Daga Pauline Odhiambo
Kafin ya fara sana'arsa ta zane-zane, Richard Mensah a yawancin lokaci kan yi zane a 'yar ƙaramar takarda lokacin cin abincin rana, a wata cibiyar sarrafa makamashin nukiliya a Birtaniya.
Lokacin da wani abokin aiki ya tura zane-zanen a yanar gizo a shekarar 2016, Mensah ya yi mamakin maganganu masu daɗi da kuma mayar da martani da suka cika shafinsa.
Allah ya yi masa baiwa a harkar zane zane, amma kafin wannan lokacin ba batun wannan baiwar ba ne a gabansa, yana gwammacewa don mayar da hankali kan sana'arsa a fannin sarrafa sinadarai don samar da abubuwa.
"Lokacin da nake tasowa a Ghana, bayar da labari ta hanyar zane-zane babban lamari ne, amma saboda wasu dalilai,a kullum ina kallon kaina a matsayin masanin kimiyya fiye da mai bayar da labari," mai zane-zanen abubuwa na zahirin ya shaida wa TRT Afrika.
"Yanzu sai na fahimci ina son bayar da labari fiye da yadda nake son zama mai ilimin kimiyya," Mensah ya faɗa, wanda cibiyar baje kolin zane-zane ta Mayfair ta saka sunansa a cikin masu zane-zane da ke tasowa guda 25 a Birtaniya.
Shagon gyaran gashi
Zane-zane na zahiri yana bayyana kowane irin zane da yake da nasaba sosai da duniyarmu ta zahiri, kuma musamman na surar jikin ɗan adam, a cewar dandalin The Artling.
A lokacin ƙuruciyarsa, Mensah a kodayaushe yana yin zane a jikin bangon wajen gyaran gashi da shagunan masu aski a unguwarsu don ya samu ƴan kuɗaɗe.
"Lokacin ina ɗan shekaru 5 ko 6 da haihuwa, ina yin zane a shagunan sayar da kaya kuma ana biya na da alawa da minti, kuma da na ɗan ƙara girma, abokanaina a makaranta suna sayen wasu daga cikin zane-zanena," in ji mai zane-zanen mazaunin London.
"Na yi tsimin ƴan kuɗaɗe a sayar da zane-zane da kuma yin zane a bangon wajen gyaran gashi," in ji shi.
"Akwai lokacin da na fara ɓoye wa iyayena kuɗaɗen da na samu saboda ba sa ganin zane-zane a matsayin wata tartibiyar sana'a."
Lokacin da ya koma Birtaniya da zama a shekarar 2002 don karatunsa na digiri na biyu a bangaren gurɓatar muhalli da kiyayewa, Mensah bai taɓa zaton zane-zane zai sake shiga rayuwarsa ba.
Dangantaka da ke ƙulla alaƙa
"Ya ɗauke ni kusan shekaru goma sha shida kafin na dawo zane-zane, amma na san bai taɓa bari na ba", Mensah ɗan shekaru 46 da haihuwar ya bayyana.
Daga cikin zane-zanensa akwai wani jeri mai suna 'Rungume da Juna’ wanda ya ƙunshi surar igiyoyi wajen isar da saƙonnin soyayya.
"Ba a magana kan soyayya tsakanin ma'aurata baƙar fata yadda ya kamata, saboda bautar da baƙaƙen fata da aka yi ya sa yana wuya su nuna wa junansu ƙauna," in ji Mensah, wanda galibi yakan tasirantu da litattafan tarihi.
Zamanin cinikin bayi, an ɗaure ƙafafun bayi da sarƙa ko a ɗaure musu wuya da igiya.
"Amma a Ghana, igiyoyi alama ne na karfi, kuma niyyata ita ce na nuna hakan a aikin zanena ta hanyar nuna yadda baƙaƙen fata har yanzu suke dunƙule waje guda cikin ƙaunar juna," mai zane-zanen ya bayyana.
"Shauƙin soyayya tsakaninmu ba za a iya kassara shi ba, sannan muna manne da junanmu kuma da ƙarfinmu fiye da kowane lokaci a baya."
Zanensa da ke nuna Yaa Asantewaa - wata mata ƴar Afrika wacce ta jagoranci wani gagarumin tawaye, domin kare masarautar Ashanti, Wanda yanzu wani bangare ne na Ghana a yau, an zaɓe shi domin nunawa a JD Malat Gallary.
An nuna ƙarin zanensa na mai a Japan, da Faransa da Afrika ta Kudu da kuma wasu ƙasashen.
‘Baƙar Fatar Birtaniya'
Amma shauƙin da Mensah yake da shi na bayar da labaran baƙaƙen fata galibi yana fitowa ne daga burushinsa tare da wariyar launin fata.
Zanensa mai take 'Taken' ya tasirantu ne daga wariyar da ya yi fama da ita musamman a farkon shekarunsa a matsayinsa na ɗalibi a Birtaniya.
"Ƴan sanda sun sha tsare ni amma zan iya tuna wani abu da ya faru lokacin da na tsaya yayin da nake barin tashar jirgin ƙasa bisa zargin ina dauke da miyagun kwayoyi," Mensah ya tunano.
"An danne kaina a jikin bango yayin da ake binciken kayayyakina. Sun min tambayoyi da yawa da suka jiɓanci shige da fice a maimakon miyagun kwayoyi.
Da ba a samu miyagun ƙwayoyi ba, Mensah ya ce, 'yan sandan sun kama gabansu ɗaya bayan ɗaya, babu ko ɗaya daga cikinsu da ya ya nemi gafara kan wulakancin.
Ya ƙara da cewa, "Na ji kamar an min ƙwace, shi ya sa alamar tutar Ingila ta yi nesa da jikin namijin da ke cikin zanen nawa".
"Idan za ka kalli wannan zanen sosai, za ka gane ƙarin bayani game da abin da ake nufi mutum ya zama baƙar fata kuma ɗan Birtaniya."
'Waye zai yi ninƙaya?'
Daga jerin zanensa mai take "Reflections", Mensah ya ƙara bayyana dangantakar da baƙaƙen fata da dama suke da ita da ruwa ko a wannan zamanin namu.
"Wannan zanen na duba ne da cigaban da baƙaƙen fata suka samu wajen samun 'yancin yin amfani da wasu wurare da a baya aka haramta musu. Ɗaya daga cikin zanen a jerin zane zanen shi ne kan baƙar fata a wasannin motsa jiki kamar wasan polo na cikin ruwa."
"Wannan zanen musamman ya samo asali ne daga wani wanda ke da tsatson Ghana da ke zama a Amurka, wanda yanzu yake aiki tare da matasan Afrika a nahiyar, yana ƙarfafa su su shiga wasannin motsa jiki na cikin ruwa ba don neman abinci ba kaɗai, har ma don su sauya irin labarin ƙasƙanci da ake bayarwa game da dangantakar baƙar fata da ruwa," Mensah ya gaya wa TRT Afrika yayin da yake tuna dubban ƴan cirani ƴan Afrika waɗanda suka rasa rayukansu yayin da suke ƙetare kogin Mediterranean.
Sahihin zane
Wani zanen mai take 'Ɓatan Kai' wani jan hankali ne kan ka rayu a yanzu kuma ka yi sha'awar abubuwan jin daɗi na rayuwar yau da kullum.
"Kasancewa a wannan doron duniyar na nufin cewa za mu rayu na wasu shekaru a wannan duniyar kafin mu koma wata," ya faɗa.
"Gadar da take cikin wannan zanen na nuni da waɗannan al'amurra guda biyu, yayin da kayan kaɗe-kaɗen wani tuni ne na a koma tafarkin abubuwa na gaskiya a kowane lokaci."
Shawararsa ga masu zane masu tasowa:
"Abin farin ciki, dandalin sada zumunta ya kawar da wasu masu kawo wa aikin zane-zane tarnaƙi, saboda haka ka tallata aikinka a can don mutane su ga abin da za ka iya yi,"
"Muddin da gaske kake aikin fasaha, duniya za ta ƙarasa maka sauran aikin."