Musulmai a faɗin Afirka da ma duniya gaba ɗaya sun gabatar da Sallar Idi, kuma suna ci gaba da shagulgulan Eid al-Fitr, wadda ranar biki ce da ke zuwa bayan watan Ramadana.
Ana gudanar da shagulgulan ne tare da iyali, da haɗuwa da dangi, da kuma sanya sabbin kaya da cin kayan maƙulashe.
Al'ummar Musulmi sun gabatar da Sallar Idi a filaye da masallatai, da ma kan tituna da harabobin masallatai.
A Chadi, sojoji sun bar motocinsu suka ajiye makamansu don gabatar da Sallar idi tare da sauran Musulmai a safiyar ranar idi.
A babban birnin Kenya, Nairobi, taron masallata sun haɗu a filin da ke yankin Ngara don gabatar da sallar idi.
A ƙauyen Abu Sir na yankin Giza a Masar, mutane sun fito da balo mai launin tutar Falasɗinu suka taru don gabatar da addu'o'i na neman zaman lafiya a Falasɗinu, kamar yadda suka ambata.
“Barka da Sallah, ina fatan kwanakin da ke tafe na farin ciki ne. Allah ya taimaki 'yan uwanmu a Falasɗinu kuma ya kare su. Kuma, in sha Allahu za su yi Idi cikin aminci da rahama,” cewar Abdallah Mohamed.