Azumin watan Ramadana na bana ya fara ne a ranar Laraba da dare, 22 ga watan Maris aka kuma tashi da shi a ranar Alhamis.
Miliyoyin Musulmai ne a fadin duniya ke azumin wata Ramadana a duk shekara.
Ramadan wajibi ne ga Musulmai wanda hakan ke nufin babu abinci ko ruwa da rana a watan baki daya.
Haka kuma baya ga yin azumi a watan Ramadana, wata ne na tsarkake kai da kuma sauran ibadu kamar yawaita karatun Al-Kur’ani da Sallar Tarawihi da kuma sallolin dare na goman karshe.
Sai dai ka taba tambayar kanka Musulman da ke zuwa sararin samaniya ‘yan sama jannati idan azumi ya riske su yaya za su yi?
A tarihi, an taba samun akalla mutum guda wanda ya yi azumi a sararin samaniya kuma Malaman Musulunci sun yi tambihi kan lamarin.
A watan Ramadan shekarar 1985, Yariman Saudiyya Sultan ibn Salman ya taba shiga jirgin da ke zuwa sararin samaniya da ke bincike.
Yariman yana sararin samaniya jaririn watan Ramadana ya fito a lokacin, kuma bisa ga fatawar da malamai suka bayar a lokacin, sai suka ce mutum za yi azumi ne daidai da wuri na karshe da ya baro na duniya.
A wajen wannan yariman, wuri na karshe da ya bar duniya zuwa sararin samaniya shi ne Jihar Florida ta Amurka.
Sa’annan akwai Sultan Alneyadi daga Hadaddiyar Daular Larabawa wanda ya tafi sararin samaniya a watan Fabrairun 2023 da zummar yin wata shida a can.
Hakan na nufin azumin bana zai same shi a can kenan.
Kafin tafiyarsa zuwa sararin samaniya, ya yi hira da ‘yan jarida inda ya bayyana cewa a matsayinsa na dan sama jannati, shi matafiyi ne, kuma hakan ya zamar masa wata hujja ta kin yin azumi domin azumi ba dole ba ne ga matafiyi.
Idan mutum na wurin da rana ba ta faduwa fa?
A ‘yan shekarun nan, ana kara samun daukakar Musulunci a kasashen da ke yankin Arctic.
A irin wadannan kasashe, ana samun lokacin da rana ba ta faduwa a lokacin bazara ko kuma ranar ta fadi ta yi sauri ta fito wanda lokacin da mutum zai iya yin buda baki da sahur ba tazara.
A irin wadannan lokuta, akasarin Malaman Musulunci na da fatawar Musulman da ke yankin su yi amfani da lokutan sahur da buda baki na kasashe mafi kusa da su, wadanda su nasu tsarin lokacin da dan sauki.
Shin azumi na kara lafiya?
Takaitaciyyar amsa ita ce e. A kimiyyance an tabbatar da cewa azumi na taimakawa wurin daidaita sukarin da ke cikin jinin mutum da rage kitse da kuma taimakawa wurin rage kiba.
Azumin da ake yi na ranaku na kara karuwa tsakanin jama’a.
Azumi kawai ake yi da Ramadana?
Azumi wani rukuni ne na watan Ramadan duk da cewa shi ne ginshikin watan. Ana kara yawaita ibadu da bayar da sadaka da yin addu’o’i na musamman.
Ana gudanar da Sallar Tarawihi bayan Sallar Isha’i wadda sunnah ce.
Sai dai ya danganta da fatawar da mutum yake bi, wasu sukan yi tarawihi a masallaci wasu kuma a gida.
Ganin cewa ayyukan alkhairi a watan Ramadana na da lada mai dumbin yawa, Musulmai na kokarin yin su a lokacin.