Maimakon wasan farauta, matasan Mara na amfani da basirarsu wajen lashe kambi a wasan Javelin na jefa mashi.. / Hoto: WWF-Kenya

Daga Sylvia Chebet

Mashahurin mashin Maasai ba makami ne kawai ba - tsinin mashin na bayyana jarumtar kabilar ta Afirka.

Wannan al'umma ce da kowanne matashi ke fito ya nuna wa duniya kan zaki don bayyana jarumtarsa da cika shekarun balaga.

Amma kamar sauran duniyoyin da ke kewaye da su, kabilar Maaasai na ta habaka. Matasan kabilar sun diana zuwa dazuka don yin wasan jefa mashi.

Mashin wasan zaman ya maye gurbin mashin karfe da suke dauka. A yanzu suna neman albarka a wasan d aya zama daya daga cikin wasanin gasar Olympic.

"Mu ne matasa mashi na Mara," in ji Anthony Njapit yayin tattaunawa da TRT Afirka, yana gabatar da rukunin matasa kusan 50 da suka taru a dajin Mara da ke Kenya don yawon bude ido.

Matasan da ke da gashin kaji a kawunansu, suna sanye da tufafin kabilar Maasai, daure da tsakiyar Maasai, sun taru suna jefa mashi.

Dabarun da suke amfani da su don jifa ba su da kyau sosai, amma duk yunkurin jifa na baiwa mashin damar tafiya mai nisa.

A al'adance, ana bukatar matasan Maasai su kawo kan zaki don bayyana cewar sun girma. / Hoto: WWF-Kenya

"A yayin da muke magana haka, mun bar farautar namun daji," in ji Njapit. "Muna amfani dammasukanmu don yin nasara, ba don yin kisa ba."

Wasa don kare muhalli

Alfred Ole Kurao, mamban matasan Javelin na Mara, ya ce wasan da al'ummar suka kawo ya samar da sauye-sauye da dama.

"Dabbobin da a baya ake harba da mashi a yanzu suna samun kariya saboda wasan jefa mashi."

Shekarun da matasan Maasai suka dauka suna harba mashi a dazuka don kama namun daji, ya taimaka musu sosai wajen samun saukin koyon wasan jefa mashi na zamani javelin.

Tun watan Maris din 2023 ne matasan Mara suke ta atisaye a filin shakatawa na kare dabbobin dawa.. /Hoto: WWF- Kenya

"Saboda kasnacewarsa wasan da yake bayar da kariya ga dabbobin dawa, muna kaunar sa," in ji Richard Soltanai. "Abu ne da muke jin mun saba da shi, ba wai sabo ba ne."

Asusun Kare Muhalli na WWF da ke Kenya ya bayyana matasan na Mara a matsayin "Masu warware matsaloli da suke da manufar nganta zamantakewa".

Asusun ya yi tsokaci da cewa wasan nasara ce ga kare dabbobin dawa. "Suna wayar da kan mutane game da inganci da darajar rayuwar namun daji, suna nuna amfanin kare duniya da dazuka," in ji Kevin Gichangi, babban jami'i a WWF-Kenya.

Karfin gwiwa daga jarumai

WWF-Kenya sun kaddamar da shirin kare dabbobin dawa na 'Mara SIana' don shigar da wasan jefa mashin zamani cikin sana'o'in da ke samar da kudaden shiga ga 'yan wasan.

A lokacin da kwararren jefa mashi dan lasar Kenya Julius Yego ya ga yadda matasan Mara ke jefa nasu, sai abin ya ba shi sha'awa.

Daga baya ya fada wa kungiyar cewa "A matsayin kwararren dan wasan jefa mashi d ake ganin yadda ake jefa shi sosai yadda ya dace, na gamsu cewa muna da masu basira a Mara."

Yego, da ya fara koyon jefa mashi ta hanyar kallon YouTube, ya lashe zinare daga nisan mita 92.72 a Gasar Kasa da Kasa da aka yi a Beijing, wanda ya zama dan kasar Kenya na farko da ya samu irin wannan nasara.

Ya lashe kambin azurfa a yayin gasar Olympic a 2016. A 2015, Yego, Zakarun Gasar Javelin na Afirka, ya samu matsayin Zakaran 'Yan Wasan Kenya na Shekara inda shugaban kasar lokacin Uhuru Kenyatta ya ba shi lambar kasa ta 'Order of the Grand Warrior'.

"Wata rana, zan zama kamar Julius Yego," in ji Alfred Ole Kurao. "Na riga na kammala wasa a matakin kasa."

A yayin da Yego ke shirin fafatawa a gasar maza manya ta jefa mashi a Paris, matasan Mara sun yi masa wata waka, suna fatan zai lashe zinare.

Ya kammala a mataki na biyar bayan ya yi jifa mai kyau a kakar bana a nisan mita 87.72. Wanda ya lashe kambin zinare daga Pakistan Nadeem Arshad ya kafa tarihi da yin jifa daga nisan mita 92.97.

Maasai Mara na daya daga yankuna mafiya yawan namun dawa a duniya, wanda na daya daga cikin abub8wan mamaki takwas a ban kasa da UNESCO ta bayyana. /Hoto: WWF-Kenya

"Ba lallai ka san irin tasirin da ka yi a nan Mara ba. Yana da girma," in ji Carlos Kiu a wani sakon bidiyo da ya aike ga Yego. "Ka karfafa mana gwiwar mu yi amfani da masukanmu don yin nasara. Ba don kashe dabbobin dawa ba."

A yayin da fada tsakanin dan adam da namun daji ya munana a Afirka, wanda sauyin yanayi da amfani da kas aya janyo, wasan jefa mashi na Javelin din Mara na da manufar samar da wasan da zai ba su farin ciki da nishadi, tare da kuma zabuwarwa don daukar mataki kan sauyin yanayi.

TRT Afrika