Zubeda: Matashiya 'yar kasar Kenya da ke da fasaha ''ta ban mamaki'

Zubeda: Matashiya 'yar kasar Kenya da ke da fasaha ''ta ban mamaki'

Ayyukan zane-zane na Zubeda suna jan hankalin mutane daban-daban a Nairobi da Mombasa.
Rufe makarantu da ba a taɓa yin irinsa ba a lokacin annobar COVID-19 a cikin 2020 ya zo da wani sauyi ga Zubeda. . Photo: TRT Afrika.

Daga Fathiya Bayusuf

TRT Afrika, Mombasa

Zubeda Shaaban Maloba wata abar burgewa ce a fannin fasaha da ke zaune a birnin Mombasa da ke gabar teku a Kenya.

Matashiyar mai shekara 16 ta sauya salon soyayyarta ga kasarta zuwa samar da zanen hotunan wurare masu ban sha'awa da na dabbobi.

Zubeda ta fara harkokin fasaha tun tana 'yar shekara 6 ta hanyar zane a bango da takardu a gidan iyayenta.

Zubeda ta shaida wa TRT Afrika cewa, "Ina jin daɗin zane, da binciko nau'o'in fasaha daban-daban. Wannan sha'awar ta fara ne tun a farkon shekaruna, ba wani yunƙuri na baya-bayan nan ba.

"Tare da goyon bayan mahaifiyata ne na fahimci baiwata ta fasaha," Zubeda ta shaida wa TRT Afrika. Mahaifiyar Zubeda, Swalha Omar, tana cikin wadanda suka fara lura da hazakar diyarta.

"An haifi Zubeda da baiwar zane, tana bayyana kanta ta hanyar zane-zane a bango da ananan takardu. Ƙawayenta na makaranta ne suka ga yuwuwar ta zama fitacci a fasaha. A lokacin ne na gane babbar baiwar da take da ita," Swalha ta shaida wa TRT Afirka .

Ƙalubalena

Rufe makarantu da ba a taɓa yin irinsa ba a lokacin annobar COVID-19 a cikin 2020 ya zo da wani sauyi ga Zubeda.

Zubeda ta fara sha'awar yin zane tun tana 'yar shekara shida. Photo: TRT Afrika.

Rungumar fasaha da zuciya ɗaya ya sa ta sadaukar da kanta don inganta ƙwarewarta kuma ta ƙirƙiri tarin ayyukan fasaha, tana nuna su akan zane na dijital na Instagram. Wannan ya sauya 'basirarta' zuwa sana'ar fasaha mai tasowa.

“A lokacin annobar cutar korona, saboda rashin zuwa makarantar boko da ta islamiyya, sai na zurfafa wajen yin zane-zanen a takarda tare da inganta sana’ata ta kafafen sadarwa na zamani, hakan ya sa na ƙirƙiro wani ƙaramin littafi na zane, daga baya na mayar da hankali kan zanen da ya shafi launuka ta hanyar amfani da manhajar canvas, lamarin da ya sa ayyukan fasahata suka bunƙasa," in ji Zubeda.

Yin la'akari da abubuwa uku a lokaci daya na zuwa makarantar boko da islamiyya da ayyukan fasaha sun haifar mata da kalubale. Amma duk da haka Zubeda ba ta karaya ba.

Bayan fagen zane, ta gano son aikin ado na duwatsu, inda take haɗa kyawawan mundaye waɗanda ba kawai ƙawata wuyan hannu suke ba, har ma suna taimakawa tattalin arzikin danginta.

Zubeda ta shiga aikin zane-zane sosai yayin kulle-kullen COVID-19. Hoto: TRT Afrika

Ayyukan zane-zanen Zubeda sun zamo hanyar samun kuɗaɗen shiga da ta tallafa wa gidansu tare da ba da gudunmawa ga karatun ƙannenta.

Nasarar da matashiyar ta samu sun zo ne da ƙalubale masu yawa waɗanda ba ta yarda sun durƙusar da ita ba, sai suka ƙara mata azamar yin aiki tuƙuru don shawo kan lamarin.

"Fafautukata ba zo da sauƙi ba. Akwai lokuta na karaya, ana tambayar ko zanen nawa zai samu karɓuwa. Matsalolin samun kayan fasaha sun haifar da ƙarin cikas, "in ji Zubeda.

Hazaƙa ta musamman

A fannin zane-zane da ke bunƙasa a Nairobi da Mombasa, Zubeda ta baje kolin zane-zanen nata masu ƙayatarwa a wajen baje koli daban-daban, wanda ya jawo hankalin jama'a da dama.

Benjamin Livoi yana bai wa Zubeda shawarwari bayan ya lura da basirarta. Hoto: TRT Afrika

Yanzu Zubeda tana samun horo a Cibiyar fasaha ta Afirka. Benjamin Livoi yane ba ta shawara a cibiyar bayan ayyukanta sun burge shi. Ya bayyana hazaƙar ta a matsayin ta ƙwarai.

"Bajintar fasahar Zubeda ta bambanta, musamman idan aka yi la'akari da shekarunta. Idan aka kwatanta zane-zanenta da na takwarorinta, ta shige gabansu.

"A cibiyarmu ta fasaha, muna da burin inganta hazaƙarta, ta yadda za ta kai ga samun karɓuwa a duniya, ana shirin shigar da ita cikin harkar fasaha. Muna shirin yadda za mu sanya ta a cikin ayyukanmu a lokacin da take hutu, da ba ta damar koyara da basirarta ga matasa masu sha'awar zane-zane," in ji Benjamin Livoi.

"Bayan na kammala karatuna, ina da burin zama masaniyar zanen gine-ginen a kan irin fasahata," Zubeda ta kammala da cewa.

TRT Afrika