An kiyasta cewa shekarun Kingo ya kai 45 lokacin da ya mutu a watan Disamba 2023. Hoto: Kungiyar Kare namun daji.  

Daga Kudra Maliro

Mutuwar goggon birin da ya yi fice ta bar masu kare namun daji yankin a Kongo-Brazzaville da wasu wuraren cikin bakin ciki.

An tsinci gawar Kingo a ranar 26 ga watan Disamba.

Yana da shekaru kimanin 45 da haihuwa, a cewar kungiyar kare namun daji ta (WCS) tana mai kari da cewa ana ganin mutuwarsa na da nasaba da matsala ta tsufa.

Kingo ya kasance ''daya daga cikin fitattun goggon birai a duniya'' sannan a tsawon shekaru talatin ya karfafa gwiwar masu ayyukan kare namun daji," kamar yadda Ben Evans, daraktan gandun dajin Nouabalé-Ndoki na WCS, ya shaida wa TRT Afrika.

An tsinci gawar goggon birin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo Kingo a ranar 26 ga Disamba. Hoto: Kungiyar Kare namun daji.

''Kungiyar IUCN tana danganta goggon birin da ke rayuwa a kasa a matsayin wadanda ba su da mummunar hadari,'' in ji shi.

Goggon birai kamar Kingo suna daga cikin biran yankin yamma da ba su da hadari. Kingo ya samu sunansa ne daga harshen Ba'aka na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo - "kingo ya bolé" wanda fassararsa yake nufin "mai babbar murya."

Fice a duniya

Shahararriyar dabbar ta dauki hankalin masu yawon bude ido da masu bincike a tsawon shekaru fiye da talatin a gandun dajin Nouabalé-Ndoki da ke kasar Kongo-Brazzaville.

Wasu masu bincike daga kasar Amurka ne suka yi nasarar gano nau'in halittar dabbar Kingo a shekarun 1990, a binciken sun gano cewa goggon birin ya fita daban.

Daga nan suka fara nazari sosai akansa don kara fahimtar dabbar daga yankin yamma wanda ke rayuwa a kasa.

A shekarar 2006 ne kungiyar kare namun daji ta karbi aikin kare su.

Kingo ya shahara a duniya bayan manyan kungiyoyi kasashen duniya ciki har da kungiyar muhalli ta National Geographic ya dauki labarinsa.

Kingo ya ja hankalin masu kare namun daji da masu yawon bude ido daga ko'ina cikin duniya. Hoto: Kungiyar Kare Namun Daji.

Masu rajin kare muhalli sun sanya wa Kingo suna da ''alamar yanayi'' dabbar da rayuwarsa ta zaburar da kare gandun dajin Nouabalé-Ndoki na kasar Kongo da duk wasu namun daji, wanda kuma tahirinsa zai iya zaburar da ayyukan kare duniya har na tsawon wasu lokuta masu zuwa.

Kafa babban tarihi

An sadaukar da gomman shirye-shirye da rubuce-rubucen kimiyya kusan 50 ga rayuwar Kingo.

Yanayin mai ban sha'awa da kuma nutsuwarsa sun shiga zukatan masu aikin bincike, da al'umomi da kuma masu yawon bude ido a tsawon shekaru da ya kwashe a raye kana mutuwarsa ta haifar da wani yanayi mara dadi.

"Kingo ya kafa babban tarihi'' a cewar Jancy Boungou, mataimakiyar kungiyar bincike ta Mondika gorilla reseachers na WCS, wanda ya bi Kingo har zuwa kwanakinsa na karshe.

"A Koyaushe yana karfafa min da abokan aikina gwiwa don kare sauran goggon birrai da gandun dajin Nouabalé-Ndoki," in ji ta.

Kingo ya zaburar da ayyukan kare namun daji a DRC Kongo. Hoto: Kungiyar Kare Namun Daji.
TRT Afrika