Dubban mutane ke amfani da TikTok a Somalia. Hoto/Reuters

Wasu daga masu amfani da TikTok na ganin cewa suna zaune a duniyar da ke da dama mara iyaka, inda suke da ‘yancin yin komai.

Wannan ne muhimmin fasali na TikTok, wanda duniya ce ta intanet da ke cike da launuka da halaye daban-daban marasa tsoro ko damuwa ko kalubale ko kuma ciwon zuciya.

Ga wasu, TikTok wata manhaja ce ta rayuwa, wadda suke amfani da ita wurin baje-kolin abubuwa da dama domin samun kudin sayen abinci.

Amma TikTok na fuskantar caccaka, inda a halin yanzu a wasu kasashe ana dakatar da amfani da manhajar.

TikTok ya kara habaka ta fannin samun kudin shiga da kuma adadin masu amfani da shi. Hoto/AP

Karin dakatarwa

Ga masu amfani da TikTok a Somalia, ita ce kasar ta baya-bayan nan da ta haramta TikTok. “Za a shiga cikin duhu a gidaje da dama saboda haramta TikTok,” kamar yadda Abdullah Ali Mohammed ya bayyana a Mogadishu.

“Muna kira ga gwamnati kan cewa ka da ta haramta TikTok saboda a nan muke samun abincinmu,” kamar yadda ya roka.

Gwamnatin Somalia na aiki “domin kare halayyar al’ummar Somalia idan suna amfani da manhajojin intanet,” kamar yadda ministan sadarwa na Somalia Jama Hassan Khalif ya bayyana.

Bukatun kasuwanci

Mai sayar da zinare Halimo Hassan ya bayyana cewa akwai bukatar a sake dubawa sakamakon wadanda suke rayuwa a Tiktok ta hanyar sayar da kayayyakinsu.

TikTok na fuskantar gasa daga sauran manyan kafafen sada zumunta. Hoto/AA

“Haramcin da aka saka kan TikTok zai yi tasiri kan kasuwancinmu sakamakon muna sayar da kayayyakinmu kan TikTok. Muna tallata kayayyakinmu kan TikTok, inda mutane ke kallo daga ko ina a fadin duniya.

“Mutane daga kasashen waje da na cikin gida suna zuwa wurinmu ta hanyar tallace-tallacenmu. Kuma mutane suna zuwa wurinmu da hotunan da muka wallafa a TikTok su kuma saya daga wurinmu,” kamar yadda ya bayyana.

Kamar yadda Bankin Duniya ya bayyana, sama da kashi 20 cikin 100 na masu shekarun aiki a Somalia ba su da aikin yi, inda kafafen watsa labarai suke taka muhimmiyar rawa wurin rage wannan adadin.

TRT Afrika da abokan hulda