Watan Ramadana, wata ne mai tsarki wanda ake son taimaka wa marasa galihu, sai dai a tsakanin masoya a arewacin Nijeriya, wata ne da wasu matan ke sa ran za su samu alkhairai daga masoyansu.
Suna sa ran masoyinsu zai cika musu kwando da kayan marmari domin amfani da su wurin buɗe baki a watan azumin.
Ana yin wannan kyautatawar ne da nufin ƙara danƙon soyayya tsakanin masoyan biyu, haka kuma yin hakan zai iya zama wata alama ga yadda mijin zai iya zama mai nuna kula da matar idan ya aure ta.
"Idan muna tare a tsawon shekara, ya kamata ka ba ni Ramadan Basket, (me ya sa) ba za ka ba ni ba?" kamar yadda budurwa Fatima Baba Dahiru daga arewacin Nijeriya ta shaida wa TRT Afrika.
Matsalolin tattalin arziƙi
"A gaskiya Ramadan Basket dole ne a tsakanin masoya," kamar yadda ta ƙara da cewa.
Sai dai a yayin da Nijeriya ke fama da matsalar tattalin arziƙi mafi muni inda farashin abinci ya ninka sau da yawa, mutane da dama na ganin ya fi kyau su taimaka wa iyayensu a maimakon masoyansu.
Fatima na ganin duka abubuwan biyu sun dace kafin da kuma bayan aure.
"Ba wanda ya ce kada ka yi wani abu ga iyayenka. Iyaye sun bambanta. Akwai ma buƙatar ka tura taimakon iyayenka a kowane lokaci," in ji ta.
"Sai dai ita ma budurwa tana da matsayinta. Bai kamata a ƙyale ta idan ana batun Ramadan Basket ba," kamar yadda Fatima ta ƙara da cewa.
Ga Fatima, ba wai jin daɗi kaɗai Ramadan Basket yake kawo ba, yana ƙara soyayyar masoyin nata a cikin zuciyarta.
"Idan na samu Ramadan Basket, nakan ji dadi sosai domin ana jin dadi sosai a duk inda kuma a duk lokacin da aka ba da shi. Idan aka bayar da Ramadan Basket, abin farin ciki ne. Ina jin dadi yayin bude shi. Ramadan Basket yana kara soyayya," in ji ta/
'Jin ba daɗi'
A ɗayan ɓangaren kuma, idan ba ta samu kyautar ba, tana jin ba daɗi, in ji ta.
"Idan ba a bani ba, ina jin ba daɗi. Ya kamata a ba ni," kamar yadda ta yi ƙarin bayani.
Ita ma Sauda wata budurwa ce daga arewacin Nijeriya, sai dai ta ce ita ba za ta ji haushi ba idan ba ta samu Ramadan Basket ba.
"Zan yi farin ciki idan aka ba ni, amma idan ba a ba ni ba, ba zan baƙin ciki ba saboda tun farko ban yi tsammani ba," kamar yadda Sauda ta shaida wa TRT Afrika.
“Ba ni da hanyar tilasta wa wani ya ba ni Ramadan Basket. Kuma iyaye sun fi Ramadan Basket daraja. Ya kamata kyautarsu ta kasance ta daban kuma ya kamata ta kasance daidai da irin arziƙin da Allah Ya yi wa mutu," in ji ta.
Hamza Umar Saleh wanda saurayi ne ya ce tun kafin watan Ramadana ya shirya kai wa matar da zai aura Ramadan Basket.
"Idan na bayar da Ramadan Basket, a gaskiya ina jin daɗi sosai saboda yin abu mai kyau ga wanda kake so kuma yake sonka yana sa ka ji daɗi sosai," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Sai dai Hamza ya bayyana cewa bai kamata a rinƙa kallon lamarin tamkar wani tilas ba inda ya ce ya kamata "a rinƙa yi ne kawai idan da hali".