sun faru ne a wurare da kuma kewayen da mata da 'yan mata - kashi 98 cikin 100 na mutanen da MSF ta samar wa kulawa a DRC a shekarar 2023 - a lokacin da suka je deɓo itace ko ruwa ko kuma yin aiki a gonaki.''
Ƙarancin kayayyaki
Bazuwar mutane da ke ɗauke da makamai a ciki da wajen wuraren gudun hijira ya haifar da ƙarin cin zarafi ta hanyar lalata, ko da yake MSF ta lura de cewa rashin isassun agajin jinƙai da ƙyawun yanayi a sansanonin sun tsananta matsalar.
Ƙarancin abinci da ruwan sha da ayyukan samar da kuɗin shiga na kara tsananta yanayin raunin da mata da 'yan mata suke ciki na tilasta musu neman aiki a tsanuka da kuma gonakin da ke makwabtaka da su, yanayin da kan sa su fuskanci barazanar hare-hare da cin zarafi daga 'yan ta'adda masu ɗauke da makamai.
Ɗaya daga cikin mutune10 da MSF ta yi wa jinya a bara ƙananan yara ne.
Kazalika ƙungiyar ta bayyana rashin tsaftar a matsayin wani dalili.
"A rubuce, da alama akwai shirye-shirye da dama da za su hana tare da amsa buƙatun waɗanda aka ci zarafinsu," kamar yadda Mambula ya shaida wa TRT Afrika.
''Amma a sansanonin, ƙungiyoyin mu suna fafutuka kowace rana wajen ganin mutanen da abin ya shafa sun samu taimako. 'Yan shirye-shiryen da aka aiwatar na ɗan gajeren lokaci ne kuma ba su wadatar ba sosai.''
Ƙira ga ɗaukar mataki
Rahoton na MSF ya nuna cewa cin zarafi ta hanyar lalata babban matsalar gaggawa ce a fannin lafiya da ayyukan jinƙai a DRC da ke buƙatar ɗaukar mataki.
Bisa ga buƙatun da mutanen da lamarin ya shafa suka bayyana, rahoton ya lissafa wasu matakai 20 na gaggawa da bangarorin da ke rikici da juna za su ɗauka, ciki har da hukumomin Kongo - na kasa da na larduna da kuma na ƙananan hukumomi - har ma da masu ba da tallafi da ƙasashen duniya da sauran ƙungiyoyin ba da agaji.
MSF ta buƙaci waɗanda ke da hannu a cikin rikicin da su tabbatar sun mutunta dakokin jinƙai na ƙasa da ƙasa, tare da haramta ko wanne ayyukan cin zarafi.
"Dole ne a ba da fifiko wajen kare mutanen da fadan ya rutsa da su," in ji rahoton.
Ƙungiyar agaji ta yi ƙira kan a inganta yanayin rayuwa a sansanonin 'yan gudun hijirar.
Kazalika MSF ta yi ira kan a saka hannayen jari a ayyukan samar da ingantacciyar lafiya da zamantakewa da fannin shari'a da lafiyar kwakwalwa ga mutanen da aka yi wa fyade.
Hakan na buƙatar tallafi na dogon zango don haɓaka horon ma'aikatan lafiya da kayan aiki na smaar da kulawa da tallafin doka tare da samar da matsugunai na musamman ga waɗanda suka tsira.
Haka kuma ana kuma bukatar kudaɗe don ayyukan wayar da kan jama’a don ɗakile yanayin kyamatar wadanda abin ya shafa, wanda wani lokaci kan hana su neman taimako.