Daga Pauline Odhiambo
Masu aikin fasaha da masu sarrafa kayayyaki dangin tufafi suna tasirantuwa da halittu shekaru aru aru,suna ɗan tsakurar wani abu daga kyaunsu, banbancinsu da sarƙaƙiyarsu domin samar da ayyuka da za su samu wajen zama a zukatan masu sha'awa.
Mai Ɗinkin Jaka ƴar Ethiopia Ruth Girmay ta zaɓi Nile perch, wani nau'in kifi ɗan asalin Afrika, a matsayin nazari,kafa da kuma saƙonta ga bukin baje kolin kayan fata na Africa Talent Leather Design Showcase 2024.
Jakarta da ke nuni da kamun kifi fiye da kima "Overfishing Bag", wacce aka ɗinka da fata mai ƙwari kuma tana da hadafin jawo hankali game da barazanar ɓacewa gabaɗaya da kifi nau'in Nile perch yake fuskanta, ta ba ta damar lashe kyautar Mai Ɗinkin Jaka Da Ta Fi Kowa Cancantar Yabo a bukin na Real Leather Stay Different (RLSD) a Addis Ababa daga ranakun 8 zuwa 10 na Nuwamba.
Bisa taken bukin baje kolin - "Sake Bayyana Rawar Da Harkar Ado Ke Takawa Kan Tasirin Aikace Aikacen Ɗan'adam Kan Muhalli" - Jakar da Girmay ta ɗinka tana nuni ne game da tattala halittu kamar yadda kuma take nuni da abin da harkar sarrafa fata a Afrika za ta iya zama nan gaba da kuma rawar da ɗorewar tsara abu za ta taka wajen sake fasalin harkar ado.
Alamar harafin 'O' ta jakar hannun an shata ta ne ta yi kama da idon kifin na Nile perch, yayin da sauran jikinta ke kama da gangar jiki da jelar kifin," Girmay ta bayyana a wani fefen bidiyo da RLSD ta wallafa a shafin Instagram.
Ƙalubalen Girmay shi ne ta yi amfani da ƙawa da ke tattare da aikin sarrafa fata ta isar da saƙon kan kamun kifi fiye da kima kasancewa ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sa yawan kifi nau'in Nile perch a ruwan Afrika ke raguwa
A lafazi irin na tattala halittu, kama kifi fiye da kima na nufin raguwar nau'in kifi daban daban a cikin ruwa cikin hanzari fiye da haihuwarsa
Hukumar kula da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), wacce ta bibiyi nau'in halittun ruwa fiye da 500 a faɗin duniya, ta yi ƙiyasin cewa kusan kaso 90% na kifi a duniya imma an kama su ne fiye da kima ko kuma an kama su ba bisa ka'ida ba.
Ado mai dalili
Gabaɗaya ayyukan Girmay suna nuni ne da kare mataki muhalli daban daban yayin da ake kare hanyar neman abincin al'umomin da suka dogara da su.
Fatar da ba ta yi wa muhalli lahani, kayan aikin da ta zaɓa ta yi aiki da shi, kayan aiki ne da ya fito daga gonannaki da ke amfani da hanyoyin kaucewa yi wa muhalli lahani a maimakon su fito daga masana'antu na kasuwanci da a galibin lokaci suke amfani da sinadarai masu hatsari kuma suke bayar da gudummawa wajen ƙara yawan shara a duniya.
Masu sarrafa fatar da ba ta yi wa muhalli lahani suna ƙoƙarin rage tasirin ta kan muhalli ta hanyar yin amfani da kimiyya wajen noma.
Saɓanin a noma mai yawa, hadafin shi ne a samar da yanayin aiki bisa ka'ida ga waɗanda aka ɗauka aiki a masana'antar fata.
Idan muka inganta kayayyakin da ake sarrafawa da fata,za mu samar da ƙarin kuɗaɗen shiga, da samar da aiki ga jama'a na tsawon lokaci da kuma tabbatar da cewa harkar sarrafa fata a Afrika ta bunƙasa a faɗin duniya," daraktan gudanarwa na cibiyar Africa Leather and Leather Products Institute, Nicholas Mudungwe ya bayyana a wajen bukin bayar da kyautar.
Mafarin fikira
Baya ga Girmay, an karrama ƴan Afrika masu aikin sarrafa fata da yawa saboda kyakkyawan ayyukansu a ɓangarori daban daban kamar kayan sawa, da kayayyakin da ake amfani da su da kuma takalma.
Kyautar zaɓin mutane tana bai wa jama'a damar zaɓar abin da ya fi burge su.
Eddie Louis ɗan ƙasar Uganda ya lashe kyautar ɗinka kayan sakawa saboda rigunan da ya sarrafa da fata, da suka samo asali daga tarihi da kayan ƙawa da ke nuna kariya da jajircewa.
An bai wa mai aikin sarrafa fata ƴar ƙasar Zimbabwe, Nompumelelo Marilyn Samambgwa kyautar wacce ta fi kowa sarrafa takalma saboda jerin ayyukata na "Amaluba", da ya ƙunshi wasu nau'ika na fata a matsayin wata gingina ga halittu tare da kamfanin kayan ƙawa na 3D.
Stephen Maosa ɗan ƙasar Kenya ya lashe kyautar zaɓin jama'a saboda "Jakar Tafiya Mai Sauƙin Sarrafawa" da ya yi wacce aka yi amfani da kashi 75 na fatar Kenya da kuma kashi 25 na wani nau'in daban. Jakar da aka tsara domin matafiyi a wannan zamanin tana nuna ƙarko da sauƙin sarrafawa.
Girmay ta lashe kyautar saboda "Jakar kamun kifi fiye da kima". A bukin 2023, ta ɗinka Jakar Komai da Ruwanka", da aka yi amfani da siffar alfadari a matsayinsa na siffantuwar kyau da daidaito da kuma ƙarfi.