Dan wasan gaban na Brazil, Vinicious Junior ya fashe da kuka a wajen taron manema labarai gabanin wasan sada zumunci tsakanin Brazil da Spain a filin atisaye na Real Madrid da ke Valdebebas a ranar 25 ga Maris na 2024. (AFP/Pierre-Philippe Marcou).

Daga

Moha Gerehou

A kwanakin baya ne dan wasan kwallon kafar Brazil, Vinicious Junior ya fashe da kuka a lokacin da yake ganawa da manema labarai gabanin wani wasan sada zumunta a Real Madrid, inda ya bayyana cewa harkar kwallo "ta fara fita a ransa" saboda yadda yake yawan fuskantar cin zarafin nuna wariyar launin fata a wasanni a kasar.

Dan wasan mai shekara 23 ya yi kira ga hukumomin kwallon kafa da su "kara kaimi" ya sake taso da maganar da aka rika yi a bara na yadda dan wasan ke cigaba da fuskantar cin zarafin nuna wariyar launin fata a ciki da wajen filin wasa.

Matsalar nuna wariyar launin fata ta wuce maganar kwallon kafa kawai, magana ake yi ta matsalar da take neman yin katutu a kasar ta Spain baki daya.

A bara, lokacin da Vinicious ya caccaci magoya bayan Kungiyar Valencia CF bisa kalaman nuna wariyar launin fata da suka yi masa da kwatanta shi da biri, an dauki makonni ana kai-komo tsakanin kungiyoyin yaki da nuna wariyar launin fata da masu fafutikar yaki da lamarin a Spain.

Ina cikin wadanda suka ta samun kiraye-kiraye daga 'yan jarida da daidaikun mutane a game da lamarin.

Nakan tuna kusan a kowace hira ake fara tambayata: Shin Spain kasar masu nuna wariyar launin fata ce? Nakan ba da amsa iri daya, cewa: e.

"Burina in buga kwallon kafa cikin kwanciyar hankali, burina in taimaki kungiyata da 'yan uwana"

Nuna wariyar launin fata ya fara zama ruwan dare a Spain, kamar yadda nuna bambancin jinsi da arziki ya zama ruwan dare a kasar. Nuna wariyar launin fata ba a filin wasa kawai ake yi ba, har a titunan kasar ana yi.

A matsayina na bakin fata da aka haifa a Spain, ina magana ne daga abin da na sani, saboda ina iya tunawa: lokacin ina yaro, mukan sha fama da taimakon 'yan'uwanmu wajen zirga-zirgar zuwa ofisoshin shige da fice, da rashin adalcin 'yan sanda a shingayensu saboda bambancin launin fata, da kuma lokacin da muka girma muka fara shan wahalar neman aiki da fama da nuna wariyar launin fata a intanet.

A Spain, babu wata kididdiga a hukumance a kan illolin da nuna wariyar launin fata ke haifarwa, amma mun san kusan kashi 80 na kamfanonin dillancin gidaje ba su cika ba baki hayan gidaje ba, ga yadda kamen 'yan sanda ya fi kamari a kan bakaken fata da Larabawa, sannan kuma ana nuna wariya a makarantu.

Duk da hujjojin da suka bayyana a zahiri, hukumomin kasar Spain suna cigaba da karyata batun nuna wariyar launin fata a kasar, inda suke bayyana cewa ba a cika samun matsalar ba a kasar.

A kwanakin nan, fitatun 'yan wasan kwallon kafar Spain, kamar Carvahal na Spain da Donato na Brazil sun ce kasar Spain ba kasar nuna wariyar launin fata ba ce. Amma tambayar da nake yi ita ce: Idan Spain ba kasar nuna wariyar launin fata ba ce, me ya sa ake yawan samun matsalar a gomman shekaru?

Idan ana maganar kwallon kafa, shugabannin harkar sun fi kowa sanin halin da ake ciki. Ba Vinicious farau ba, kuma ba karau ba.

Kwanakin baya, a mako daya an samu matsalar sau uku: An nuna wa golan Rayo Majadahonda mai suna Cheikh Sarr da kocin Sevilla mai suna Quique Sanchez Flores da dan wasan kasar Ajantina mai suna Marcos Acuña wariyar launin fata.

Shekara 10 da suka gabata, wato a shekarar 2014 ce aka jefa wa dan wasa Dani Alves ayaba. A shekarar 2006, dan wasan Kamaru Samuel Eto'o shi ma ya yi yunkurin ficewa daga filin wasa saboda ana kwatanta shi da biri.

Haka kuma a shekarar 1993, golan Nijeriya Wilfred Agbonavbare ya ce ya ji ana ihun "Ku Klux Klan" a filin wasan Real Madrid da kuma jefa masa auduga.

A bara ma, Iñaki Williams, dan wasan Athletic Club de Bilbao, wanda iyayensa 'yan asalin kasar Ghana ne ya kai karar cin zarafinsa kotu.

Dan wasan Athletic Bilbao Inaki Williams a gefen hagu yana yunkurin kwace kwallo a hannun dan wasan Valencia Mouctar Diakhaby a wasan farko na kusa da karshe na Gasar Copa del Rey a birnin Bilbao a Spain a ranar Alhamis, 10 ga Fabrailun 2022. (AP/Alvaro Barrientos).

Idan ana wasan kwallo, akwai kamarori da yawa, ga kuma dubban masu kallon wasa. Bai kamata a ce an sha wahala wajen gano wadanda suka yi wakar nuna wariyar launin fata ba. Sannan matsalar fa ba a tsakanin manya kadai ta tsaya ba.

Haka kuma ana haka a tsakanin magoya bayan wasa. A watan Fabrailu, kafin wasan Real Madrid da Atletico de Madrid, wani mutum ya ci mutunci tare da yi wa wata 'yar shekara 8 mai sanye da rigar Vinicious Junior barazana, duk da an kama shi bayan watanni.

Na tuna lokacin da nake kwallon yarinta a kungiyar Huesca, wani karamin gari a Arewacin Spain, inda tun ina dan shekara 12 nake jin wakokin nuna wariyar launin fata, kuma abin ban haushi manya ne suke yi. Bayan shekara 20 har yanzu ina tuna lamarin. Haka ma na fuskanci barazana, wanda wannan sanannen abu ne ga dukkan bakaken fata masu buga kwallo a Spain.

Matsalar ita ce, duk abubuwan da suke faruwa, shin me hukumar La Liga ke yi a game da matsalar? Shin ana samun canja? A ra'ayina, suna daukar matakan da ba za su wani kawo gyara ba ne. Gasar ta Spain ta koma tura korafin da aka kawo musu ne zuwa ga kotunan gama-gari, maimakon na kwallo, wanda hakan ke jawo cikas wajen saurin yanke hukunci.

A jawabinsa game da yawan samun matsalolin nuna wariyar launin fata a Spain, kocin Atletico Madrid, Diego Simeone ya ce, "Magance matsalar nuna wariyar launin fata ba aikin mutum daya ba ne. Dole a hada karfi da karfe."

Hukuncin da ake yi ba su da zafi kamar rufe filayen wasa da zaftare maki da sauransu, kamar yadda ake yi a Gasar Firimiyar Ingila.

Amma duk da haka, lamarin ya fi karfi a tsakanin mutane. Mun fara sanin wariyar launin fata ne a wajen magana da kafofin sadarwa da siyasa da makarantu. Matukar ba mu sauya wannan lamarin ba, za a cigaba da samun matsalolin nan a filayen wasa da ma a tsakanin mutane.

Hawayen da Vinicious ya zubar a taron manema labaran ya nuna tsananin damuwar da ke ci masa tuwo a kwarya.

Hawaye ne da ya zubar a madadin wasu, wadanda kamar dan wasan na Brazil suke takaicin yadda nuna wariyar launin fata ke cigaba. Dan wasan yana sane da hakikanin abin da ke faruwa sama da abin da muka sani.

Wanann matsalar ta sa mutanen Spain suke tattaunawa, suke tunani, suke karatu tare da sauraron abubuwan da ake fada a game da bambancin launin fata, tattaunawar da ta zama dole idan har muna son kawo sauyi. Domin babu matsalar da ba ta da magani.

Haka kuma hawayen Vinicious ya kara bayyana illar nuna wariyar launin fata ga lafiyar kwakwalwa.

Burina shi ne nan gaba a daina tambayata a game da ko kasar Spain kasar masu nuna wariyar launin fata ce ko a'a.

Burina shi ne nan gaba a fara tambayata me kasar Spain take yi domin yaki da nuna wariyar launin fata. Wannan me abin da ya kamata mu mayar da hankali.

Marubucin, Moha Gerehou, dan jarida ne mai zaman kansa da yake aika rahotanni a jaridu da rediyo da gidaje talabijin. Mamba ne a Kungiyar Conciencia Afro, tsohon Shugaban SOS Racismo a Spain, sannan marubucin littafin "Qué hace un negro como tú en un sitio como este" wanda ke nufin (Me bakin mutum kamar kai yake yi a waje irin wannan?)

Togaciya: Ra'ayin marubucin ba dole ba ne ya zama ya yi daidai da ra'ayin da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.

TRT Afrika