Daga Kudra Maliro
Ghana ta karbi bakuncin taron gasar wasannin Afirka karo na 13 wanda ke dauke da ƴan wasa kusan 4,000 a fannonin wasanni 29, an soma taron ne daga ranar 8 zuwa 23 ga watan Maris.
Taron wanda kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ke shiryawa a madadin kasashe mambobinta duk bayan shekaru hudu ya wuce wasanni, a cewar shugaban kasar mai masaukin baki Nana Akufo-Addo.
"Wadannan wasannin za su baje kolin al'adu da basirar wasanni na nahiyar Afirka da kuma banbance- banbancen da ke cikinta," in ji shugaban Ghana a Accra babban birnin kasar inda aka soma wasannin a ranar Juma'ar da ta gabata.
Akwai ƴan wasa da ke wakiltar kasashe daga ko ina daga fadin nahiyar a fannonin wasannin daban-daban.
Daga cikin wasannin akwai na kwando da ƙwallon ƙafa da wasan tennis da kuma ɗaga nauyi da tseren keke da ninkaya da kokawa da dai sauransu.
Wasu daga cikin wadanda suka yi nasara za su damar shiga gasar Olympics za a yi a birnin Paris a 2024, a cewar masu shirya gasar, sannan taron zai samu tallafi daga jami'ai 3,000 da masu aikin sa kai 2,000.
A bangaren kwallon kafa, kasashe takwas da ke rukunin maza da suka hada da Ghana mai masaukin baki da Nijeriya da Senegal da Gambia da Kongo da Uganda, Sudan ta Kudu, da kuma Benin ne za su fafata da junansu domin zama zakara a gasar.
Ana gudanar da gasar wasannin Afirka ne karo na 13 a biranen Accra da Kumasi da kuma Cape Coast.