Daga Kudra Maliro
Yawan hare-haren da kadojin cikin tafkin ruwan Edouard da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyya kongo ya sa hukumomi a kasar suka yanke shawarar kafa kejin karfe a bakin tekun da mazauna yankin ke amfani da su.
Mutane 10 ne suka mutu a hare-haren kadojin a tsawon watanni uku da suka gabata a Kyavinyonge da ke yankin Beni na Kivu ta Arewa.
"Mun tattara bayanai na mutane kusan 10 da kadoji suka kashe tun daga watan Nuwamba 2023 zuwa yanzu. Yawancin wadanda aka kashe din, masunta ba bisa ka'ida ba," kamar yadda Jérémie Tsororo, wani dan jarida mai zaman kansa da ke Kyavinyonge ya shaida wa TRT Afrika.
Ya ce harin baya-bayan nan ya faru ne a karshen makon da ya gabata kuma ya rutsa da wani masunta ne.
Kejin karafa
Ko da yake ba kasafai ake samun rahoton hare-hare kan masu zuwa diban ruwa ko wanke tufafi a tafkin ba.
Mai magana da yawun Cibiyar Kare Halittu na kasar Kongo (ICCN) da ke Arewacin Kivu, Bienvenue Bwende, ya ce za a kafa kejin karafa a bakin rairayin ruwan tek don takaita hare-haren kadoji.
Tafkin Edouard na daya daga cikin manyan tafkunan Afirka. yana yankin kwarin Great Rift da ke tsakanin iyakar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (wanda ke da kusan kashi 71 cikin 100 na ruwan) da Uganda (wacce ke da kashi 29 cikin 100).
Tafkin ruwan na tsakanin gandun dajin Virunga na Kongo da gandun dajin Sarauniya Elizabeth a Uganda.
Ayyukan Ruwa
Kamun kifi wani muhimmin aiki ne ga al'ummar yankin.
Hukumar ICCN ta ce tana shirin tona ayyukan ruwa a yankunan da ke kewaye domin rage yawan yaran da ke zuwa neman ruwa a tafkin.
''A karshe, ya kamata ICCN ta dauki batun yawan hare0haren kadoji a tafkin Edouard da muhimmanci," in ji Bienvenue Bwende.
Ka'idoji da dokokin kamun kifi
"Tabbas an samu rahotanni kan wasu mutane da hare-haren da kadoji suka rutsa da su daga ciki akwai wadanda suka mutu wasu kuma suka ji rauni kuma duk yawanci kan mutanen da ke zuwa kamun kifi ne ba bisa ka'ida ba, galibi a wuraren da aka haramta kamun kifi,'' a cewar Bwende.
"Yayin da take nuna rashin jin dadinta game da wadannan abubuwan da suka faru, hukumar ICCN ta yi kira ga masunta da su mutunta ka'idojin kamun kifi a tafkin Edouard, wanda shine hanaya na kadai na tabbacin kare lafiyarsu," in ji shi.