An shirya gudanar da taron ba da lambobin yabo na wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya a shekarar 2024 domin karrama manyan ‘yan wasa a duniya, kuma Afirka na da manyan ‘yan wasa waɗanda suka nuna hazaƙa a fannin wasannin guje-guje da tsalle-tsalle.
An zaɓi manyan 'yan wasa biyu daga kowane nau'in wasanni a zagayen farko na kaɗa kuri'un zaɓen 'yan wasa, wanda ya kunshi kuri'u daga hukumar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya, da na ƙungiyar wasanni da duniya da kuma kuri'un jama'a a shafukan soshiyal midiya.
Bayanan 'yan wasan
Letsile Tebogo daga (Botswana)
Ɗan wasan mai shekaru 21 da haifuwa ya shiga wasan da ƙafar ɗama inda ya kafa tarihi a Afirka tare da samun lambar yabo ta zinare a Gasar Olympic na 2024 a tseren mita 200 a birnin Paris.
Gudunsa da kuma hazaƙarsa ya ɗau hankalin al'ummar duniya.
Ta hanyar lashe tseren mita 200 a gasar Olympics ta Paris, Letsile Tebogo ya kafa tarihin samun lambar yabo ta zinare na farko da Bostwana ta samu a kowane wasan gasar na Olympics a bana.
Ya kafa tarihi a gasar tsere na Afirka da mintoci 19.46 — lokacin da ya ba shi damar zama na biyar a jerin 'yan wasa mafi gudu a duniya — sannan wasan ya biyo bayan da ya zo na shida a ƙarshen tseren mita 100.
Ya kuma ba da gudummawa ga nasarar Botswana a wani ɓangare na nasarar tawagar tseren mita 4x400 ta maza wadda ta lashe lambar yabo ta azurfa.
Ruth Chepngetich daga (Kenya)
'Yar tseren gudun dogon zango ta Kenya ta matukar kafa tarihi a duniya tare da nuna hazaƙa a wasannin da ta yi, wanda ya tabbatar da matsayinta na ɗaya daga 'yan wasa a matsakin gudun dogon zango da ke kan gaba a duniya.
Ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko da ta yi gudun mil 26.2 a kasa da mintuna 2:10, inda ta yi nasarar samun kambunta na uku a gasar tseren dogon zango na Chicago tare da taka rawar gania cikin mintuna huɗu. wani abin sha'awa ita ce, maza tara ne kawai suka yi fi ta gudu a tseren.
Tamirat Tola daga (Habasha)
Ɗan wasan tseren dogon zango na ƙasar Habasha ya lashe lambar yabo ta zinare a gasar Olympics a wani lokaci da ya kafa tarihi, inda ya nuna gagarumin jarumta da juriya.
Duk da cewa an ƙira shi cikin tawagar Habasha a Paris don maye gurbin wani, amma Tamirat Tola ya yi amfani da wannan damar ta hanyar da ta dace wajen lashe tseren dongon zango na gasar Olympic a awanni 2:06:26.
Cikakken jerin sunayen wadanda aka zaba
'Yan wasan tseren mata na shekara
Julien Alfred (Saint Lucia) - Zakaran Olympics na 100m
Sydney McLaughlin-Levrone (Amurka) - Zakaran tseren tseren mita 400 na Olympics
'Yan wasan tseren maza na shekara
Jakob Ingebrigtsen (Norway) - Zakaran tseren mita 5000 na Olympics
Letsile Tebogo (Botwana) - Zakaran tseren mita 200 na Olympics
’Yan wasan a fagen wasannin tsalle-tsalle na mata na shekara
Yaroslava Mahuchikh (Ukraine) - zakara a gasar Olympics na tsalle- tsalle mai tsawo
Nafissatou Thiam (Belgium) - Zakara a heptathlon na Olympics
Gwarzon ɗan wasan tsalle-tsalle na maza na shekara
Mondo Duplantis (Sweden) - Zakaran tseren sanda na Olympics
Miltiadis Tentoglou (Girka) - Zakaran tsalle-tsalle mai tsawo na Olympics
Gasar tsere Mata a wajen fili ta Shekara
Ruth Chepngetich (Kenya) – mai riƙe da kambun tseren ɗogon zango a duniya
Sifan Hassan (Netherland) - zakara a tseren ɗogon zango na gasar Olympics
Gasar tsere Maza a wajen fili ta Shekara
Brian Pintado (Ecuador) - Zakaran tseren kilomita 20 na Olympic
Tamirat Tola (Ethiopia) - zakaran tseren ɗogon zango na Olympics
Za a bayyana ‘yan wasa da suka yi nasara a kowane fanni, da kuma wanda ya yi nasara gaba ɗaya a wasannin, a wani biki da za a yi a Monaco a ranar Lahadi, 1 ga watan Disamba, a matsayin wani ɓangare na karrama 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle a Duniya na 2024.