Daga Sylvia Chebet
Yayin da wasu yankunan Afirka ke ci gaba da fuskantar barazanar cutar Ebola, wasu sabbin bayanai kan tasirin allurar rigakafin cutar sun sanya ƙwarin gwiwa.
A wani binciken baya-bayan nan da kungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta gudanar ya nuna cewa an samu raguwar mace-macen mutanen da suka kamu da cutar har ma a tsakanin wadanda aka yi wa allurar rigakafin cutar, yana mai ƙaryata batun da ke cewa allurar rigakafin ba shi da wani tasiri.
Binciken wanda aka wallafa a shafin ''The Lancet Infectious Diseases'', ya yi nazari kan bayanan bullar cutar Ebola karo na 10 a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC) daga shekarar 2018 zuwa 2020.
Bayanan binciken sun yi nuni da cewa an samu ragi a haduran mace-mace da kusan kashi 56 cikin 100 a tsakanin mutanen da suka kamu da cutar da ba a musu allurar rigakafin ba zuwa kashi 25 cikin 100 ga wadanda suka yi allurar.
Rage haɗarin mutuwa ta hanyar allurar rigakafi ya shafi kowane shekaru da jinsi, ba tare da la'akari da ko sun taba yin allurar a baya ko kafin su kamu da cutar ba.
Manajan shirye-shiryen kungiyar MSF na yankin Gabas da Kudancin Afirka, Dokta Christopher Mabula, wanda ya kasance a DRC lokacin bullar annobar ta ƙarshe, na ganin an samu ci gaba sosai.
Ya shaida wa TRT Afrika cewa sakamakon binciken na ƙara ba da ƙwarin gwiwa a daidai lokacin da ake kan yaki da sake ɓullar cutar ''mai ban tsoro''.
Alamun cutar mara tushe
Wani abu da ya sa cutar Ebola ta zama mai haɗari shi ne, a sauƙaƙe za a iya ruɗan wanda ya kamu da cutar ya yi tunanin mura ce har sai cutar ta ci karfin jikinsa ko kuma ta kai wani mumunar mataki.
"Alamomin cutar sun hada da - zazzaɓi da ciwon kai da ciwon makogwaro da rashin ci abinci da rashin kuzari da ciwon jiki da kuma gabobi - suna kama da cututtukan yau da kullum na laulayi tsakanin kwanaki biyu zuwa 21," in ji Dokta Mabula.
"Ga wadanda suka kamu da nau'in cutar mai tsanani, takan shafi hanta da ƙodarsu. idan hakan ya faru, toh sassan biyu za su daina aiki, kuma hakan zai iya haifar da zubar jini.''
Dakta Mabula ya yi imanin cewa idan ba a yi allurar rigakafi ba, duk wanda ke yankin da cutar Ebola ta barke yana cikin hadarin mutuwa. "Da zarar mutane sun kamu da kwayar cutar, kusan kamar ana jujjuya tsabar kudi ne," in ji shi.
A lokacin barkewar cutar Ebola mafi girma a tarihi tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016, ta bazu a Afirka zuwa Turai har da Amurka, inda aka tattara adadin mutane 28,000 na wadanda suka kamuwa da cutar.
Sama da mutum 11,000 da suka kamu da cutar ne suka mutu a kasar Guinea da Saliyo da kuma Laberiya da ke zama cibiyar da cutar barke.
Sabbin matakai da suka bullo
Sakamakon wannan koma bayan da aka samu, sabon binciken ya buɗe sabbin damarmakin samar da magani da takaita cutar ta ebola.
"Sakamakon da muka samu ya ba mu damar hada alluran riga kafi da magani. Ba a samu wata illa tsakanin ba da allurar riga kafi da maganin cutar Ebola ba a cikin binciken," in ji Etienne Gignoux, daraktan kula da cututtuka masu yaduwa na MSF.
Sai dai kamar yadda Dr Mabula ya bayyana, akwai matsaloli masu tarin yawa. Na farko shi ne samun allurar rigakafin har yanzu yana da fuskantar tangaro.
"Ba wai kawai za ku danna yatsarku ba ne, sai ku samar da allurar da yawa," in ji shi, yana mai bayanai cewa maganin baya kasuwa ga masana'antu don su samu damar samar da adadi masu yawa.
Bugu da ƙari, allurar riga kafin da MSF ta yi nazari a kai yana tasiri ne kawai kan nau'in cutar Ebola na Zaire ba a kan sauran nau'in cutar uku ba wato (Sudan da Bundibugyo da kuma Tai Forest) wadanda suma suke haifar da rashin lafiya ga mutane .
Wani labari mai dadi shi ne idan aka sake samun barkewar cutar a nan gaba, likitoci za su yi dace wajen yi wa wadanda suka taba yin allurar da kuma wadanda ba su yi ba magani.
Kazalika masana sun bayyana cewa hakan zai ba wa ma'aikatan kiwon lafiya da ake tura wa yankunan da cutar Ebola ke bulla kwarin gwiwa.
Ƙalubalen samarwa
An tsara karbar riga kafin ERVEBO ko rVSVΔG-ZEBOV-GP sau daya ne lacal, musamman ake ba da allurar a matsayin wani ''riga kafin zobe'' ga mutanen da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar Ebola a lokacin bullarta.
"Idan aka samu wanda ya kamu da cutar, sai a yi gaggawar yi wa duk abokan huldarsa ko kuma wadanda ya yi mu'amala da su allurar," in ji Dokta Mabula.
Yayin da binciken da MSF ta gudanar ya nuna cewa duniya ta samu wata katanga mai karfi kan zazzafar cutar zazzabin, sai dai Dakta Mabula ya yi nuni da cewa akwai wasu matsaloli masu alaka da samar da alluran rigakafin.
"Ebola ba cutar ba ce da ake samu a ko da yaushe. Hakan na nufin ta fuskar kasuwanci ba riga kafin ba ne zai sa a samu makudan kudade, domin har yanzu akwai iyaka wajen samar da wadannan allurai."
Kazalika hakan ya shafi hanyoyin samar da magungunan cutar Ebola.
"Magungunan da ake da su ba su da yawa, ina nufin, idan aka samu bullar cutar a yankin yammacin Afirka, maganin da ake bukata ba za su isa ba. Daga karshen, kayan aikin da ake bukata don yaki da cutar Ebola suna da iyaka,” in ji Dr Mabula.