Tokozile Ngwenya, marubuciya ta bayyana cewa litattafai sun zama kamar mudubi da masu karatu ke kallon rayuwarsu a ciki. Hoto: Tokozile Ngwenya

Daga Tokozile Ngwenya

Na girma a shekarun 1990 a Afirka, musamman ma a Zambia, na tsunduma wajen karanta litattafai da marubutan Yammacin Duniya suka rubuta. Litattafan da ke dakin karatun makarantarmu kusan duk na marubutan Yammacin Duniya ne.

Da wahala na iya tuna cin karo da wani littafi na marubutan Afirka a lokacin da nake tasowa, sai dai a lokacin da nake sakandire na karanta littafin "Things Fall Apart" na Chinua Achebe wanda malamin Turancinmu na ba mu shawarar karantawa.

An rika karatu sosai a aji, kuma hakan ya ci gaba - littafin Achebe ya bude sabon shafi mai kyau. Idan har wannan abu ya kubuce maka, bari na ba ku takaitaccen bayani cikin gaggawa: littafin ya yi bayani kan rayuwar Okonkwo, shugaba mai karfin fada a ji sosai wanda an san shi da zama jarumin dambe da ya lashe gasar dambe sosai.

Okonkwo da jama'arsa sun fuskanci karfin ikon Turawan mulkin mallaka da Kiristoci 'yan mishan. Littafi ne na musamman a Afirka, kuma ina ba ku shawara ku neme shi don karantawa.

Kungiyar karanta litattafai ta kasa da kasa

Kungiyar Litattafai ta 'The Africana Woman Book Club", da aka kafa a watanni ukun farkon 2021, na kokarin magance bukatar al'umma. Duk da cewa sunanta na mata ne, amma kungiyar ba ta mata kawai ba ce; tana da mambobi maza da yawa.

Tana da mambobi 282 masu karatu a Afirka da Turai da Asiya, inda kungiyar ke alfahari da mambobi daga bangarori daban-daban da kuma mutane masu matsayi daban-daban da ke da shekaru tsakanin 30 zuwa 50.

Ana zabar litattafai da za a karanta ta hanyar jefa kuri'a. A 2022, kungiyar ta zurfafa wajen karanta litattafai bakwai daga cikin takwas da 'yan Afirka suka rubuta, kuma a 2023, adadin ya karu zuwa takwas daga goma sha biyu.

Kungiyar 'Africana Woman Book Club' na da mambobi a Afirka, Turai da Asiya. Hoto: Africana Woman Book Club

Chulu Chansa da ta kafa kungiyar ta bayyana cewa wannan sabon ci-gaba na nuni ga karuwar karfin gwiwa a tsakanin al'umma wajen amfana da fahimtar adabi ta fuskar Afirka.

Chansa ta karfafa alakar labaran Afirka, da suke bai wa masu karatu ko saurare karsashi sabo da jin suna da alaka da juna, musamman ga wadanda suke kasashen waje.

Ta kara da cewa "Litattafan da halin da aka kalla wajen rubuta suna da alaka da juna, za ka ga wuraren da ka sani ko yanayin da ka fahimta, musamman sauran mambobinmu da ke kasashen waje suna jin kamar suna gida, idan suna karanta litattafan."

Alakantuwa

Misali, litattafan da kungiyar ta ware don karantawa a 2023 sun hada da "Americanah," da Chimamanda Ngozi Adichie ta rubuta, wanda ke bayani kan tafiyar Ifemelu mara dadi daga Nijeriya zuwa Amurka.

Ifemelu, babbar jigo a cikin littafin, ta fuskanci wariyar launin fata da ma bambanci a abubuwa daban-daban a karon farko.

Ta fahimci Amurkac inda cikin sauri ta koyi cewa "mafarkin Amurka karya ne", kuma domin ta samu damar sabawa tare da sajewa a cikin jama'a, tana bukatar ta sauya halayenta da kamanninta sannan ta rungumi siyasar Amurka.

Mambobin kungiyar sun fahimci dalilan gwagwarmayar Ifemelu, suna kwatanta tasu gwagwarmayar da labaran da suka karanta. Yadda aka siffanta mutane batu ne mai muhimmanci, kuma marubutan Afirka na bayar da dama ga masu karatu don su kalli kawunansu a cikin labaran da suke karantawa.

Chansa ta ce "Mambobi na alakanta kawunansu da jigogin cikin litattafan, suna samun karfin gwiwar zurfafawa wajen karanta litattafan da 'yan Afirka suka rubuta."

Na ji dadin zantawa da wata mai karatu Susan Mukosha Ngombe, wadda ita kawai ta fi son karanta litattafan da 'yan Nijeriya suka rubuta. Susan da ta dimautu da salo da jigon marubutan Nijeriya, ta ce suna ba ta damar fahimtar kasar da bambance-bambance da take da su.

Tafiyarta ga karanta adabin Afirka ta fara ne da littafin "The Secret Lives of Baba Segi's Wives" da Lola Shoneyin ya rubuta, littafin da ke bayani kan auran mata da yawa, matsin lambar al'adu da karfin iko tsakanin iyali a al'ummar Nijeriya.

Mutuntaka

Wani littafi kuma da take kauna shi ne "I Do Not Come To You By Chance" da Adaobi Tricia Nwaubani ta rubuta, kuma ta bayyana cewa "wannan littafin na dadin karantawa sosai, kuma yana yin karin haske kan masu zamba da cuwa-cuwa."

Littafin na bayani kan wani da ake kira Kingsley Ibe, wanda ya kammala digiri a jami'a da yake gwagwarmayar neman aiki a Nijeriya inda ya koma koyon yadda ake zamba da damfarar mutane ta hanyar aika sakon imel daga wajen kawunsa "Cash Daddy".

Ta hanyar bayanin da Susan ta yi, ta bayyana cewa litattafai sun zama madubin rayuwar dan'adam.

Idan mutum ya ga yadda aka yi bayanin al'adu da salon rayuwarsa a wani littafi, to yana jin gasgatawa da alakantuwa da rubutun, hakan kuma na kara bunkasa yawaitar al'adu da gwagwarmayar da aka fuskanta iri guda.

Litattafai na bayar da sabo da karsashin alakantuwa. /Hoto: Tokozile Ngwenya

A karshe, yawaitar litattafai da 'yan Afirka ke rubuta wa, ya fi karfin a yi musu kallo ta fuskar adabi kawai - suna wakiltar bukatar bai-daya ta tabbatuwar asali, amintuwa, da murnar wanzuwa muryoyi bambanbanta a nahiyar da wajen ta.

A matsayin masu karatu, muna samun farin ciki, ilimi da sake tabbatar da matsayinmu na 'yan'adam a cikin shafukan adabin Afirka.

Tokozie Ngwenya marubuciya ce da ke da sha'awar kirkirar litattafan yara kanana da ke bayar da labaran yanayi da dabbobin Afirka.

Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya zama daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afirka.

TRT Afrika