Daga Ferhat Polat
17 ga Fabrairu ce ranar tunawa da boren da aka gudanar a kasar Libiya, inda a bana aka cika shekara 13 da yin hakan. Akwai 'yan dalilai kaɗan da zai sanya 'yan Libya farin ciki, a lokacin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar rashin tabbas.
Tun bayan kifar da gwamnatin Muammar Gaddafi a 2011, Libiya ta fada ƙazamin rikicin siyasa. Yunkurin kifar da gwamnatin Gaddafi bai yi nasarar samar da zaman lafiya a kasar ba. Libiya ta zama kasar da ta tsinci kanta a yakin basasa mai fuskoki daban-daban.
Tun 2014, kasar na fuskantar rabuwar kan shugabanci, wanda ya janyo wanzuwar kungiyoyin 'yan tayar da kayar baya da dama a kasar da kuma karya ƙa'idoji. A hankali kasar ta fada rikici saboda hamayyar da ke tsakanin jagororin siyasa kuma soji.
Daga 2014 zuwa 2021, Libiya ta rabu gida biyu ta fuskar shugabanci; daya na Tarabuls dayan kuma a Tobruk.
A watan Maris din 2021 an kafa sabuwar gwamnati mai suna Gwamnatin Hadin Kan Kasa. An zabi Gwamnatin ta hanyar samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya kuma aka yi mata hedkwata a majalisar dokokin gabashin Libiya.
Wannan amincewa da gwamnati sabuwa ya zama muhimmin mataki ga Libiya, a yayin da take murnar kafa gwamnati guda daya tun 2014.
Bayan kafa gwamnatin, an dinga fata da sa ran samun zaman lafiyar siyasa, da ma gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a watan Disamban 2021.
Sai dai kuma, shirin bai yi nasara kamar yadda aka zata ba, wanda ya janyo aka dage zaben har sai baba ta gani.
Rashin Tsaro
A shekaru 13 da suka gabata, yanayin tsaro a Libiya na ci gaba da fada wa halin rashin tabbas saboda adawar da ke tsakanin shugabancin siyasa da gaza samun matsaya guda.
An sha fama da rarrabuwar kai a fagen siyasar Libiya da gazawar da aka yi ta shawo kan bangarorin da ke hamayya da juna, da kasa samar da rundunar soji guda daya mai kishin kasa.
Barazanar tsaro ta bayyana daga kungiyoyin masu tayar da kayar baya da dama a yammaci da gabashin Libiya, inda suka fi mayar da hankali ga gabashi.
Wannan duk na faruwa ne saboda Khalifa Haftar wanda ke jagorantar Sojojin Kasa na Libiya da suka yi tawaye, da suka hada da 'yan tawaye da kungiyoyin tayar da kayar baya.
Gibin shugabancin ya kuma bai wa mayaka sojojin haya na kasashen waje kamar Wagner na Rasha damar shiga kasar, ta kai ga ma karbe iko da rijiyoyin mai na Libiya.
Rarrabuwar kawuna a Libiya a fannonin siyasa da tsaro ya kawo gogayya wajen karbe iko da rijiyoyin man fetur. Daga nan kuma sai mayakan kasashen waje suke rufe rijiyoyin man fetur din.
Mayaka dauke da makamai da ke da alaka da Wagner sun kwace iko da kadaorin mai biyu mafiya girma a Libiya; El Sharara da tashar jiragen ruwan da take amfani da ita wajen fitar da man kasashen waje.
An san Libiya da zama kasa ta biyu mafi yawan albarkatun mai a Afirka kuma ana yi mata kallon daya daga mafiya yawan arziki d akudaden da ake samu ta sayra da albarkatun mai.
Abun takaici, sakamakon daukar tsawon lokaci ana rikicin, Libiya ta zamo kasar da ba ta samun kudade sosai. Wannan ya janyo durkushewar tattalin arziki a kasar.
Matsalolin hukumomi
Gine-ginen gwamnati sun zama wuraren da za a iya amfani da su don warware rikici da biyan bukatun da za su taso bayan yaki, kuma suna taimaka wa wajen cigaban kasa, habaka tattalin arziki, zaman lafiyar siyasa da dimokuradiyya.
Game da haka, babbar gwagwarmayar Libiya ta sake gina kasa na fuskantar cikas daga muta ta'annati a kungiyoyi da suke kallon wannan yunkuri a matsayin barazana ga abin da suke samu, hakan ya sanya suke hada karfi wajen yakar duk wani yunkurin gina kasa da samar da zaman lafiya da gwamnati ke yi.
Shekaru 13 bayan fara yakin Libiya, babbar hanyar dawo da zaman lafiya da sake gina kasar ta ta'allaka kan hadin kan gwamnatoci da hukumominsu, misali hukumomin tsaro da na kula da cigaban tattalin arziki.
Karfi da tasirin Rashin gwamnati guda da wanzuwar 'yan tawaye ne ke hana kawo cigaba a kasar.
Wannan ne kawo kalubalen shiryawa da aiwatar da matakan gyara. Haka kuma, gwagwarmayar kwatar madafun iko da ake ci gaba da yi tsakanin bangarorin biyu, na hana aikawa ma'aikatu kudade tare da kawo jan kafa ga sake gina kasa.
Misali, karyewar manyan madutsun ruw abiyu a garin Derna mai tashar jiragen ruwa ya janyo ambaliyar ruwan da ta illata fararen hula da dama, ta ra su da matsugunansu tare ds rusa gidajensu.
Zabukan da aka dade ana jira
Zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da aka dade ana jira a Libiya, an so a gudanar da shi ne a watan Disamban 2021, amma kuma an dage lokacin a yanzu har sai baba ta gani saboda rashin amincewa da ci gaba da tattaunawa da ake yi.
Kasashen duniya na kallon gudanar da zaben a Libiya a matsayin hanya maimuhimmanci da za a bi waje magance rikicin waye shugaba, da kuma sake gina tubalin dimokuradiyya.
Gudanar da zabe na gaskiya ba tare da muna-muna ba zai warrware rikicin. Sai dai kuma, zaben da zai zo a nan gaba na fuskantar kalubale da dama. Daya daga cikin matsalolin shi ne rashin amincewa kan kundin tsarin mulki guda.
Dadin dadawa, bangarorin da kawunansu suke a rabe kamar Haftar Khalifa da Saiful Islam Gaddafi na son tsayawa takarar shugaban kasa, wand ahakan ke kara rikita batun zabukan.
Domin tabbatar da kyakkyawan tsarin siyasa a kasar, ya zama dole a yi aiki sama da yadda ake yi a yanzu. Daya daga cikin manyan manufofin zabe shi ne ya samar da turba mai kyau ga kasa, tare da fitar da manufofi da tsare-tsare.
Zabukan da aka yi a baya ba su da wasu manufofi ko tsare-tsare, tare da Samar da Kundin Tsarin Mulki a 2012 wanda shi ne mataki na karshe na manufofin siyasa.
Saboda haka, gudanar da sabon zabe zai bayar da damar a kafa zababbiyar gwamnati, a kuma fayyace hanyar da za a bi a nan gaba.
Ya zama wajibi a lura da cewa Turkiyya da Masar na ta yin kokarin kyautata alakarsu da ta tabarbare musamman tun farkon 2021.
Ankara da Alkahira na da damar dabbaka zaman lafiya a Libiya, duba da karfin fada a ji da suke da shi kan bangarorin da suke adawa da juna a kasar.
Ankara na goyon bayan gwamnatin Libiya da Majalisar Dinkin Duniya tayarda da ita mai helkwata a Tarabulus, a yayin da Alkahira ke goyon bayan gwamnatin Haftar ta LNA.
Sai dai kuma, duk da suna goyon bayan bangarori daban-daban, kasashen biyu sun bayyana muhimmancin farfado da siyasa da dimokuradiyya a Libiya.
Makomar Libiya na nan a cikin rashin tabbas a yayin da kasar ke wani mataki mai rauni na neman sauyin shugabanci. Ana bukatar kyakkyawan tsari da taswirar tabbatar da dimokuradiyya a kasar cikin gaggawa.
Dole ne wannan taswira ta hada da samar da sabon kundin tsarin mulki, gudanar da zabe da hade kan hukumomin gwamnati, wanda za su kai ga cimma dawwamammun manufofin gina al'umma mai aiki da dimokuradiyya.
Marubucin makalar Ferhat Polat, malami ne mai bincike a cibiyar Bincike ta TRT World. ya kware wajen siyasa da tsaron Arewacin Afirka, ind aya fi mayar da hankali kan Libiya.
Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya zama daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.