Daga Charles Mgbolu
An yi bikin ranar Kirsimeti a dukkan fadin duniya a yanayi daban-daban, an yi casu da taruka a coci-coci.
Sakonnin sun bayyana lokuta daban-daban na shekarar da za ta kare.
A shafukan sada zumunta, gwarazan 'yan wasa na Afirka sun fitar da sakonni, mafi yawa na tunawa da wani al'amari da ya faru a shekarar nan.
Kyaftin din kasar Masar kuma dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah ya yada hoto mai baki da fari na wata bishiya da aka kunnawa fitilu tare da sakon jan hankalin duniya ga halin da ake ciki a Gaza.
A wani sako da ya fitar ta shafin Instagram, Salah ya ce "Kirsimeti lokaci ne da iyalai suke haduwa waje guda su yi murna. Tare da mummunan yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya, musamman kisa da rusau a Gaza, mun is aga lokacin Kirsimeti na wannan shekarar cikin bakin ciki da bacin rai, kuma muna jin radadi irin na wadanda suka rasa masoyansu. Kar ku manta da su, kar ku saba da wahalar da suke sha."
Shi ma da yake yada hoton matarsa da yaronsa, kyaftin din kungiyar Super Eagle ta Nijeriya Ahmed Musa ya yi addu'ar samun zaman lafiya a yayin da duniya ke tunkarar sabuwar shekara.
"Ina muku fatan alheri. A wannan lokaci na biki, Ina addu'ar ku samu farin ciki da zaman lafiya, ina fatan biki da murna ba za su gushe daga gidajenku ba, Barka da Kirsimeti."
Mai tsaron raga na Ghana Lawrence Ati Zigi na cike da farin ciki, wanda shi ma ya fitar da bidiyonsa yana rawar gargajita ta Ghana da ake kira Agbadza tare da iyalinsa.
A saman bidiyon ya rubuta "Iyalina da nake kauna".
Agbadza salon kida da rawar Ewe ne da jama'ar Ewe suke yi a yankin Volta na Ghana.
Dan damben Faransa dan asalin Kamaru Francis Ngannou bai bari shekarar ta tafi da shi ba saboda rashin nasara a hannun Tyson Fury da ya yi a ranar 28 ga Oktoba a Saudiyya ba.
Ya saka malafar Kirsimeti, ya yada hoton a shafin Instagram tare da rubuta "Barka da Kirsimeti daga ni zuwa gare ku baki daya!!!
Gwarzon kwallon kafar Nijeriya Kanu Nwanko ne z amu rufe da shi inda ya yada nasa sakon Kirsimeti da yin addu'ar fatan samun zaman lafiya a shekara mai zuwa.
A shafinsa na Instagram ya rubuta "Barka da Kirsimeti, Ina Addu'ar Ubangiji ya kare, ya albarkace mu tare da ci gaba da kasancewa tare da mu".