Daga Awa Cheikh Faye
Désiré Kabengele Sebazungu ya hada wani injin motsa jiki na katako wanda ya laka wa suna Desiré Run" wanda yake aiki da karfin tafiyar kafa. Matashin mai shekara 26 fitaccen mai wasan motsa jiki ne wanda yake da sha’awar kirkira.
Ya samu yanke wannan shawarar tare da karfin sha’awar da yake da ita ta motsa jiki. Yana kuma daga cikin masu gudun famfalaki a Goma.
Désiré Kabengele ya shafe makonni uku kafin ya kera injin motsa jikin mai amfani da lantarki, wanda zai iya shafe shekaru yana aiki, ba ya gurbata muhalli.
Guje wa rashin tsaro
Tuni Désiré ya shiga wasu daga cikin gasanni na guje-guje. Sai dai wasanni wadanda ake yin su a fili ko kuma a waje ba lamari bane mai sauki a wuraren da yakin masu rike da makamai ya daidaita inda jami’an tsaro ke kokarin dakile su.
“Al’ummarmu na da matsaloli da dama haka kuma ba a bar wasanni a baya ba...masu wasannin guje-guje na shan wahalar yin atisaye akai-akai saboda rashin tsaro,” kamar yadda Désiré ya shaida wa TRT Afrika.
Ya tsara injin dinsa na motsa jiki domin ya yi tafiya ko kuma gudu a kansa a cikin gida domin guje wa barazanar da ke tattare da rashin tsaro.
Wani kuma amfanin wannan injin din motsa jikin na katako shi ne yaki da cututtuka masu alaka da zuciya ta hanyar motsa jiki akai-akai.
“Mutanen Goma sun saba da motsa jiki da safe, sai dai akwai matsalolin tsaro da dama a yankin, wanda hakan ke nufin mutane ba za su iya motsa jiki a kullum ba kamar yadda suke so. Injin din motsa jikin na katako wata hanya ce ta zama cikin lafiya da motsa jiki,” in ji shi.
Gaba da Goma
Injin din motsa jikin yana da tsawo a kwance na 120 cm, da fadin 64 cm sai tsayin 115 cm, kuma an yi shi ne da katako da ke da karfin daukar abu mai nauyi.
Wannan injin din motsa jiki ne na gwaji. Désiré ya kammala karatun shekara hudu kan ilimin kere-keren lantarki a ISTA-Goma kuma yana ci gaba da kara inganta kirkirarsa ta injin din katako.
Duk da kalubalen da yake da shi na kudi, burin Desiré shi ne ya samar da karin injinan na katako ta yadda karin mutane da ke Goma da kuma wajen Goma su amfana.