Aikin Hajji na daya daga cikin rukunnan Musulunci biyar / Hoto: AA

Musulmai miliyan 1.8 ne suka yi tururuwa zuwa Dutsen Arafat a ranar Talata domin gudanar da muhimmin rukunin Aikin Hajjin.

Aikin Hajjin 2023 na daga cikin mafi girma bayan annobar korona.

Mahajjatan suna karanta ayoyin Alkur’ani a yayin da suke saman dutsen, wanda a nan ne Annabi Muhammad (S.A.W.) ya yi hudubarsa ta karshe.

Miliyoyin Musulmai ne ke taruwa a Dutsen Arafat. Hoto/AA

Hawan Arafat wajibi ne ga mahajjaci. Yana daga cikin ibadun da ake yi wadanda ke gajiyar da jiki, saboda mahajjata na shafe sa’o’i da dama suna addu’o’i da karatun Alkur’ani a kan Dutsen na Arafat kuma mafi yawancin lokaci wurin na da tsananin zafi.

Wasu Musulmai suna gudanar da Aikin Hajji tare da iyalansu. Hoto/AA

Zafin da ake yi ya kai maki 46 a ma’aunin selshiyos a ranar Litinin, inda mahajjata suka rinka amfani da lema a yayin da suke tafiya daga Makkah zuwa Mina, inda suka kwana a karkashin tenti kafin suka kama hanya zuwa filin Arafat da safiyar Talata.

Da yamma, mahajjatan za su yi tafiya zuwa Muzdalifah, wuri ne da ke tsakanin Arafat zuwa Mina inda za su kwana bude ba a cikin tenti ba.

Bayan hawan na Arafat, mahajjatan za su tsinci duwatsu wadanda za su yi amfani da su wurin jifan shedan a Mina.

A lokacin Hajji, ana so Musulmai su kara kaimi wurin bautar Allah. Hoto/AA

Aikin Hajji ibada ce mai karfi ga Musulmai wadda take kankare musu zunubansu, tare da jawo su kusa da ubangijinsu da kuma hada kan Musulman duniya.

Wasu suna shafe shekaru suna tara kudi domin jiran lokaci don su gudanar da Aikin Hajji. Aikin Hajji na daga cikin taron addini mafi girma.

Yana hada kan Musulmai - manya da kanana, mai kudi da talaka - daga fadin duniya.

Ana gudanar da Aikin Hajji a duk shekara. Hoto/AA

A bana, an dage duka takunkuman da aka saka na annobar korona da suka hada da bayar da tazara da saka takunkumi.

Haka kuma an cire sharadin da aka saka cewa idan mutum ya wuce shekara 65 ba zai iya yin aikin ba, lamarin da ya bai wa dubban tsofaffi damar halartar Aikin Hajjin.

Alhazai suna tafiya zuwa Dutsen Arafat da zarar Asuba ta yi. Hoto/AA

Bayan hawan Arafat da jifar shaidan, wuri na karshe da ake kammalawa shi ne Babban Masallacin Makkah, wanda a nan Musulmai ke yin dawafin karshe a Ka’aba.

Aikin Hajji wajibi ne da Musulmai da ke da iko da kuma lafiya akalla sau daya a rayuwarsu

A lokacin Aikin Hajjin, ana bukatar duka maza su saka farin hirami wanda bai da dinki, wata alama ce da ke nuna mai kudi da talaka duk daya suke a gaban ubangiji.

Haka kuma mata ba za su saka kayan kwalliya ba inda ake son su saka kayan da za su rufe jikinsu.

Daya daga cikin abubuwan da ake koya daga Aikin Hajji shi ne tawali'u. Hot/AA

Hukumomin Saudiyya sun bayar da jirage masu saukar ungulu wadanda suke shawagi baya ga dubban ma’aikatan lafiya da kuma motocin daukar marasa lafiya domin kula da marasa lafiya.

Sakamakon yadda yanayi zafi yake, maniyyata da dama suna amfani da lema domin tare rana tare da saka hula mai malfa.

Mahajjata na shafe yini guda a Dutsen Arafatkafin su wuce Muzdalifah. Hoto/AA

A karshen Aikin Hajjin, ana gudanar da bikin babbar sallah inda Musulmai a fadin duniya duk suke yi.

Ga wadanda suke da dama, ana sa ran su yanka dabba kamar rago ko shanu ko rakumi a domin rarraba wani kaso na naman ga marasa galihu.

TRT Afrika