Daga Staff Reporter
Kiristocin Orthodox na gudanar da bukukuwan Kirsimeti da sauran shagulgula da ake gudanarwa a ƙasashe da dama, wasu ma a Afirka.
A kasar Habasha, an gudanar da tsayuwar dare a jajibirin Kirsimeti na ranar Litinin kuma mabiya addinin Kirista sun halarci taron coci a ranar Talata.
Kiristocin Orthodox suna bikin Kirsimeti a ranar 7 ga Janairu, bisa ga lissafin kalandar Julian.
Sauran ƙungiyoyin Kirista suna bin kalandar Gregorian, suna bikin Kirsimeti a ranar 25 ga Disamban kowace shekara.
A Addis Ababa, masu ibadar sun kunna kyandir kuma suna bin ja-gorancin limamai, waɗanda suka rera waƙoƙin ruhaniya.
Jama'a sun sanya fararen tufafi, alamar tsarki da kariya daga mugayen abubuwa. kamar yadda yake a al'adarsu.
“Yana da kyau sosai kasancewa cikin wannan al’ummar Kirista. Ina fata dukkan matasan su zo nan su yi murna tare da mu,” in ji Kibir Girma, wata mata ‘yar shekara 23, kamar yadda ta shaida wa manema labarai a lokacin taron ibadar a Addis Ababa.
Kiristocin na Orthodox suna bikin Kirsimeti ta hanyar haɗuwa tare da danginsu da abokansu don yin liyafa.
An gudanar da irin wannan bukuwan a Masar da Eritriya wadanda ke da Kiristocin Orthodox masu yawa.
A kasar Masar, an gudanar da wani taron majami'a na bikin jajibirin Kirsimeti a Cocin Arch Michael Coptic da ke babban birnin Alkahira.
Shagulgulan biki sun yi kyau a tsakanin mahalartan da suka taru a majami'u a faɗin Masar.