Masu yawon buɗe-ido suna tafiya kan rairayin bakin teku a tsibirin Silhouette Island, tsibiri mafi girma a Seychelles. / Hoto: AFP

Yawon buɗe-ido a Afirka ya farfaɗo sama da na kafin Covid-19, a cewar wasu alƙaluma daga Majalisar Ɗinkin Duniya.

Nahiyar ta samu ƙarin kashi 7% a yawan masu shigowa a 2024, idan an kwatanta da 2019, shekara guda kafin ɓarkewar annobar Covid-19, wadda ta janyo dokar kulle a wasu ƙasashen Afirka da ma mafi yawancin na duniya.

Afirka ta samu ƙarin maziyarta kashi 12% a 2024 sama da 2023, kamar yadda ma'aunin hukumar MDD kan yawon buɗe-ido a duniya ya nuna.

Arewacin Afrika ya samu mafi girman ƙari a nahiyar, da kashi 22% a 2024, sama da na 2019.

Alƙaluman suna yin nuni da gamagarin yanayi a duniyar yawon buɗe-ido, inda aka samu farfaɗowar kashi 99% a 2024, idan an kwatanta da adadin 2019. An ƙiyasta cewa an samu masu yawon buɗe-ido biliyan 1.4 a faɗin duniya a 2024.

Majiya: UN Tourism | World Tourism Organization

Ƙasashen Afirka sun saba samun maziyarta daga faɗin duniya saboda akwai gandun namun daji, da yanayin ƙasa mai ƙayatarwa, da al'adu, da rairayin bakin teku.

Alal misali, harkar yawon buɗe-ido ta samu adadi mafi girma a 2023, bayan samun har miliyan 14 na adadin 'yan yawon buɗe-ido.

Ƙasar tana da aniyar cim ma adadin maziyarta miliyan 17.5 nan da 2026, bayan ƙaddamar da sabbin wuraren da jiragen sama ke zuwa, da kuma miliyan 26 nan da 2030, lokacin da za ta karɓi baƙuncin Kofin Duniya tare da Sifaniya da Portugal.

Kuɗin-shiga da Kenya ta samu ya ƙaru da kusan kashi uku a 2023, bayan samun maziyarta miliyan 1.95. Ta yi fatan samun masu yawon buɗe-ido miliyan 2.4 a 2024, amma ba a samu tabbacin ko an cim ma wannan buri ba.

Ƙasashe kamar Zimbabwe sun faɗaɗa abubuwan da suke samarwa, don ba da dama ga mazauna yankin su mori wuraren buɗe-idon.