Daga Charles Mgbolu
Tallan shirin fim din "Shekko" na ci gaba da yaduwa a shafukan sada zumunta bayan nasarar da fim din ya samu na sayar da na fam din Masar miliyan 52 (1,085,000) bayan shafe makonni 17 a gidajen cinema, kamar yadda akwatin tattara bayanan gidajen sinima na masar ya sanar.
Fim din da Karim El-Sobky ya bayar da umarni ya ta'allaka ga littafin kagaggen labari na Chuck Hogan mai suna "Prince of Thieves" (Yariman Barayi).
El-Sobky, wanda ya bayar da umarnin shirin ya samu nasara a fina-finan Masar da dama da suka hada da 'Boshkash da A Whole One', kuma ya samu yabo sosai tun bayan sakin shirin fim din Shekko.
A daren da aka fara sakin shirin, an samu kudi har fan miliyan 1,200,000 dai-dai da dala $25,053.
Fim din ya kuma samu yabon bayar da taurari 7.3 kamar yadda elcinima suka sanar.
Shekko ya samu rabanu na fan miliyan 9,797,486 a kowanne mako kuma shi ne shirin fim din da ya fi kowanne samun kudi a Masar a tarihin gidajen kallo na cinema na kasar kuma a lokacin bikin Sallah.
Farfadowar cinema bayan Covid-19
A fadin kasar Masar, sha'awar kallon fina-finan da aka samar a cikin gida ta dawo bayan annobar Corona, lokacinda aka shaida dakunan shirya fina-finai na ta tafka asara.
Rufe duniya da aka yi lokacin annobar ya janyo bangaren shirya fina-finai a Masar yin asarar fan miliyan 270, kamar yadda alkaluman da Cibiyar Nazarin Tattalin Arziki ta Masar ta fitar.
Kudaden da ake samu bayan annoba ba su da yawa amma abun a yaba ne, ina gidajen cinema na kasar suka samu dala miliyan huɗu a 2023, kamar yadda ofishin Tattara Bayanai na Mojo ya sanar.
Sai dai kuma, wannan adadi ya yi kasa sosai idan aka kwatanta a dala miliyan $18 da aka samu kafin zuwa annobar Covid-19 a 2014.
Babbar gogayya
Gidajen cinema a Masar na bukatar sanya idanu sosai kan makociyarsu Saudiyya, inda masarautar ta sanar da cewa za ta zuba jarin dala biliyan 64 a bangaren shakatawa da sharholiya na kasar, kamar yadda Bloomberg ta sanar.
Wannan zai iya sanya Saudiyya zama cibiyar shakatawa da jin dadi ta Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka, inda nan da 2023 kasar ke son bude gidajen kallo na cinema 2,000.
A yanzu haka, akalla dai masana'antar fina-finai ta masar za ta yi murnar wannan nasara ta Shekko, wadda ta dawo da su kan hanya.
An yi hasashen a 2024 kudaden shiga a masana'antar fina-finai da gidajen cinema na iya kai wa dala miliyan $8.37, kamar yadda Statista suka sanar.
Shekko, shirin baya-bayan nan da ya samu gagarumar nasara, zai ci gaba da kasnace a gidajen kallon kasar Masar har nan da 'yan kwanaki.
Fim din ya nuna sanannun jaruman kasar irin su Amr Youssef, Mohamed mamdouh, Yousra, Dina El-Sherbiny, Amina Khalil da Abbas Abu Al-Hassan.