Duk da matakan da aka dauka da tasirin da ake ganin sun yi, amma duk da haka an bayar da rahotanni na sayen kuri’a – da kudi da kuma kayan abinci /Photo AA

Daga Mustapha Musa Kaita

Daya daga cikin abubuwan da aka fi tattaunawa a lokacin zaben shugaban kasa a Nijeriya shi ne karancin kudade a hannun jama’a da ‘yan siyasa.

Wannan sabon lamarin ya samo asali ne daga sabon tsarin babban bankin Nijeriya na fitar da sabbin kudaden da aka sauya wa fasali, da kuma tilasta daina amfani da tsofaffin kudi.

An aiwatar da wannan sabon tsarin ne makonni kadan kafin zaben shugaban kasar wanda aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, wanda dan takarar Jam’iyyar APC mai mulki Bola Tinubu ya yi nasara a zaben inda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari.

Sauya fasalin kudin Nijeriya ya zo da kalubale iri-iri da suka shafi hada-hadar kudi a lokacin zabe – wani sabon abu a kasar wadda aka sani da amfani da kudi a lokacin zabe tsawon shekaru.

Cikin lokaci kadan tsoffin kudi suka bace sannan kuma sabbin kudin babu isassu.

Babban Bankin Nijeriya ba wai ya sauya fasalin kudin ba ne kawai, sai dai kuma ya kayyade adadin kudin da mutum zai iya cirewa daga banki a kasar da ta fi kowace karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika.

Gwamnatin Najeriya ta ce ta fito da wannan sabon tsarin na sauya kudi domin yaki da jabun kudi da rashin tsaro da halasta kudin haram da kuma dakile hauhawar farashi.

Sai dai a irin wannan lokaci – daf da babban zabe, wannan tsarin ya yi tasiri matuka a siyasance ga kasar dimokradiyya mafi girma a nahiyar Afrika.

Wasu sun ce wannan tsarin ya sa sayen kuri’a ya yi wahala a Nijeriya.

Wani wanda ya sa ido a kan zabe a birnin Kaduna da ke arewacin Nijeriya Abubakar Ibrahim, ya bayyana cewa adadin kudaden da aka yi amfani da su a lokacin zabe a bana “sun takaita” idan aka hada da zabukan da aka yi a baya.

Ya ce akwai yiwuwar karancin kudin da ake fama da shi ne ya haddasa hakan.

A zabukan da aka gudanar a baya, an ga yadda wasu 'yan siyasa ke fitowa fili suna raba bandir-bandir na kudi ga masu zabe.

Haka kuma ya bayyana cewa a baya sayen kuri’a abu ne da ake gani a fili a rumfunan zabe da ke cikin birane, amma a bana abin ya zama daban saboda “akwai karancin kudi kuma ba a iya raba abinci a fili".

Wani abu da ake ganin ya hana siyan kuri’un a fili shi ne yadda jami’an yaki da cin hanci da rashawa suka je wasu rumfunan zabe musamman a birane.

Sabon salo

Duk da matakan da aka dauka da tasirin da ake ganin sun yi, amma duk da haka an bayar da rahotanni na sayen kuri’a – da kudi da kuma kayan abinci.

Ana zargin hakan ya faru a kusan duka sassan kasar kuma kusan dukkan jam’iyyu na da hannu.

Wani mai zabe a Jihar Kano wanda bai so a bayyana sunansa, ya shaida wa TRT Afrika cewa a gabansa aka rinka raba wa masu zabe tsabar kudi, amma shi bai karba ba.

A jajibirin zaben shugaban kasar, sai da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta kama wani babban dan siyasa a Jihar Ribas da ke kudancin kasar wanda ake zargin yana da niyyar sayen kuri’u.

Hukumomi sun ce an kama shi da kusan dala 500,000, ana kuma zargin an kama shi da jadawali na sunayen wadanda za su amfana da kudin duk a cikin motarsa, a lokacin da yake hanyarsa ta zuwa mazabarsa domin zabe.

Dakta Tukur Abdulkadir wanda malamin kimiyyar siyasa ne a Jami’ar Jihar Kaduna, ya ce a ganinsa kusan babu wani abin da ya sauya ta fuskar sayen kuri’a bayan wannan sabon tsarin kudin na Nijeriya.

“Ba da kudi kawai ake sayen kuri’a ba, ana amfani da tufafi da abinci da wasu hanyoyi da dama."

Dakta Tukur ya bayyana cewa akwai wasu 'yan siyasa da suka yi kokarin kauce wa takunkumin da aka saka na cire kudi inda ake zargin sun rinka tura kudi ta asusun ajiyan wasu masu zabe.

“An yi amfani da hanyar tura kudi ta waya matuka,” in ji Dakta Tukur. Mai sa ido kan zabe Ibrahim ya bayyana cewa a wannan lokacin “wadanda kawai suke da asusun banki” ne ake zargin sun samu kudi daga yan siyasa.

Abu ne mai wahala a iya gane adadin kudin da yan siyasa da jam’iyyu suka kashe a lokacin zabe a Nijeriya – a zaben baya da na yanzu – sakamakon babu wasu hanyoyi na musamman da aka tanada domin sa ido.

Auwal Musa Rafsanjani daga kungiyar Transparancy International, wanda ya shafe shekaru yana sa ido kan zabukan Nijeriya ya shaida wa TRT Afrika cewa kusan babu wasu bayanai sahihai da ke da akwai game da kudin da ake kashewa a lokacin yakin neman zabe.

Karancin masu zabe

Wani kuma tasiri da sauyin kudin Nijeriya ya yi shi ne batun karancin fitowar masu jefa kuri’a a zaben da ya gabata.

A lokacin zaben shugaban kasa, kashi 29 cikin 100 ne kacal na 'yan kasar miliyan 87 da suka cancanta su yi zabe kacal suka fito suka kada kuri’unsu – wanda wannan shi ne adadi mafi karanci tun bayan dawowar Nijeriya kan turbar dimokradiyya a 1999.

Dakta Tukur Abdulkadir na Jam’iyyar Jihar Kaduna ya ce karancin fitowar jama’a a wurin zabe yana da alaka da karancin kudin da ake fama da shi.

Ya bayyana cewa “sauyin kudin da aka yi ya fusata mutane matuka, haka kuma ya takaita adadin mutanen da ke fita wurin zabe saboda ba su ji dadin yadda wannan matakin ya takura wa rayuwarsu ba”.

Duk da cewa babu wani dan siyasa ko jam’iyya da suka fito fili suka yi magana kan tasirin sauyin kudin a lokacin zaben, amma kafin zaben wasu sun fito sun yi magana kan yadda karancin kudin zai iya shafar gudanar da zaben.

Bayan kammala zaben shugaban kasa, gwamnatin Nijeriya ta cire takunkumin da ta saka na amfani da tsoffin kudi domin yin biyayya ga hukuncin Kotun Kolin kasar.

Daga nan ne sai wasu bankuna suka soma sakin wasu daga cikin tsofaffin kudi domin amfani jama’a, amma duk da haka tasirin matakin sauyin kudin na taba jama’a.

A takaice dai babu tabbaci ko wannan tsarin zai zama na din-din-din.

Masu sharhi suna da ra’ayin magance siyasar kudi a Najeriya zai iya habaka dimokradiyya a kasar.

Sai dai cimma wannan buri zai iya zama wani jan aiki ga kasar da ta fi kowace yawan jama’a a nahiyar Afrika.

TRT Afrika