Cin zarafi da ake yi wa fursunonin da aka tsare su a gidan yarin Abu Ghraib na kasar Iraki ta hanyar amfani da ''muggan dabarun amsa tambayoyi'' ya bayyana a duniya a watan Afrilun 2004.  Tun daga lokacin wadanda suka tsira suke ta fafutukar ganin sun samu adalci .Hoto: AP / AA  

Daga Hamzah Rifaat

Shekaru 20 kenan da mummunan labarin cin zarafin da ake yi a gidan yarin Abu Ghraib.

Hotunan ban tausayi da tashin hankali da kuma rashin imani da mutunta ɗan'adam na yadda sojojin Amurka ke cin zarafi da kuma wulakanta fursunonin gidan yarin Abu Ghraib da ke kasar Iraki sun yi matuƙar tayar ɗa jijiyoyin wuya a duniya.

An yi ta sukar Sakataren Tsaron ƙasar na lokacin Donald Rumsfeld saboda kawar da kai da kuma ƙarfafa ayyukan cin zarafi kan fursunoni a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba George W. Bush na Amurka.

Har yanzu an gagara yi wa mutanen da lamarin ya shafa adalci.

Lauyoyi uku da suka gabatar da ƙara sun shafe tsawon lokaci suna gwagwarmaya kan shari'ar, kana a ƙarshe suka samu zama a kotu a watan da ya wuce bayan wata ƙarar aka shigar kan Cibiyar Nazarin Tattalin Arziki ta Virginia (CACI).

Sun yi zargin cewa ma'aikatan da ke aiki da sojojin Amurka a lokacin sun aikata munanan cin zarafi a gidan yarin.

Sai dai zaman kotun ya gamu da cikas, bayan da alƙalin da ke jagorantar shari'ar ya bayyana cewa shari'ar ba ta kammalu ba.

Wannan rashin adalci ne tsantsa.

Abin da faru

Lamarin ya soma ne bayan mamayar Amurka na shekarar 2003 a Iraki don hamɓarar da gwamnatin Saddam Hussein.

A 2004, shirin labaran Minti 60 da gidan talabijin din Amurka ya ɗauka, ya bayyana hotunan 'yan Iraqi maza da jami'an Amurka ke cin zarafinsu ta hanyar duka da azabtarwa a gidan yarin Abu Ghairb.

Kazalika lamarin ya biyo bayan watanni 13 da ƙawanya da kuma mamayar Amurka a Iraki.

Wannan al'amari ya zama abin kunya da misali ga mulkin mallaka da munafurcin da Amurka ke nunawa wajen ɗaukaka kanta a matsayin abin da ake kira tushen manufar ‘yantar da ƙasar Iraki, kafin a gano sojojinta na dukan fursunonin Iraki tare da cin zarafinsu.

A cewar ƙungiyar agaji ta Red Cross, kashi 70 zuwa 90 cikin 100 na fursunonin Abu Ghraib da aka tsare, waɗanda ba su ji ba ba su gani ba ne aka kama su bisa kuskure kana suka faɗa kuncin rayuwa da azaba da kuma cin zarafi daga hannun jami'an sojin Amurka.

Rahoton ICRC na 2004 ya bayyana cewa akwai tarin misalai na cin zarafi a Abu Ghraib waɗanda suka keta Yarjejeniyar Geneva, gami da zagi da wulakanci da kuma azabtarwar fitar hankali daga masu tambayoyi.

Sakamakon binciken da hotuna da rahotanni da aka fitar sun haifar da ce-ce-ku-ce a fadin duniya wanda ya kai ga Majalisar Ɗinkin Duniya.

A lokacin, Muƙaddashin Babban Kwamishinan Kare Hakkokin ɗan'adam Bertrand Ramicharan ya ba da bayyana cewa munanan ayyukan cin zarafin fursunoni a Abu Ghraib ka iya zama laifin yaƙi.

An shigar da karar farko kan CACI a shekarar 2008 kana aka jinkirtar da shari'ar har zuwa shekaru 15 saboda takaddamar doka da korar da kamfanin ya yi kan zargin cewa jami'an suna da rigar kariya kana doka ta kare su a yayin da suke aiki a matsayin sojojin Amurka.

Bayan shekara daya, wata kotun daukaka kara ta Amurka ta yi watsi da karar da wasu 'yan Iraki mutum 250 suka shigar, wadanda aka azabtar da su a gidan yarin Abu Ghraib bisa ga dogaro kan dokar bincike da ake kira da "battlefield preemption."

Duk da tsanani da girman cin zarafin da aka aiwatar, wasu kananan jami’an sojoji ne kawai aka gurfanar da su gaban kotu.

Kafa misalai masu muni

Rashin ɗaukar nauyi ko alhaki na zama babbar matsala.

Shari'ar 2024 na zuwa ne a daidai lokacin da duniya ke ganin manya rikice-rikicen da cin zarafi masu muni.

Hakan ya kafa babbar hujja mai haɗari kan cewa za a ci gaba da cin zarafin fursunoni saboda rashin adalci da kariya ga waɗanda lamarin ya shafa. Hakan ya haɗa da cin zarafin Falasɗinawa a gidajen yarin Isra'ila da kuma fursunonin Ukraine da jami'an Rasha ke yi.

Dubban fursunonin Ukraine ne ake tsare da su a gidajen yarin Rasha tun lokacin da aka fara kai farmakin a shekarar 2022, inda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa, jami'an Rashan sun azabtar da su da wutar lantarki da aiwatar da hukuncin duka mai tsanani da ɗaukar tsawon lokaci wurin azabtarwa har ma da barazanar kisa.

Haka zalika, likitocin Isra'ila sun bayyana mummunan yanayin da fursunonin Falasɗinawan daga Gaza suke ciki a cibiyoyin da ake tsare da su na wucin-gadi, yanayin da ya haɗa da kulle a kowane lokaci tare da rufe musu idanuwa da kuma fuskantar azabatarwar jiki da wulaƙanci da kuma cin zarafi.

Su ne Suhail Najim Abdullah Al Shimari, Salah Al-Ejaili da As'ad Al-Zuba'e. Al-Ejaili ɗan jarida ne kafin sojojin Amurka su kama shi kuma ya shaida cewar an yi masa mugun duka, da ɗaure shi da kuma tsare shi cikin yanayi na rashin fahimta duk da cewa ba a tuhume shi da wani laifi ba. Masu shigar da ƙara sun ce sun sha irin wannan cin zarafi.

An fara shari'ar da masu shigar da ƙara suna jayayya cewa CACI na da alhakin cin zarafi duk da rashin iya tabbatar da cewa masu binciken ɗan kwangilar suna da alhakin cin zarafin fursunoni kai-tsaye.

Shaidu sun zo ta hanyar shaidar waɗanda abin ya shafa da wasu janar-janar na sojan Amurka biyu da suka yi ritaya waɗanda suka rubuta cin zarafi a Abu Ghraib tare da alaƙanta CACI da shi.

A cikin rana ta takwas na muhawara duk da haka, alƙali ya ayyana shari'ar da ba ta dace ba bayan da alƙalai na mutane takwas a Alexandria suka kasa yarda da yanke hukunci. Wannan ya zo ne kai-tsaye bayan CACI ta yi jayayya cewa bai kamata ya zama alhakin ayyukan da Sojojin Amurka suka aikata ba kuma ya kamata a rataya alhakin gwamnati a maimakon haka.

Akwai yiwuwar a sake zaman shari'ar, amma matakin rashin kammala shari'ar da alƙalin ya nuna cewa ba za a sake samar wa fursunonin Abu Ghaib adalci ba lamarin da ya girgiza duniya ya kuma keta yarjejeniyoyin Geneva da tona asirin Amurka da munafuncinta.

Hamzah Rifaat na da shaidar digiri a fannin Nazarin Zaman Lafiya da rikice-rikice a Islamabad da Pakistan da kuma Harkokin duniya da Diflomasiya daga jami'ar Bandaranaike da ke Colombo na ƙasar Sri Lanka.

Hamzah ya taba kasancewa wakilin Kudancin Asiya a Cibiyar Stimson da ke Washington, DC a cikin 2016.

Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya yi daidai da ra'ayi ko ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika ba.

TRT World