Wakilan ƙabilu tara na yankin sun gudanar da wasannin al'adu a wajen bikin.

Daga Charles Mgbolu

Rawa da waka inda mata ke sanye da rigunan raffia na gargajiya maza kuma na kade-kade da kayan kidan gargajiya na kpaningbo, na daga cikin abubuwan jan hankali yayin da ake bikin ranar al'adu da haɗin kai a Yammacin Equatoria na Sudan ta Kudu.

An gudanar da taron, wanda Hukumar Wanzar da Zaman Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu (UNMISS) ta tallafawa, a ranar Talata 21 ga watan Nuwamba a babban birnin Yambio na yankin, domin baje kolin kayayyakin tarihi da suka hada da wake-wake da raye-raye da kade-kade da dama.

Masu shirya taron sun ce babban burinsu shi ne a haɗa kan al’ummomin ƙabilu daban-daban na yankin. Yana ɗaya daga cikin irin wannan al'adu a ƙasar don taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya.

Ma'aikatar Al'adu da Matasa da Wasanni ta Sudan ta Kudu, wadda ta shirya bikin, ta ce wakilan ƙabilu tara na yankin sun gudanar da wasannin al'adu.

Sudan ta Kudu dai ta sha fama da rikice-rikicen ƙabilanci da ya kai ga mutuwa da ɓarna tsawon shekaru

Mahalarta taron sun ce wata dama ce ta nuna cewa za a iya amincewa da al'adu don tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a cikin al'umma mai mabambantan al'adu.

Sudan ta Kudu dai ta sha fama da rikice-rikicen ƙabilanci da ya kai ga mutuwa da ɓarna tsawon shekaru.

“Duk lokacin da rikici ya ɓarke, mu ne muke shan wahala a matsayin uwaye da ƴaƴansu. Muna buƙatar zaman lafiya. Mu zauna lafiya da kanmu kullum. Muna son ’ya’yanmu su girma a yanayi mai kyau domin su samu ilimi kuma su maye gurbinmu a matsayin shugabannin gobe,” in ji Hellen Mading, daya daga cikin ’yan rawa a wurin taron.

James Amabele, mazaunin Yambio, ya yarda da batun. "Irin wadannan abubuwan za su kawo zaman lafiya tsakanin al'ummomi da kuma [a] Sudan ta Kudu baki daya.

Wannan shi ne abin da muka yi marmarinsa—dole ne mu kasance da haɗin kai, kuma idan komai ya daidaita, to zaman lafiya zai wanzu,’’ in ji shi.

An yi amfani da kayan kiɗa daban-daban a wajen bikin.

‘’Wannan aikin shi ne ya nuna bambance-bambancenmu, da salo-salonmu, da bambancinmu ta fuskar al’adu, kuma manufar ita ce yin farin ciki.

"Kuma ta hanyar wannan farin ciki, za mu iya inganta haɗin kan zamantakewa; za mu iya ƙara sanin juna, za mu iya ƙara fahimtar juna, mu manta da ƙalubalen da aka fuskanta a baya,” a cewar Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar UMISS, Emmanuel Dukundane.

Usur da sarewa da wasu abubuwan na daga cikin kayayyakin da aka yi amfani da su don kaɗe-kaɗen da haɓakar raye-raye waɗanda suka haɗa masu rawa a matsayi ɗaya.

TRT Afrika