Labaran ƙarya sun taka muhimmiyar rawa wurin tayar da tarzoma a Birtaniya. / Hoto: Reuters

Daga Sunder Katwala

An gudanar da tarzoma mafi muni a Birtaniya wadda aka shafe shekaru ba a ga irinta ba makonni biyu da suka gabata.

Gungun masu ra'ayin riƙau waɗanda labaran ƙarya suka cika musu kunne kan cewa wani Musulmi ɗan ci rani ne ya caka wa wasu yara mata uku wuƙa a Southport, wanda hakan ya ja suka mayar da martani ta hanyar kai hari masallatai da kan 'yan ci rani da wasu kuma ƙananan ƙabilu.

Sai dai wani yaro ɗan Rwanda wanda mabiyin addinin Kirista ne, an haife shi a Wales kuma shi ne ya aikata kisan.

Yaɗa labaran na ƙarya sun taimaka wurin rura wutar tarzoma, sai dai son zuciya na daga cikin abubuwan da ya ƙara rura wannan wutar.

Son zuciyar masu ƙin jinin Musulunci

Ya Birtaniya take game da hakan? Wannan labarin mai tsawo yana tattare da sauyi mai kyau na tsawon shekaru. Sai dai masu ƙin jinin Musulunci suna da yawa sosai fiye da sauran nau'ukan wariyar launin fata da son zuciya a Birtaniya yau.

A shekarar 2019, wani bincike da aka yi a Turai ya nuna cewa cikin mutum 20 da ake yi wa tambayoyi, ana samun aƙalla mutum ɗaya da ke cewa ba ya so ya yi maƙwabtaka da Musulmi. Wannan zai kasance kamar adadi maras yawa, amma mafi yawa na yau da kullun na iya kaiwa kashi uku ko fiye na yawan jama'an.

Sai dai abin jin daɗin shi ne an samu yadda aka rinƙa Allah wadai a siyasance daga ɓangaren jama'a kan wannan lamarin. Wata ƙuri'ar jin ra'ayi da YouGov ta yi ya nuna cewa kaso 85 cikin 100 na jama'ar da aka yi wa ƙuri'ar ba su ji daɗin wannan tarzomar ba. Sai dai sauran kaso 7 ɗin sun ce sun amince da hakan, daga ciki har da kaso biyu waɗanda suka ce sun yi matuƙar amincewa da hakan.

Binciken farko da aka gudanar kan halayyar jama'ar dangane da tarzomar ya nuna cewa akasarin waɗanda suka gudanar da wannan tarzomar 'yan daba ne, haka kuma suna daga cikin masu tsatsauran ra'ayi kuma masu wariyar launin fata. Sai dai kashi ɗaya cikin biyar na waɗanda aka yi binciken a kansu ya nuna cewa wasu daga cikinsu na da damuwa mai ƙarfi a tattare da su, haka kuma ɗaya bisa huɗu na waɗanda aka yi binciken a kansu na ganin ya kamata a ga laifin Musulmi dangane da wannan abin da ya faru.

Haka kuma kaso 62 na wannan kashin bakwai na ganin wannan tarzomar ta nuna akasarin yadda 'yan ƙasar ke kallon wannan lamarin.

Bakwai cikin mutane 10 na wannan kungiya sun ce musulmi ne ke da alhakin wannan rikici. Waɗannan alamu ne da ke nuna cewa kaso uku zuwa huɗu na al'ummar na da tsatsauran ra'ayi, wanda hakan ke nufin akwai mutum miliyan ɗaya zuwa biyu waɗanda ke da tsatsauran ra'ayi a zukatansu.

Wannan adadin yana da yawa kuma ya isa ya rura wata wutar rikici wadda za ta iya bazuwa.

Martanin gwamnati

Ta yaya gwamnati ya kamata ta mayar da martani? Gwamnatin Firaminista Kier Starmer ta gaji tsare-tsare waɗanda ke cike da ƙin jinin Musulunci.

Gwamnatin Conservative ta ƙarshe ta himmatu wajen aiwatar da ayyana kyamar Islama a cikin 2019 - sai dai ta yi watsi da hakan ba tare da yin wani aiki ba. Haka kuma shirin da suka yi na naɗa mai bayar da shawara kan ƙin jinin Musulunci shi ma duk bai faru ba.

Kalmar Islamophobia, wadda aka soma amfani da ita a shekarar 1997 wanda Runnymede Trust ya ƙirƙira, ƙungiyoyi masu zaman kansu da 'yan siyasa na yawan amfani da ita domin alaƙanta masu ƙin jinin Musulunci.

Amma wasu suna ganin cewa mayar da hankali ga imani ("Musulunci") maimakon mabiya ("Musulmi") na iya haifar da rudani game da manufar da ke tattare da ayyukan.

Dangane da gwamnatin Burtaniya, ingantacciyar ma'anar kyamar Musulunci yakamata ta hadu da gwaje-gwaje guda uku: Ya kamata ta zama sahihiya da adadin Musulmi masu yawa; a fahimci cewa akwai adalci sannan kuma a samu ‘yanci tsakanin ‘yan ƙasa; a yi amfani da ita ga mutanen da ke aiki ɓangaren ilimi da wuraren aiki duk a ɗaya daga cikin matakan daƙile ƙyama da son zuciya a hanyar da ta kamata.

Yawancin mutane za su yarda cewa ba kyamar Musulunci ba ne yin sukar ra'ayoyi ta fuskar imani ko siyasa; ko kuma a yi muhawara, cikin gaskiya, ƙalubalen asali da kuma haɗewar 'yan ƙasa a Birtaniya a yau.

Ma'anar kalmar wani ɓangare ne kawai na farawa. Babban burin ba wai shi ne faɗakarwa kaɗai game da girman matsalar ƙin jinin Musulunci ba, amma kaiwa ga jama'a da dama da suka dace domin ƙalubale daban-daban da ake fuskanta da kuma rage son rai.

Akwai sauran ƙalubale

Daga cikin waɗannan ƙalubalen - waɗanda ake nuna wa ƙiyayyar nan na buƙatar taimako da nuna kula domin su kai ƙara da kuma hukunta laifin kiyayya. Akwai buƙatar waɗanda ke da halayyar bayar da goyon baya su haɗu domin samar da tsare-tsare masu ƙwari don kawo ƙarshen ƙiyayyar.

Wannan tarzomar ta nuna amfanin ƙara matsa ƙaimi kan a shafukan sada zumunta, waɗanda suka gaza gane jan layi tsakanin tofa albarkacin baki da kuma cin mutunci da ƙiyayya da tarzoma.

Babbar hanyar rage irin wannan ƙiyayyar ita ce kaiwa ga asalin jama'ar da ke cikin al'ummomi waɗanda suke tsoron Musulmai 'yan Birtaniya fiye da sauran ƙananan ƙabilu.

Sanin mutane masu muhimmanci na yin tasiri wurin ƙara azama da ƙwarin gwiwa - sai dai hakan bai cika yaɗuwa cikin al'ummar mu ba. Ana haɗuwa da matasa sosai a manyan birane fiye da garuruwan da ke mil 20 daga manyan biranen da ƙauyuka da kuma a bakin teku waɗanda aksarin jama'ar da ke zaune a wurin kaso 95 zuwa 98 fararen fata ne.

Domin taimakawa da hakan, akwai buƙatar duk wata makaranta ta tabbatar ɗalibanta sun rinƙa mu'amala mai kyau da Musulmai - daga faɗin al'ummomi.

Hakan zai iya faruwa lafiya kalau a makarantu a manyan birane, amma zai buƙaci fito da dabaru, daga ciki har da gudanar da ayyukan makaranta a wuraren daban-daban.

Idan ƙalubalen ya fi girma a tsakanin tsofaffi, ana buƙatar tunani mai zurfi game da yadda za a nasara a tsakanin ɗalibai na makaranta ta yadda za su samu hanyoyin wayar da kan iyayensu.

A nan gaba, magance kin jinin Musulunci ba zai zama aikin gwamnati kaɗai ba. Akwai buƙatar al'umma su shigo ciki domin ƙara faɗaɗa lamarin ga waɗanda ke can ƙasa.

TRT Afrika