Musulmai sun gudanar da Sallar Tarawih a dare na farko na watan Ramadana a harabar Masallacin Ƙudus a Gabashin Birnin Ƙudus, inda wasu daga cikin Falasɗinawan suka yi sallolinsu a kan titunan tsohon birnin.
Hotunan sun nuna adadi ƙalilan na masu ibada a harabar suna sallah duk da takunkumin da ƴan sandan Isra'ila suka saka inda tun farko suka sanar da tura ƙarin jami'an tsaro zuwa harabar masallacin.
Tura jami'an tsaron na zuwa ne a daidai lokacin da dubban Falasɗinawa ke shirin gudanar da Sallar Tarawih, wadda sallah ce ta musamman da Musulmai ke gudanarwa a watan Ramadana.
Tashar Isra'ila ta Channel 12 ta ruwaito cewa tura ƴan sandan na zuwa ne a daidai lokacin da ake nuna damuwa kan matsalar tsaro a Gabashin Birnin Ƙudus da Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye.
Kafar watsa labarai ta Channel 12 ta Isra'ilar ta kuma ruwaito cewa an tura saƙonni a wayoyin mazauna Birnin Ƙudus inda ake gargaɗinsu kan tayar da duk wata tarzoma.
Masallacin Ƙudus shi ne na uku mafi tsarki ga Musulmai baya ga Masallacin Makkah da na Madinah.
Yahudawa na kiran Al Aqsa da "Temple Mount" inda suke cewa Masallacin na daga cikin wuraren bautarsu na tun asali.
Isra'ila ta mamaye Gabashin Birnin Ƙudus wanda a nan Masallacin Ƙudus yake a 1967 a lokacin yaƙin Larabawa da Isra'ila.
Isra'ilar ta mamaye baki ɗaya birnin a 1980, wanda yunƙuri ne da ƙasashen duniya da dama ba su amince da shi ba.
An ta zaman fargaba a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan tun bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da wani mummunan harin soji kan Gaza bayan dakarun Hamas sun ƙaddamar da hari kan Gaza a watan Oktoban da ya gabata.
A Gaza, duk da irin ɓarnar da Isra'ila ta yi musu sakamakon hare-haren da take kai musu, amma duk da haka sun fita Sallar Tarawih a dare na farko na watan Ramadana.