Abin da ya sa dole Ƙasashen Yammacin Duniya su sake nazari kan goyon bayan da suke bai wa  Isra'ila

Abin da ya sa dole Ƙasashen Yammacin Duniya su sake nazari kan goyon bayan da suke bai wa  Isra'ila

Rundunar sojin Isra'ila na ta gazawa a fannoni da dama duk da cewa tana karbar miliyoyin daloli na tallafi daga Ƙasashen Yammacin Duniya.
Jamus ta fitar da kayayyakin soji da suka haɗa da motoci masu sulke da kayayyakin sadarwa da suka kai dala miliyan 323 a shekarar 2023. / Photo: Reuters Archive

Daga Fatih Semsettin Isik

Rundunar sojin Isra'ila na daya daga cikin manyan masu safarar makamai a duniya da ke samun gagarumin tallafi daga Ƙasashen Yammacin Duniya, na kuɗi da siyasa.

Amurka kaɗai na bai wa Isra'ila tallafin soji na aƙalla dala biliyan huɗu duk shekara.

Jamus ta fitar da kayayyakin soji da suka haɗa da motoci masu sulke da kayayyakin sadarwa da suka kai dala miliyan 323 a shekarar 2023.

Faransa ta sayar da kayayyakin da suka kai na dala miliyan 226 a cikin shekara 10 da suka gabata, yayin da Canada ta ba da izinin fitar da kayayyakin yaƙi zuwa Isra'ila har na dala miliyan 21 sakamakon hare-haren da Hamas ta kai a watan Oktoban 2023.

Sai dai irin yadda Isra'ila ke amfani da ƙarfi fiye da ƙima a kan Falasɗinawa fararen hula da rashin cimma manufar kubutar da dukkanin Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su, ya sanya ayar tambaya kan tasiri da amincin wannan runduna ta soji da ke samun goyon bayan da a yanzu ke shirin bude wani sabon fada a kan iyakar arewacin kasar da Lebanon. .

An fi wata takwas da Isra'ila ta ƙddamar da mummunan yaƙi a kan Gaza, amma har yanzu ba a kai ga cimma manufar da aka yi ta yayatawa ba ta son kawar da Hamas.

Ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa tare da wasu sauran ƙungiyoyihar yanzu suna ayyukansu a zirin. Tana yawan kai hare-haren kwanton-ɓauna a kan dakarun Isra'ila da kuma watsa bidiyoyin lokutan da take aikata hakan a shafukan sada zumunta.

Tun shekarar 2006, bayan Yaƙin Isra'ila da Labanon na Biyu, rundunar soji Isra'ila ta fuskanci bincike daga magoya bayansu da masu suka, a cikin gida da waje.

Ba kisan ƙare dangi kawai ake zarfinta da yi ba, ta jawo ana yi mata kallon rundunar sojin da "take yi wa yara kisan gilla" a idon duniya.

Har ila yau, ko waɗancan 'yan tsirarin da har yanzu suke mata kallon "wacce take aikinta a halasce," suna yin la'akari da ita a matsayin wadda ba ta da ƙwarewa.

Wani abu da yake ƙara dagula wadannan batutuwa, wasu jerin tantancewa na ciki da na waje da aka yi, sun bayyana sojojin Isra'ila a matsayin marasa ƙwarewa.

Misali, wani rahoto na 2006 na Kamfanin RAND ya ba da haske kan gazawar aiki da dabaru, da bijiro da tambayoyi game da shiri da ingancin sojojin Isra'ila.

Wadannan damuwar sun bayyana a cikin wani bayanin sirri da aka bayyana a cikin 2018, wanda ya yi gargadin cewa sojojin Isra'ila ba su da wani shiri na fuskantar ɓarkewar rikice-rikice. Sakamakon binciken ya nuna batutuwan tsare-tsare, ciki har da rashin isasshen horo da tallafin kayan aiki.

Kaɗuwar da suka yi sakamakon ƙaƙƙarfan harin ba-zata na 7 ga Oktoba da Hamas ta kai, ya rusa wannan "izzar ta rundunar sojin Isra'ila ta jin cewa ta fi kowa", lamarin da ya sanya ta yin zaluncin da ba a taɓa ganin irinsa ba, a kokarin rufe zubewar martabarta a idanun Isra'ilawa da gwamnatocin da ke tallafa musu.

A yau, rigingimun sun nuna cewa lokaci ya yi da za a sauya tunanin rundunar sojin Isra'ila a yankin da ma duniya baki ɗaya.

Camfin da ake yi na cewa ba za a taba yin nasara a kan rununar sojin Isra'ila irin haka ba ya rushe, inda ya bayyana rauninta da aka daɗe ana rufewa ta hanyar zafafan kalamai da farfaganda.

Ana buƙatar sake nazari don magance kura-kuran tsarin da ke cikin amincin sojojin Isra'ila.

Bincike ya gano cewa akwai naƙasu sosai a ayyukan rundunar sojin Isra'ila. REUTERS ARCHIVE 

Naƙasu a tsare-tsare

Yaƙin Gaza ya bankaɗa irin gazawa da naƙasun da ke cikin rundunar sojin Isra'ila ta fannin tsare-tsare da ma sha'anin tsaro gaba ɗaya.

A lokacin da aka fara yaƙin a ranar 7 ga watan Okotba, Isra'ila ta samar da wani jawabi na "barazanar da ke akwai" wanda kuma ke da alaka da kaɗuwar da ta kunno kai bayan da mayakan Falasdinawan suka keta iyakokinta cikin sauki a karon farko tun shekara ta 1948.

Akwai isasshiyar hujja cewa Tel Aviv ta faɗa cikin rudani na girman kai kuma ta faɗi ba nauyi a yunƙurinta na nuna cewa ta fi kowa ƙarfin soji. Tun a farkon yakin ma, an yi ta cece-ku-ce kan matsalolin kayan aiki da tsare-tsaren sojojin Isra'ila a kafafen yada labarai na cikin gida.

Muhawarar ta tabbatar da cewa irin wadannan matsalolin sun dade, har ma ta kai ga sojoji sun yanke shawarar layin Whatsapp na gaggawa don magance "ƙorafe-ƙorafe da yawa game da rashin kayan aiki."

Bugu da ƙari, an bayar da rahoton cewa an gudanar da kamfen na ba da gudunmawa don isar da kayan aiki na yau da kullun kamar "ƙananan cajoji da kayan tsafta da kayan amfanin ban-daki".

Ko da yake mai magana da yawun sojojin Isra'ila Daniel Hagari ya musanta irin wannan mummunan halin, kafofin yada labaran Isra'ila sun ruwaito cewa ana aika sojojin zuwa Gaza ko da ba tare da "kwalaben shan ruwa ba".

Wata hira da aka yi kwanan nan da sojojin Isra'ila a yankin abalia na Gaza ta bayyana yadda rundunar sojin Isra'ilan ke fuskantar ɗumbin matsaloli da suka fi ƙarfin na tsare-tsare kawai, inda aka gano har ma da matsaloli a muhimman fannoni kamar na ba da horo.

A cewar Haaretz, an kai sabbin sojoji Gaza ba tare da ba su isasshen horo ba, inda suka samu kansu a cikin tsananin yanayin rashin ƙwarewa da ba za su iya shawo kan matsalar ba, abin da ke nuna rashin bin ingantaccen tsarin aikin soji.

A yanzu rundunar sojin Isra'ila ga alama tana yaudarar kanta ne a kan ikirarin da take yi cewa tana samun gagarumar nasara a kan Gaza.

Bugu da ƙari, karsashin sojoji na taɓarɓarewa, sakamakon yadda ake samun hujja ta ƙaruwar sojojin da suke guje wa aikin. Wani rahoto na baya-bayan nan

Wani rahoto na baya-bayan nan ya nuna rashin jin dadin da ake samu, inda da dama daga cikin masu rajin kare hakkin bil adama ke nuna rashin gamsuwa da irin rawar da suke takawa da kuma halin da sojoji ke ciki a halin yanzu, wanda ya biyo bayan rashin gamsuwa da gwamnatin Isra'ila mai tsatsauran ra'ayi.

Yitzhak Brik, tsohon mai shigar da ƙara na rundunar sojin Isra'ila, wanda ya rubuta rahoton na shekarar 2018, ya kuma nanata wannan damuwar watanni biyu kacal kafin yaƙi ya ɓarke a ranar 7 ga Oktoba.

Matsalolin ɗa'a

Ba kisan fararen hula da aikata laifukan yaƙi kawai ake yi zargin dakarun Isra'ila da aikatawa ba, ana iya ganin rashin tsari ƙarara a tsakaninsu.

Rahotanni sun nuna wani lamari marar dadi na rashin ƙwarewa a tsakanin sojojin.

A cewar The Intercept, sojojin Isra'ila sun yi ƙoƙarin sarrafa labarin game da waɗannan hare-haren ta hanyar ɓoye abubuwan da ba su dace ba. Wani sashin leken asiri na rundunar sojin Isra'ila ya sanar da kafafen yada labarai cewa an haramta ba da rahoto kan wasu batutuwa ba tare da izini ba.

Wadannan sun hada da fallasar abin kunya na yadda Hamas ta yi amfani da makaman da aka kama daga hannun sojojin Isra'ila, da tattaunawa kan taron majalisar ministocin tsaro, da kuma mutanen da Isra'ila ta yi garkuwa da su a Gaza - batun da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha suka kan kuskure.

A daya bangaren kuma, babban lauyan sojin Isra'ila ya yi gargadi ga sojojin dangane da halin da suke ciki a Gaza, lamarin da ke nuni da tabarbarewar tarbiyya da kuma bukatar bin dokokin kasa da kasa bayan da aka samu rahotannin kwasar ganima da barna da sojojin Isra'ila ke yi.

A wannan gaɓar, an ga yadda sojojin Isra'ila suka dinga ɗaukar bidiyon kansu suna lalata kayayyakin Falasɗinawa, har ma suke wallafa bidiyoyin a intanet.

"Ina ga duk wani soja da ke cikin wannan tawagar ya ɗauki kofunan shan gahawa," in ji sani soja mai muƙamin sajan na Isra'ila a Gaza a wata hira da Mujallar The Economist ta yi da su. Ofishin watsa labarai na gwamnatin Falasɗinu ya ce aƙalla dala miliyan 25 da gwala-gwalai aka sace a wata ukun farko na fara yaƙin.

Ana zargin Isra'ila da kisan ƙare dangi a Gaza. AA ARCHIVE

Siyasantar da sha'anin soji

Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da asarar ƙwarewar sojojin Isra'ila shi ne yawan shigar da kafofin watsa labarai cikin lamarinsu da kuma shigar su harkokin siyasa. Wannan wuce gona da iri ba wai kawai ya bata mata suna ba har ma ya bayyana rauninta.

A cewar wani rahoton Ynet, sojojin Isra'ila sun fito fili sun bayyana matsalolin da suke fuskanta na tattalin arziki, inda suka bayyana bukatunsu ta hanyar da za su nuna gazawarsu wajen gudanar da ayyukansu. Wannan fayyacewa, duk da cewa dabara ce, amma sai ta nuna zallar dogaro da sojojin ke yi da kuma gazawar su.

Haka kuma, yadda sojojin Isra'ila ke bibiyar shafukan sada zumunta ya ƙara dagula ƙima da amincinsu. Jaridar Times of Isra'ila ta rawaito cewa sojojin sun yi amfani da kalamai na ban dariya a shafukansu na sada zumunta, mai yiwuwa don karfafa halaccin abin da suke yi.

Duk da haka, ana ganin wannan tsari a matsayin ƙuruciya darashin ƙwarewa,anda bai girma ba kuma marar kwarewa, tare da rage ƙarfin faɗa a jinsu zuwa wata farfagandar siyasa kawai.

Mafi mahimmanci, sojojin sun samu kansu a tsakiyar shugabannin siyasar Isra'ila masu adawa da juna. Sojojin da suka yi ritaya sun yi ta tofa albarkacin bakinsu game da wannan batu, tare da yin kakkausar suka ga Netanyahu.

Sun bayyana cewa Netanyahu yana amfani da ayyukan soji don biyan bukatunsa na siyasa, da nufin gamsar da tushensa na kishin kasa da kuma hana jam'iyyun da ke da ra'ayin mazan jiya yin watsi da gwamnatinsa.

Da yawa daga cikin manyan hafsoshin sojan sun yi na’am da wannan ra’ayi, suna ganin cewa, siyasantar da ayyukan soji ya haifar da cikas ga inganci da amincin sojojin.

Ya zama wajibi Ƙasashen Yammacin Duniya su sake duba irin gagarumin goyon bayan da suke bai wa sojojin Isra'ila saboda gazawar aiki da da'a.

Sojojin Isra'ila, duk da samun tallafin kudi da kuma fitar da makamai daga kasashe kamar Amurka, Burtaniya, Jamus, da Faransa, sun nuna mummunar gazawa na dabaru, da na ladabtarwa a Gaza, suna bayyana kansu a matsayin daya daga cikin "zuba jari" mafi muni a tarihi a duniya.

Don haka, sake tantance wannan tallafin yana da matukar muhimmanci don magance al'amurran da suka shafi tsari kafin a kasa shawo kan tsaron yankin saboda gazawar wannan runduna.

Fatih Semsettin Isik mataimakin mai bincike na Cibiyar Bincike ta TRT World. Kafin sannan, ya yi aiki a amtsayin mataimakin mai bincike da kula da shafukan sada zumunta a Dandalin Al Sharq Forum. Yana da digiri a fannin Kimiyyar Siyasa daga Jami'ar Bilkent da kuma digiri na biyu a wannan fannin daga Jami'ar Sehir ta Istranbul da kuma Jami'ar Central European. Yana da sha'awar bincike a kan siyasar Isra'ila da dangantakar Tarayya da Gabas ta Tsakiya da Siyasar Turkiyya da kuma rawar da mazauna kasashen waje suka takawa a harkokin waje.

TRT Afrika