Rubutun ayoyin farko na sūrat al-Nūr na Al-Kur'ani da aka yi da salon Kufic a arewacin Afirka a karni na 14. Hoto: Esra Yagmur      

By Esra Yagmur

Kimanin shekaru 100 da suka wuce, wani Baturen Ingila masanin adabin kasashen gabashin duniya Thomas Arnold ya kai ziyara kasar Masar kuma zanen zayyanar haruffan Larabci ya dauki hankalinsa.

Ya ga yadda aka yi ado da rubutun a komai da komai ciki har da masallatai da hubbare da gidaje da sauransu, daga nan ne bayan ganin haka sai Arnold cikin mamaki ya ce "Babu wani aikin zayyana da aka martaba da bunkasa kamar aikin zayyanar rubutu."

An bayyana zanen zayyanar Larabci a matsayin wata babbar nasara a fannin zayyanar Musulunci, kuma za ka ga tasirinsa a kan duwatsu da jikin katako da jikin karfe da jikin gilas da sauransu.

Har zuwa yanzu, abin da Arnold ya bayyana dangane da zanen zayyanar Larabci ya ci gaba da kasancewa gaskiya, inda ya ci gaba da rike tasirinsa da karbuwarsa har zuwa yau.

Aikin yin kyakkyawan rubutu, ko ḥusn al-khaṭṭ, a harshen Larabci yana nufin "kyakkyawan rubutu" kuma daidai yake da rubutun Girkawa na “kalligraphia”, ya bayyana a Musulunci daruruwan shekaru kafin masanan nahiyar Turai kamar Jacob Georg Christian Adler.

Adler shi ne mutum na farko da ya yi nazari kan zayyanar rubutun Larabci, ya ci karo da shi a karni na 18 kuma ya sanar da duniya gaba daya wannan salon rubutun

A addinin Musulunci, salon zayyanar haruffan Larabci da na matsayi sosai a addinin fiye da yadda sauran addinai suke daukar nasu.

Sana'a ce da ake darajata

“Tsarkin rubutu, tsarkin ruhi ne," a cewar wata tsohuwar karin maganar harshen Larabci kuma wannan karin maganar tana nuna muhimmancin zayyanar rubutun Larabci ga addinin Musulunci.

Salon da aka rubuta Al-Kur'ani an yi shi ne da salon zayyanar rubutu na kufic a tsakanin karni na 9 zuwa na 10. Hoto: Esra Yagmur

Addinin Musulunci ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba da bunkasar salon rubutun, in ji Esra Akin-Kivanc, wadda farfesa ce a Jami'ar South Florida.

"Sabanin addinin Kirista da sakon Ubangiji na tsohon alkawari ya aiko shi ne ga dan Adam a rubuce, shi Alkur'ani an saukar da shi ne ga Annabi Muhammad (SAW) ta hanyar wahayi.

Ko da yake Musulmi sun ga dacewar a rubuta Alkur'anin don kawar da kura-kurai da samar da daidaito wajen kira'a, kamar yadda addinin Musulunci ya tsara," in ji ta.

Kuma duka komai ya ta'allaka ne ga yadda sakon Ubangiji ya zo ga Musulunci.

Kur'anan farko da aka rubuta an yi su ne da salon rubutu na Kufic ta amfani da launin ruwan gwal. Hoto: Esra Yagmur

"Wahayin farko da aka saukar wa Annabi Muhammad (SAW) shi ne "Iqra" wanda yake nufin yi karatu.

Rubutu yana da muhimmanci a addinin saboda sakon farko da aka saukar wa Annabi," kamar yadda Bahia Shehab ta shaida wa kafar yada labarai ta TRT World, Bahia masaniyar tarihi ce kuma mai fafutika kuma farfesa a fannin zayyana a Jami'ar Amurka da ke birnin Cairo.

A shekarun farko, ana amfani da zayyanar rubutun ne wajen buga littafan addini, wani aiki da yake daraja da martaba a lokacin.

Ko da yake, bayan wani lokaci zayyanar rubutun ya rikide ya zama wani salon rubutu mai zaman kansa, inda ya bazu zuwa wasu sassan ilimi ba kawai ya takaita ba ne ga rubutun littafan addini ba.

"Shakka babu rubutun zayyanar haruffan Larabci yana da matukar amfani wajen rubutun littafan addini, da kuma sauran abubuwan da suka shafi addinin," in ji Akin-Kivanc na Jami'ar South Florida.

Zama mai zayyanar rubutu

“Tun lokacin Daular Umayyad (661 – 750) miladiya, ana amfani da rubutun zayyanar ne wajen ado abubuwa da ba su da alaka da addini a wasikun hukuma da jikin kudin sulalla da abubuwan tarihi, ayyukan zayyanar sun shafi harkokin yau da kullum din kowane Musulmi."

Kufic, wani salon rubutun haruffan Larabci wanda ya yi fice a duniyar Musulunci, kuma da shi ne aka yi amfani wajen rubuta Al-Kur'ani.

Salon rubutun Kufic yana da kyatarwa sosai da ban sha'awa. Al-Qalqashandi, wani masani na karni na 14 daga Masar ya ce "daya daga cikin salon rubutun Larabci shi ne a yanzu ake kira Kufic. Daga shi ne duka sauran suka samo asali."

Wani bangare na Al-Kur'ani da aka yi da salon rubutu na Kufic a tsakanin karni na 9 zuwa na 10 wanda ya kunshi wani bangare a sūrar al-Ahzāb. / Hoto: Esra Yagmur

Ana alakanta salon rubutun Kufic da Kufa, wani birni da ya faro daga kudancin tsohon yankin Babylon — wani wuri da ya yi suna saboda tarihinsa da al'adunsa.

Mai nisan akalla kilomita 170 daga babban birnin İranı, Baghdad, Kufa ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da ci gaba.

Sha kundum

Wannan shi ne labarin salon rubutun Kufic, wato wani salo na zayyanar rubutun addinin Musulunci, wanda ya dauki sunan birnin da ya samo asali a can.

Kamar yadda Shehab wadda ta bayyana zayyanar rubutu a matsayin "bayyana wani abu mai tsarki" da kuma "bayyanar da asali, salon rubutun Kufic ya tasirantu da wasu al'adu a tsawon daruruwan shekaru.

"Akwai wata babbar lema dangane da salon rubutun Kufic yake karkashinta. A Musulunci, idan da kalli duka daulolin da aka yi, salon rubutun da kowa yake kira Kufic, wanda karkashinsa akwai wasu kananan salo iri-iri kamar na gabashi da na yammaci da sauransu," in ji ta.

"Duka wadannan yankuna da Musulunci ya kai sun sauki rubutun kuma suka fassara shi inda suka mayar da shi nasu. Saboda haka wannan ya samar da salo daban-daban daga samuwar ci gaban yankunan."

Tsakanin karni 11 zuwa na 12 an rubuta Al-Kur'ani da salon rubutun Kufic na Gabashi wanda na mutane kasar İran ne kadai wanda yake da alaka da Daular Seljuqs ko kuma Daular Ghaznavid na Iran.

Hoto: Esra Yagmur Masu rubuta Al-Kur'ani da hannu sun fi son salon rubutun Kufic saboda yadda yake da ban sha'awa.

“A tarihin masu zayyana sun zabi salo mai kyau don su rubuta Al-Kur'ani, salo ne mai ban sha'awa da kayatarwa wajen rubuta Al-Kur'ani.

Abin da ya sa suka zabi su yi haka shi ne saboda su yi rubuta sakon Ubangiji ta hanya mafi kyau. Kamar yadda masana na farko suke gani, akwai alaka ta kai-tsaye tsakanin salo da siffar haruffa da tsarki," in ji Shehab.

Masu tsara haruffan

Ko da yake, yayin bunkasar zayyanar rubutun haruffan Larabci, ana amfani da salon rubutun Kufic fiye da kawai a littafan addinin Musulunci.

Ana amfani da shi yanzu a fannoni da dama ciki har da wash sabbin hanyoyi — tun daga yi wa abubuwa ado da tufafi da adon masallaci da jikin kudin sulalla da jikin bangon manyan gidajen da sauransu.

"An fara salon rubutun Kufic ne daga rubutu sakon Ubangiji," in ji Shehab kuma ta ci gaba da cewa "amma kuma sai ya samu karbuwa daga sarakuna.

An rika amfani da shi wajen adon masallatai da wurare da gidaje da kuma makarantu."

"Saboda zubin haruffansa, salon rubutun Kufic ya yi kama da zayyanar zanen gine-gine kuma masu tsara shi na farko da yin rubutunsa ainihinsu masu zayyanar zanen gine-ginen haruffa ne wadanda suka fito da martabar da sarakuna da kuma muhimmancinsa a addini."

Wani bangare na Al-Kur'ani da aka rubuta da hannu a Arewacin Afirka da salon rubutun Kufic a karni 14, yana da wani salo mai kayatarwa a gefen shafin. Hoto: Esra Yagmur

Farin jinin salon rubutun Kufic wanda ya kwashe tsawon daruruwan shekara da shi, ya fara samun raguwa wajen farin jininsa ne a karni na 12, yayin da daulolin Musulunci suka ci gaba da fadada, an maye gurbinsa da wani sabon salo na cursive, sai dai ba rasa farin jininsa ba gaba daya.

Yana da kayatarwa sosai

Akin-Kivanc ta bayyana cewa kamar sauran ayyukan zayyana, aikin zayyanar rubutu ya samu sauye-sauye saboda yadda bukatar masu zayyanar ta canja da kuma bukatar masu son aikin, salon cursive ya maye gurbin angular sannu a hankali, wannan ne tsarin rubutun zayyana na farko na Musulunci, yayin da ake kwafan rubutun Al-Kur'ani da aka rubuta da hannu.

Kamar yadda Akin-Kivanc ta bayyana, masu zanen zayyana sun koma amfani da salon rubutun cursive wanda ya fi sauki karatu da kuma saukin rubutu, saboda ilimin addini ya kai ga dimbin mutane kuma su iya karanta Al-Kur'ani cikin sauki.

"An fi mayar da hankali kan saukin karatu ne a littafan addini, kodayake, yawancin ayyukan zayyanar da muke gani a masallaci da wurare da fadodi da kuma makarantu, an yi wa rubutun ado sosai ta yadda ko masana a wani lokacin ba sa iya fahimtar abin da aka rubuta cikin sauri," in ji ta.

"Idan aka yi amfani da salon angular da salon cursive a tare musamman idan aka yi musu ado sosai, to hakan yana kasancewa wata gasar zayyanar rubutu maimakon isar da ilimi ko sako, a wasu lokuta suna nuna kwarewar mai zanen zayyanar ne da basirar hannunsa."

An yi amfani da bulo da tayar wajen fitar da salon rubutun Kufic a masallacin Bibi-Khanym da ke birnin Samarkand a kasar Uzbekistan. / Hoto: GettyImages.

Bunkasar Italiya

A karni na 14, yayin da aka samu bunkasa a nahiyar Turai, Giotto di Bondone, shahararren mai fenti da zane-zanen gine-gine dan Italiya, ya samu kyautuka da dama saboda wani zane da ya yi wanda ke nuna “Madonna and Child” (wato Madonna da Yaro) wanda aka saka a gaban wata coci a birnin Florence.

Don bunkasa al'adar kula da gumaka da aikace-aikacen fenti da zane-zane, Giotto ya rubuta rubutu a manyan ayyukan da ya yi — wani abu da aka saba gani a wancan lokaci.

Da wuya ka iya karanta rubutun cikin sauki wanda aka yi a daya daga cikin harsunan nahiyar Turai.

Ko da yake rubutun da Giotto ya yi ya kayatar sosai, amma daga farko idan ka kulla ya yi kama da rubutun zayyanar haruffan Larabci.

Salon zanen pseudo-Kufic da launin zinare mayafin Virgin Mary wanda yake nuna tasirin salon rubutun zayyana na Musulunci a nahiyar Turai a shekarun baya. / Hoto: nga.gov

Watakila wani yayi mamakin yadda salon rubutun pseudo-Kufic ya shiga jerin dadadden salon fenti da zayyansr gine-gine, ganin cewa gabanin karni na 16 nahiyar Turai ba ta san harshen Larabci.

Akin-Kivanc tana da wasu hanyoyi biyu ta yada salon rubutun zayyana na pseudo-Arabic da sauran salo kamar mirror script wanda ake kira 'muthanna' "wanda da ya masu zayyanar rubutu Musulmi da suke neman aiki a nahiyar Turai da kayan kawa da ake kai wa kasuwanni a Turai, da ya yi suna."

"Yaduwar kananan kayayyaki suka sa aka san da Turawa masu aikin zayyana kanana kuma suka fara son rubutun zayyana na Musulunci," in ji Akin-Kivanc.

Hasumiya mai kayatarwa

A kotunan sarakuna da baya can, shugabanni da mutane masu rike da manyan mukamai suna sanya kaya masu tsawo da aka yi wa ado wanda ake kira "tiraz".

An samo kalmar ne daga harshen Farisa wanda yake nufin "ado" ko "kawa", wadannan kayan suna da muhimmanci sosai.

Yayin da aka ci gaba da samun kasuwanci da huldar diflomasiyya, mayakan Kiristoci yayin wani atisayen soji sun gano muhimmancin kayan kuma sun sauke sun tafi da su gida a matsayin ganima.

Daga bisani, bukatar wadannan kaya ya karu sosai tsakanin karni na 14 zuwa 15 a Turai, abin da ya jawo aka yi jigilar kayan tiraz zuwa biranen Italiya, wanda hakan ya taba tunanin Turawa.

Hoton Sarki Sicily Roger II sanye da rigar alfarma wadda aka yi wa zayyanar rubutun Kufic na Larabci, za ka iya karanta rubutun daga kasa. / Hoto: islamicart.museumwnf.org

Shehab ta bayar da labarin wani abu da ya same ta a birnin Bellagio, inda ta nuna yadda kyan aikin zayyana ya ja hankalin Kiristocin Yamma.

“Kasancewa ta a Bellagio a Arewacin Italiya na ji dadin ganin yadda na samu birnin. Yayin da nake tafiya a kewayen birnin, a zuciyata ina ta tunanin duniyar Musulunci, abin da ya same ta, ko da yake na san amsar abin da nake tambayar kaina, lokacin da na ga tsohon hubbaren karni na 16 zuwa 17 a bayan wani tafki."

“Yayin da na ga yadda aka zayyana wani gida wanda ya ja hankalina, na ga wata hasumiya wacce ta burge ni. An yi rubutu a jikinta, inda aka rubuta "“wala ghaliba illa Allah” wato “babu wani mai nasara bayan Ubangiji."

Bar batun al'ada

Duk da cewa Turawa ba sa fahimtar rubutun Larabci, amma shakka babu yanayin salon rubutun yana daukar hankalinsu.

Salon rubutun zayyana na Pseudo-Kufic yana zuwa ne a salo iri-iri kamar floral arrangements da geometric patterns kuma a wasu lokuta ana hade su ne a tufafi kamar a tufafin alfarma na manyan limaman addini kamar fafaroma da kadinal-kadinal," in ji Shehab.

Salon zanen zayyana na Musulunci wanda ya kawo ci gaba sosai da al'adu, yana da tarihi daban-daban fiye da yadda ake tunani.

Wannan yana tabbatar da cewa zane-zanen sun kunshi al'adu daban-daban, in ji Akin-Kivanc: "Idan kana son ka fahimci ainihin tarihi da da al'adar rubutun zayyana na Musulunci to wajibi mu kalli abin fiye da gaban tarihin zane-zane, mu kuma duba batun zamantakewa da addini da kuma siyasa na al'ummo daban-daban."

TRT Afrika