Littafin koyon girke-girke na Sarah da Ornélie Yenault saɗaukarwace ga ƙarfin gwiwar da suka samu a fasahar dafa abinci a farkon rayuwarsu daga wajen mahaifiyarsu wacce ta mutu . Hoto: TRTAfirka  

Daga Firmain Eric MBadinga

A matsayinsu na tagwaye masu matukar kama da juna, ba a taba iya bambanta Ornélie da Sarah Yenault.

A lokacin tasowarsu, tagwayen 'yan asalin Gabon sukan yi abubuwan da aka fi sanin 'yan biyu suna yi - kamar yin ado iri ɗaya da dariya a lokaci guda, sannan tafiyarsu iri ɗaya haka kuma a lokuta da dama sukan yi tunani a kan abu iri ɗaya ba tare da sun yi magana da junansu ba.

A yanayin rayuwar Ornelie da Sarah, babu wani abu da suke yi wanda ba ya kama da juna, suna tafiyar da rayuwarsu iri guda, inda suke koƙarin kafa tarihi a duniya a abu ɗaya da ya matukar haɗa su da juna: ƙaunar da suke yi wa fasahar girƙe-girƙe.

Tagwayen sun rubuta wani littafi na girƙe-girke wanda ya zama abin girmamawa ga ire-iren abincin ƙasar Gabon, wanda ya sake fito da abincin ƙasashen Afirka zuwa ga duniya.

Abin da ya sa littafin 'Gastronomie Gabonaise: Voyage à travers le Gabon en 38 recettes' ya zama na musamman shi ne yadda aka fassara yadda ake girke-girken zuwa harsunan gida guda18.

A yanzu haka Ornélie da Sarah, sun cika shekaru 30, kuma ba wai kwatsam suka tsinci kansu a cikin harkar abinci ba. Sha'awarsu ta girke-girke ya samo asali ne tun suna shekara goma lokacin da suka fara makarantar sakandare.

Gastronomie Gabonaise: Voyage à travers le Gabon en 38 recettes littafin girke-girke ne wanda Ornélie da Sarah Yenault suka rubuta tare. Hoto: TRTAfirka 

''Abin da ya ba mu sha'awa game da fasahar dafa abinci shi ne, za mu iya haɗa kayan da muke so tare da yin wani abun da zai yi daɗi a baki,'' kamar yadda tagwayen suka shaida wa TRT Afirka.

''Haka kuma wata dama ce ta fahimtar ɗabi'u da asalin abinci," yanayin da ya matukar haɗa tagwayen wuri ɗaya baya ga kimiyya da yan sanya tunani da kamannin Ornélie da Sarah ya zo iri ɗaya.

Tagwayen sun taso a wuri ɗaya, kana yanayin tarbiyyar da karatunsu da kuma hulda na zamantakewarsu duk iri ɗaya ne.

Haka ya matukar taka muhimmiyar rawa wajen tsara yanayin tunaninsu da halayensu da irin abubuwan da suke so da kuma hanyoyin magance kowane yanayi da warware matsala da ayyukansu.

Sarah da Ornélie sun taso suna dafa abinci tare, inda ya bi jikinsu har zuwa kafa sana'arsu ta fasahar daba abinci a kuruciyarsu.

"Mun kasance ƙawaye na ƙut da ƙut a ko yaushe, yanayin da ya taimaka wa muraɗunmu," in ji 'yan'uwan a tare.

Zuwansu Faransa bayan kammala karatun shiga jami'a a shekarar 2011 ya ƙarfafa burinsu na fasahar girƙe-girƙe.

A 'yan shekaru masu zuwa, tagwayen ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen koyo da sanin sirrin kowane ɗandano da suka ci karo da shi.

Shigarsu wata makaranta ta musamman ya taimaka wajen buɗe idanunsu ga duniyar girke-girken abinci.

Hakan ya taimaka musu wajen haɗin gwiwar rubuta littafi da ya shafi ire-iren abincin asar Gabon.

"Horon da muka samu ya taimaka mana wajen koyon ɗabarun abinci da alaƙar girƙe-girƙen da juna, da kuma yadda ake adana abinci," in ji Ornélie da Sarah.

''A wurin mu, dafa abinci fasaha ce da ke ba mu damar kasancewa tare da kuma sauran mutane a yanayi mai kyau.''

To, ko mai suka fi la'akari da shi a matsayin sinadarin da ya fi muhimmaci a cikin girƙi?

"Kar da a yi jinkirin yin amfani da wani abu mai ɗandano, kamar dai yadda muke tallata abincin Gabon.

Baya ga ingancin abincin, yanayin wuri yana ƙara daɗin abinci,'' a cewar tagwayen Yenault.

Girƙe-girƙen da ke cikin littafin Tagwayen Yenault na nuna irin al'adu da tarihin abincin Gabon. Hoto: TRTAfirka

Sautin girki

Duk da cewa tagwayen sun samu ƙwarewa da kwarin gwiwa a tsawon shekaru, har yanzu dai suna ci gaba da dogaro ne a faɗaɗa da'irar masu ɗanɗana girke-girkensu da suka ƙunshi 'yan'uwa da abokai don sanin ko suna yin daidai ko akasin haka.

Mahaifiyarsu ta kasance ɗaya daga cikin waɗanda ke kan gaba wajen bai wa tagwayen goyon baya kana ta shaida ci gaban da suka samu a duniyar fasahar girƙe-girƙe.

''Wannan litaffin saɗaukarwa ce ga irin ƙaunar da muke yi wa mahaifiyarmu, Kiki Marie Céline da kuma yadda ta nuna goyon bayanta ga girke-girken mu.

Haka kuma, yana nuna irin haɗin gwiwar da muka kulla tsakaninmu da mabiyanmu da iyalansu ta kafofin sadarwar mu," in ji Ornélie.

Mutane da dama sukan bai wa tagwayen sirrin gire-girƙe da suka samu daga wurin iyaye da kakanninsu, wanda aka bayyana a cikin littafin mai shafuka 100.

''Kazalika girke-girke abincin gabon gayyata ce zuwa ga ƙayatacciyar ƙasar Gabon. Mun bayyana tarihin kowane lardi a cikin girke-girke,'' kamar yadda Ornélie ta shaida wa TRT Afrika.

''Littafin ya gabatar da mafi ɗadewa da kuma sanannen hanyoyi da dabarun haɗa girke-girken kamar miyan yakuwa da nkumu (Gnetum africanum),da miyar ganyen rogo da Nyembwe (miyan manja).''

Haɗin abinci na musamman

Littafin Sarah da Ornélie na ɗauke da girƙe-girƙen iri daban-daban har 38 kana an farrasa shi zuwa harsuna 18 na cikin gida. Hoto: TRTAfirka

Ire-iren girke-girken abincin har guda 38 sun gabatar da fasahar abinci Gabon, wanda ya gabaɗaya ya dogara kan ganyayyaki da sinadaren gargajiya.

Littafin nan ya samu lambar yabo guda biyu a Faransa da Sweden, in ji Sarah.

Tagwayen suna ayyukan dafa abincin taruka. Suna alfahari da jin daɗin bai wa mutane labarin fafutukarsu da kuma gabatar musu da abincin Afirka.

Baya ga girke-girken Gabon, sun kuma koyi girkin ƙasar Comoros da Angola da Congo, wanda ya zama sirrin da ya sa suke zaƙuwa don koyon nau'ukan girke-girken wasu sassan.

TRT Afrika