Wadanda suka shirya wajen sun ce maziyarta za su ga kayan tsohuwar Masar da babu irin su a wani waje.  Hoto: GEM

Masar ta ce ya kamata masu sha'awar zane-zane da sassaƙa a Afirka da ma sauran nahiyoyi su zo su shaida 'sabuwar duniyar adana al'adu da baje-kolinsu", a yayin da aka sanar da ranar ƙaddamar da Babban Gidan Tarihi na Zamani na Masar.

A ranar 3 ga Yuli, Masar a hukumance za ta ƙaddamar da Babban Gidan Adana Kayan Tarihi na Masar, wanda ke da girman sukwayamita 500,000, ninki biyun wajen da aka gina Gidan Adana Kayan Tarihi na Louvre da ke Paris kuma ninki biyu da rabi na Gidan Adana Kayan Tarihin Birtaniya, in ji masu shirya waje a wani sako ta shafin Twitter a ranar Talata.

Gidan Adana Kayan Tarihin na babban waje mai girman 500,000 sukwayamita. Hoto: GEM

Dr. Ahmed Ghoneim, Shugaban Hukumar Kula da Gidan Adana Kayan Tarihi Mai Girma na Masar, ya kira wajen da sunan bigiren tarihi da aka sadaukar ga sakafar tsohuwar Masar.

"Kwanaki 100 kenan da na fara wannan aiki, kuma a yayin da ake tunkarar lokacin bude wajen, ina jin alfahari da sauke nauyi," Ghoneim ya fada wa manema labarai.

Ana sa ran daukar kwanaki da dama ana kaddamar da gidan adana kayan tarihin. Hoto/ GEM

Babban Gidan Adana Kayan Tarihin na Masar na nan a kan Tsaunukan Giza, kuma yana kusa da tuddan Pyramid da ke kusanci da Filin Tashi da Saukar Jiragen Sama na Sphinx na Kasa da Kasa.

Ghoneim ya ce bikin zai haura na kwana guda, inda akwai yiwuwar a dauki kwanaki ko ma makonni ana yin sa, ana kuma kashe kwarkwatar idanuwa da kayayyaki na kasa da kasa.

"A yanzu muna shirin abubuwa da yawa, kuma bikin na iya daukar tsawon kwanaki - watakila kwanaki uku, ko ma watanni da yawa. Kamitocin manyan mutane na tattauna wadannan tunane-tunane karkashin jagorancin Ministan Yawon Bude Ido da Al'adun Baya, sannan kuma a karkashin kulawar Firaminista." in ji Ghoneim.

An kashe dala biliyan 1.2 don gina gidan adana kayan tarihin. Hoto: GEM

Tun ma kafin kaddamar da shi, Gidan adana kayan tarihin na zamani ya samu yabo daga kasashen duniya, ya lashe babban Kambin Versailles daga hukumar UNESCO a 2024, inda ta amince da shi a matsayin waje mai kyawun tsari da gini.

Gina wannan waje na tarihi na bayyana zuba jarin kudade a yawa, inda Ghoneim ke cewa an kashe dala biliyan 1.2, wanda dala miliyan 750 ranto su aka yi, gwamnatin Masar kuma ta cika sauran.

A waje mai girman sukwayamita 500,000, Gidan Adana Kayan Tarihin zai zama daya daga cikin mafi girma a duniya. Hoto: GEM

Masu kula da wajen sun kuma bayyana cewa bikin bude wajen zai zama aikin Masar kawai, bayan nasarar manyan taruka irin su Faretin Masarauta a watan Afrilun 2021, da kaddamar da Filin Jirgin Saman Sphinxes a Luxor, shi ma a 2021.

Girman Gidan Adana Kayan Tarihin ya kai sukwayamita 500,000, ya fi gidajen tarini na Louvre da Birtaniya girma.

Wadanda suka shirya wajen sun ce maziyarta za su ga kayan tsohuwar Masar da babu irin su a wani waje, da ma kambin Sarki Tutankhamun.

TRT Afrika