Daga Pauline Odhiambo
Marubucin waka da wasan kwaikwayo Oscar Wilde ya ce ya kamata mutum ya zama mai ƙirƙirar kayan zane na hannu ko ya zama mai sanya su a jikinsa.
Amma a wajen mai fasahar tsara zane-zane 'yan kasar Kenya Shiko Onyango, ka zama mai yin zanen ado kuma mai saka shi a jikinka na da kayatarwa matuka gaya.
Mai zanen 'yar shekara 34 ta samar da kayan ado da yawa da ake iya saka su a jiki ga mawakiyar zamani ta Nijeriya Yemi Alade, dan gambara na kasar Kenya Muthoni he Drummer Queen da mawakiyar da ta lashe kambin Grammin Angelique Kidjo, da dai sauran mashahurai.
Karsashinta na cakuda fasahar gargajiya da ta zamani na bayyana irin salon kabilarta, tunanin da ta fara yi tun tana makarantar sakandire.
"Na fara samar da dan kunne da sarka da awarwaro tun 2006 a lokacinda na koyi sana'ar hada wuri a samar da kayan ado a tsakanin al'ummar Maasai," ta fada wa TRT Afirka.
"Bayan kammala makarantar sakandire, ban samu aikin yi da ya dace da abin da na ke sha'awa ba, sai na kirkiri aikin da nake so da kaina."
Kalaman mai sana'a
Kayan zane da ka iya hawa jiki na nufin zane a jikin tufafi ko dan kunne da sarka da awarwaro, kuma ana samar da su da hannu kuma da yawa a lokaci guda.
Wani shafi mai sunan 'Anotolian Craft' ya bayyana cewa kayan da aka samar da hannu da ake saka wa a jiki na bayyana irin kaifin basirar mai samar da su.
"Dukkan kayan da na ke samarwa na haduwa da yadda na ke son su zama a zuciyata a lokacinda na ke samar da su. Misali, adon da ke 'kan Muthoni' wani ado ne da ke taya murna ga babbar mace mai karfi kuma na bai wa abun sunan mace ta farko a Kenya mai mukamin 'field marshal'," in ji Shiko.
"Kayan adon wata sanyayyiyar hanya ce da ke bai wa mutane damar koyon tarihi da al'ada matukar dai sun shafi tufafi."
Adon kan Muthon da aka samar da bangorin wuri, wata alama ce ta kabilar Kikuyu da ke Kenya kuma ana sayen sa sosai.
Ya zuwa 2013, Shiko ta samar da ayyukan yi ga matan da ke zama a gida kamar ta, tana horar da su wajen hada tsakiya da sauran kayan fasaha domin samun damar biyana bukatar kayan ado na sanya wa a jiki.
Ta bude shaguda da bayar da hiri a lokuta da dama don samar da kayayyaki masu kayatarwa.
"A matsayin mai fasaha, a lokacin da ka tsara wani abu na adon jiki, yana da wahala ka iya sake samar da shi kamar yadda na farko yake," in ji mahaifiyar yara biyu.
Ta kara da cewa "Saboda haka ake horar da mata da suke zaune a gida kuma suke sha'awar irin wannan sana'a ta kayan sawa da al'ada, ta yadda su ma za su zama masu samun kudade da habaka al'adu."
Al'adar sanya suna
"Wani abu kuma da shi ma ake yawan saya shi ne Akinyi, wanda ake samarwa da kashi."
Akinyi suna ne da aka samo daga kabilar Luo da ke Kenya kuma an tsara wannan kayan adon saboda sunan wata mata da Shiko ke tunanin "uwa ce mai kyau kuma mai karfi da ke kula da yaranta ba tare da yadda al'ada ke kallon ta ba."
Shiko da ta fito daga kabilar Kikuyu da Kamba, kuma ta auri dan kabilar Luo, ta ce sunayen gargajiya da take saka wa kayayyakinta na ado na da manufar habaka zaman lafiya a al'adun Kenya.
"A Kenya, akwai wata almara d aake bayarwa tun zamanin baya cewar kabilun Kikuyu da Luo ba sa jituwa da juna. Shi ya sa nake bai wa kayayyakina sunayen wasu kabilun na daban a Kenya a matsayin hanyar habaka hadin kai da watsi da al'adar nan ta kabilanci."
A wannan yanayi, abun ado na Kasiva ya samu sunansa daga mashahuriyar jarumar Kenya, Kasiva Mutua da ta rayu a yankin gabashin kasar.
Kayan adon jiki na Nekesa ya samu sunansa don girmama matakn Kenya 'yan kabilar Luhya.
"Daga Afirka zuwa Duniya baki daya"
Taken Shiko shi ne "Daga Afirka zuw aga Duniya", na bayyana jajircewarta wajen yada kyawu da al'adun Afirka ga sassan duniya - nasarar da ta samu a da yawan masu sayen kayayyakinta kawai ba, har ma da ta hanyar yadda take gudanar da kasuwancin nata.
"Watakila ta hanyar mulkin mallaka aka kawo wuri zuwa Afirka, amma kafin wannan lokacin ma akwai na katako irin na Afirka da ake yi, sannan akwai na kasusuwa da kwalayen kayan marmari da 'yan Afirka ke amfani da su wajen samar da abubuwa." in ji mai sana'ar da ta koyawa kanta da kanta.
"Har yanzu muna amfani da kasusuwa da aka debo daga bola. Ana tsaftace kasusuwan da gyara su do samar da wuri da wasu kayan sawa," in ji Shiko.
"Wannan ne dukkan abun da ke dorar da aikin. Ana fara wa tun daga tattara ƙasusuwa daga bola, a karshe sai mutane su saka a jikinsu bayan an samar da kayan adon."
Kazlaika, baya ga samar da kayan ado daga wuri, kasusuwa da wuri, yayin da ake yi a tsakanin kabilu ma na sanya a samar da wasu abubuwan na daban daga kayayyakin da aka tsnto aka tsaftace.
Sana'a mai dorewa
Muna sabundata dalmar da aka samu a jikin tsaffin kwadunan rufe kofa ta hanyar narka su mu sauya su zuwa kayayyaki masu kyau," in ji ta. "Muna kuma hada dan kunne, sarka da suaran kayan daura wa daga tsaffin alminiyom."
Ta fada wa TRT Afirka cewa "Muna sayen mafi yawan karafan daga karafan da suka lalace a Kenya a matsayin hanyar karfafa gwiwar masu aiki a wannan fannin,."
"Bangaren kayan gwanjo ma na da girma a Kenya, shi ya sa muke sanya matasa su sabunta wanduna da sauran kayayyaki ta ahnyar amfani da sinadarin graffiti."
Wannan aiki, na da taken "Daga Bola zuwa Amfani" na yin maganin rashin aikin yi a tsakanin matasa.
An nuna kayan ado na sanya wa a jiki da Shinko ta samar a wajen Bikin Kasa da Kasa na Tufafi da Kayan Sawa a Zanzibar da ma wasu wuraren da dama.
A yanzu tana aikin hadin gwiwa da wani babban kamfanin kayan sawa a jiki a Afirka ta Kudu kuma ta tsara wasu abubuwa ga kamfanin 'TruFace by Grace' - wani kamfani mallakin wata bakar fata da ke habaka yadda ake adana dabarun sana'ar hannu.
Shawarar da take bayarwa game da masu zanen d ake tasowa ita ce "Babu wata ka'ida ta sarrafa kayan sawa, kawai ka kalli me za ka iya ta hanyar amfani da basirarka a karon farko, sai ka ga kabilarka ta biyo ka a baya. Kawai ka yi daidai da basirarka. Hakan zai amfanar da kai."