Ana hasashen aikin hako ma’adinin lithium na Ewoyaa a Ghana zai samar da tan miliyan 25.6 na tama. Hoto: Reuters      

Daga Dr. Peter Asare-Nuamah

A ’yan kwanakin nan, duniya na kara bayyana bukatar ma’adinin lithium saboda yadda yake da matukar muhimmanci wajen yunkurin samar da cigaba mai dorewa ba tare da illa ga muhalli ba.

A daidai lokacin da duniya ke ta fafutikar yaki da sauyin yanayi ta hanyar amfani da hanyoyi marasa illa ga muhalli, daya daga cikin manyan cigaban da aka samu shi ne amfani da motoci masu amfani da lantarki.

Irin wadannan motocin, ba kamar wadanda suke amfani da fetur ba, suna amfani ne da batirin da ke amfani da sinadirin lithium, wanda ba shi da illa ga muhalli.

Hakan ya sa kasashen da suka shige gaba a bangaren samar da irin wadannan motocin suke da damar taimakawa wajen kawo sauyi a kan matsalolin gurbacewar muhalli da duniya ke fuskanta.

Haka kuma bayan kasancewar motoci masu amfani da lantarki za su rage yawaitar sinadaran carbon masu gurbata muhalli, suna kuma taimaka wajen habaka tattalin arziki da cigaban kasa.

Shi ya sa ba abin mamakin ba ne ganin yadda manyan kasashe irin su Amurka da China da Tarayyar Turai suke gogoriyon samun lithium din saboda habaka tattalin arzikinsu.

Misali, an kiyasta cewa zuwa shekarar 2030, Tarayyar Turai za ta bukaci kusan ninki 18 na lithium da take samu a yanzu domin cimma muradinta na adana makamashi da kuma hada batiran motoci masu amfani da lantarki.

Sannan zuwa shekarar 2050, tarayyar za ta bukaci kusan ninki 60 na ma’adanin.

An kiyasta cewa bukatar lithium na Tarayyar Turai zai ninku sau kusan 20 zuwa 2030. Hoto: Reuters

Ganin yadda ake gogoriyon ma’adanin a duniya ne ya sa kasashen da suke da shi suke tunanin amfani da shi wajen habaka tattalin arzikinsu da zamantakawarsu.

Daga cikin kasashen nan akwai Ghana, wadda a kwanakin baya ta sanar da fara hako ma’adanin.

A watan Satumban shekarar 2022, kamfanin Atlantic Lithium ya kammala gwajin farko na yiwuwar hako ma’adinin lithium a yankin Ewoyaa da Kaampakrom da Abonko da ke kasar Ghana.

Bayan wannan wanda somin-tabi ne, kamfanin ya sake yin gwajin na kwakwaf, wanda shi me ya nuna sakamako mai kyau.

A sanarwarsa a watan Yunin 2023, kamfanin Atlantic Lithium ya ce bayan bincikensa na karshe ya gano akwai kusan tan miliyan 25.6 na ma’adanin tama wanda yake dauke da matakin kashi 1.22% na ma’adinin lithium oxide.

Haka kuma an ruwaito za a iya rika fitar da tan miliyan 2.7 na ma’adinin a duk shekara daga nan zuwa shekara 12 masu zuwa.

Bayan gano isasshen ma’adinin da za a iya shigarwa kasuwa, sai gwamnatin kasar ta Jam’iyyar New Patriotic Party (NPP) ta shiga yarjejeniya da Barari DV Limited, wanda wani sashe ne na kamfanin Atlantic Lithium domin fara aikin a rubu’i na uku na shekarar 2024 domin fitar da lithium na farko a rubu’i na biyu na shekarar 2025.

Yaya amincin wannan yarjejeniyar take, sannan yaya za ta taimaka wajen ciyar da kasar Ghana, da kuma mutanen yankin na Ewoyaa gaba?

A cikin yarjejeniyar an kulla cewa kasar Ghana tana da kashi 10 na ribar da za a samu, da kashi 13 na ma’adinin ba tare da zuba jari ba, da kuma wani kashi 6 na arzikin a cikin tsarin Minerals Income Investment Fund (MIIF).

Jimilla, Ghana na da kashi 19 na ma’adinin na Ewoyaa. Sannan bayan haka, kamfanin na Atlantic Lithium zai ware kashi 1 na ribar da ya samu wajen samar da ababen more rayuwa a yankunan da ake aikin.

Yarjejeniyar aikin hako ma’adinin ta nuna Ghana na da kashi 10 na riba. Hoto: Reuters

Ana danganta yarjejeniyar ta hako ma’adinin na Ewoyaa, musamman a tsakanin masu madafun ikon kasar da yarjejeniya mafi inganci a tarihin kasar.

Suna cewa hakan ne saboda ma’adinan kasar da aka hako a baya, irin su zinare da lu’u-lu’u da sauransu, kashi biyar take samu, da kuma kashi 10 na arzikin ma’adinanin ba tare da ta zuba jari ba ba wajen aikin.

Wasu masana a bangaren, irin su Sa Sam Jonah, wanda tsohon shugaban kamfanin AngloGold ne, ya yaba wa gwamnatin kasar bisa kokarin da ta yi wajen daukar matakin farko na mallakar ma’adinin a nan gaba ta hanyan yarjejeniyar ta Ewayaa.

Wannan ya sa lamarin ke faranta ran mutanen kasar ta Ghana, wadanda suka dade suna korafin cewa kasar ba ta da kaso, ko kuma takan samu kaso kalilan ne kawai a bangaren ma’adinanta, wanda hakan ya sa ‘yan kasar ba sa cin moriyarsa.

Sai dai akwai bukatar karin bayani a kan yadda yarjejeniyar za ta zama daban wajen samar da ababen more rayuwa a yankunan aa ake aikin irin su Obuasi, Bogoso, Prestea da sauransu.

Domin tabbatar da cewa yankunan sun samu rabonsu, musamman wajen ciyar da su gaba ta hanyar samar musu ababen more rayuwa, lallai neman karin bayani yana da muhimmanci.

Daga cikin manyan tambayoyin da suke bukatar amsa akwai shin wadanne irin ci-gaba za a samar a yankunan Ewoyaa, Abonko da Kaampakrom nan da shekara 12 da za a kammala aikin?

Ta yaya aikin zai habaka aikin noma da kiwon lafiya da tsaftace muhallin da sauran ababen more rayuwar mutanen yankunan?

Ta yaya za a tabbatar mutanen yankunan sun samu shiga cikin tsarin?

Haka kuma ganin an samu rahotannin da ke nuna cewa aikin hako ma’adinin lithium ya jawo gurbacewar muhalli a wasu wuraren, lallai akwai bukatar karin haske a kan yadda aikin zai shafi muhalli a yankunan kasar ta Ghana.

A daidai lokacin da ake jiran sahalewar Majalisar Dokokin Kasar a kan yarjejeniyar, lallai akwai bukatar ’yan majalisar su duba cikin tsanaki da kuma muhimmantar da bukatun mutanen kasar baki daya.

Wannan zai sa majalisar ta dauki matsaya daya ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba domin tabbatar da kasar Ghana ta ci moriyar ma’adinin sosai, wanda yanzu haka duniya ke kara nemansa.

Ganin yadda duniya ke neman ma’adinin na lithium ya sa lallai akwai bukatar Majalisar Dokokin kasar su dage wajen tabbatar sanya ci-gaban kasar a gaba, musamman cigaban yankunan da ake aikin.

Dokta Peter Asare-Nuamah malami ne a tsangayar cigaba mai dorewa na Jami’ar Environment and Sustainable Development, da ke Ghana, kuma babban mai bincike a Cibiyar Binciken harkokin ci-gaba wato Development Research a Jami’ar Bonn.

Togaciya: Ra’ayin marubucin ba dole ba ne ya zama daidai da ra’ayi da dokokin aikin jarida na TRT Afrika.

TRT Afrika