Manyan baki suna shirye-shirye bikin sabuwar doya. Hoto: TRT Afrika      

Daga Rachida Houssou

Ana bikin sabuwar doya ne a tsaunukan birnin Savalou a cikin fadar sarki.

Kamar kowace shekara, ranar 14 ga watan Agustan shekarar 2023, malaman addini da Sarkin Savalou da jama'arsa da manyan baki sun halarci dandalin da ake bikin al'ada mai tarihin daruruwan shekaru.

Yadda aka gudanar da bikin ya canja kadan amma dalilin shirya sa bai canja ba: wato kare al'ummar daga cututtuka da ake samu bayan cin doya "mai daraja", kamar yadda mutanen yankin suka yi imani.

A gaban dimbin jama'a, manyan baki sun zauna a kusa da abin da za a sadaukar: wata kwarya da aka kewaye da ciyawa da kaji biyu da burkutu da kwanuka da abin da ya fi komai muhimmanci – doya da wuka.

Sarki Dada Ganfon Gbaguidi XV yayin bikin a ranar 14 ga watan Agustan shekarar 2023. Hoto: TRT Afrika

Bayan addu'o'i da iface-iface, daya daga cikin manyan baki ya dauko doyar wadda sai ya yi surkulle kafin ya fara yanka ta, sai a hada ta da abu mai launin ruwan dorawa.

Ana yin wannan ne a gaban idon Sarkin Savalou Dada Ganfon Gbaguidi XV wanda yake zaune a kan kujerarsa ta mulki yana kewaye da jama'arsa.

Ragowar doyar da ta rage ana watsi da ita ne a iska. Daga nan sai su fado a kan mumbari, inda daga nan sai limamin addinin gargajiya ya sanar da alamomin da za a yi amfani da su wajen cin doyar a cikin shekara.

Dawowar abinci

Bayan jawabi da iface-iface, ana kai wa sarkin wani bangare na doyan da wasu manyan masu rike da sarautun gargajiya suka yi amfani da ita. Sarkin yana dandanawa kuma daga nan ya bude sabon babi na cin sabuwar doya a kasar da kuma al'ummar Savalou.

Bayan haka ne ake kawo karshen babin bikin al'adar yanka sabuwar doyar kuma yanzu kowa zai iya cin doyar. Daga nan sai a fara shagulgula!

Mabiya wasu kungiyoyin al'adu yayin da suke rawa lokacin bikin. Hoto: TRT Afrika 

Bikin ya kunshi wake-wake da raye-raye. Doya tana hada kowa da kowa duk shekara. Ana kallon doyar ne kamar jinjiri wanda ya yi wata tara a cikin mahaifiyarta, saboda doya ma tana kwashe wata tara a kasa kafin a girbe ta, kamar yadda wani mazaunin Savalou mai suna Gabin Alognon ya bayyana.

Ga zarar an kammala bikin, galibin bakin da mazauna birnin za su taru a gaban abincin da aka yi wato sakwara da miyar gyada.

Bayan kammala bikin, kowa zai iya cin doya. Hoto: TRT Afrika.

Doya abinci ce mai farin jini a Benin. Mutane da yawa suna son soyayyiyar doya da marece a kasar wacce take Yammacin Afirka.

Benin ta samar da akalla tan 3,150,248 na doya tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021, kamar yadda Fannin da ke Kula da Kididdigar Aikin Gona ya bayyana.

Doya tana taka muhimmiyar rawa a zamantakewa a kasar. "Abinci mai asali a Afirka. Kuma tana da muhimmanci lokacin bukukuwa a wasu yankuna," kamar yadda Nasser Baco na Jami'ar Abomey Calavi ya bayyana.

TRT Afrika