Masu fasahar sun dade suna sana’ar hada kayayyakin adon tsawo gomman shekaru. Hoto: AP    

A birnin Fez da ke Arewacin kasar Maroko, kwararrun masu fasaha sun dade suna sana’anta kayayyakin ado na gomman shekaru.

Wannan dadaddiyar fasahar, ana gadar ita ne tun shekaru aru-aru, inda ta zama kan gaba wajen nuna al’adu na mutanen kasar Maroko.

Kayayyakin adon yana cikin kayayyakin da Hukumar UNESCO ta amince da su. Hoto: AP

“Zane-zanen kayayyakin ado dadaddiyar sana’a ce wadda ta kunshi zane a karafa da azurfa da zinare. An fara sana’ar ce a tsakanin karshen Karni na 12 zuwa farkon Karni na 13 a Maroko.

A birnin Fez aka fara, sannan daga bisani ta bazu zuwa wasu biranen na Maroko, musamman birnin Marrakesh,” inji Mohamed Arnani, mai shagon hada kayayyakin ado a Fez.

Ana yin zane-zanen a jikin jan karfe mai inganci. Hoto AP

Fasahar ta kunshi sana’anta zane-zane, domin hada kayayyakin ado masu bayyana al’adu da tarihi.

“Fasahar ta kasu zuwa uku, wanda ta fi fice ita ce irin zane-zane da aka fi sabawa da su na siffofin yau da kullum, akwai kuma zane-zanen fulawa, sai kuma zayyanar kirkira, wadda ake kirkira ta hanyar tunane-tunanen zuci,” in ji Arnani.

Idan za a fara, akwai bukatar mai sana’ar ya lura matuka wajen zakulo karfe mai inganci.

Kowane kayan ado yana da abin da yake nufi. Hoto: AP

“Abu na farko shi ne zanen, inda mai fasahar zai yi tunanin irin zanen da zai kirkira. Sai kuma yanka, sannan na karshe shi ne fitar da ainihin abin da yake so, wanda ya kunshi aikin harhada aikin waje daya,” inji Moncef Adyel, wanda yake da shagon aikin karafa.

Masu sana’ar suna fitar da kayayyaki masu kyau daban-daban ne ta hanyar zane-zanen, inda kowane mai zanen yake da tasa fasahar.

Masu fasahar suna kokarin kawo daidaito tsakanin al’adu da cigaban zamani. Hoto AP

Akwai yadda ake farawa daga kanana, sannan a hada su domin fitar da kayayyakin ado, wadanda suke kayatarwa matuka.

A ’yan shekarun nan, masu sana’ar suna ta kokarin samar da daidaito tsakanin al’adun da cigaban zamani.

Kasar Maroko tana yin kokarin tallata fasahar. Hoto: AP

“Kasancewar muna kokarin zamanantar da sana’ar, wannan ya sa muke kokarin sanya fasahohin zamani a ciki, misali muna neman hanyar da za a rika zanen ta hanyar amfani da kayayyakin zamani maimakon na dauri,” in ji Adyel.

“Misali, fasahar samar da kwan filita mai fitar da na’ukan haske da ya fi fice a Maroko shi ne tun wanda aka saba da shi a Masallatai. Yanzu mun kirkiri sababbi masu kyau,” in ji shi.

Kasar Maroko na kokarin tallata fasahar a cikin kasar da ma kasashen duniya.

Tuni kasar ta kuduri aniyar adana dadaddiyar fasahar mai tarihi.

Sana’ar ta Maroko tana fuskantar barazana. Hoto: AP

“Sai dai kuma fasahar tana fuskantar barazanar bacewa, duk da cewa kasar tana ta kokarin hana yiwuwar hakan. Sanya fasahar a cikin kayayyakin tarihin duniya ya kara taimakawa wajen adana ta, sannan hakan ya kara daga kima da darajar masu fasahar,” in ji Mustapha Jellok, darakta a Ma’aikatar adana tarihi, matasa, al’adu da sadarwa a Rabat.

Kasuwannin birnin Fez suna cikar dango wajen baje-kolin saya da sayar da kayayykin adon, wadanda kasar Maroko ke fatar za su zama kayayyakin nuna al’adun kasar na har abada.

TRT Afrika