Mazauna birnin Kisangani wanda yake gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, suna shaukin jiran zuwan damina saboda bayyana fara. Hoto: TRT World

Gizaka abinci ce da wasu mutane ba sa iya ci, amma ban da mutanen Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, inda mazauna kasar suke kiwon gizaka.

Mazauna birnin Kisangani wanda yake gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, suna shaukin jiran zuwan damina saboda bayyanar fara.

Ana kiran fara da sunan "Mbinzo" a harshen Lingala. Da misalin karfe 7:00 na safe daruruwan mata ne suke zuwa kasuwar "Limanga du PK5" a birnin Kisangani don su sayar da gizaka, wasu daga cikinsu suna zuwa ne da kafarsu, wasu kuma a kan babura yayin da wasu suke zuwa a mota.

Masu tallan kaya a gefen titi suna zuwa daga kowane bangare cikin murmushi dauke da sako daya "ka dandana, lokacin gizaka ne", suna yawan cewa haka don su jawo hankalin jama'a.

Idan kana so ka dandana gizaka, to ya kamata ka je tsakanin watan Yuli zuwa Agusta, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

Maye gurbin nama a abinci

Idan ba haka ba, to sai ka jira zuwa badi saboda abu ne na lokaci zuwa lokaci. Mapenzi Vahirwe, dan kasuwa mai shekara 26, bai taba bari lokacin fara ya wuce shi ba a shekara 10 da suka wuce.

Masu tallan kaya a gefen titi suna zuwa daga kowane bangare cikin murmushi dauke da sako daya "ka dandana, lokacin gizaka ne", suna yawan cewa haka don su jawo hankalin jama'a. Hoto: TRT World

"Fara tana da dandano mai dadi kuma za ta iya maye gurbin nama a abinci. Za a iya cin fara tare da wasu nau'ukan abinci. Fara ana cinta ne da ganyayyaki da ayaba da dankali ko kuma fufu," in ji Mapenzi.

Gizaka alheri ce ga birnin Kisangani, mai mazauna miliyan 1.8 kuma yara suna fuskantar karancin abinci da tsaftataccen ruwa.

"Gizaka ta kunshi sanadarai masu muhimmanci ga jiki da kuma samar da kuzari ga jiki," kamar yadda Jacky Kasisa wata masaniya kan lafiyar abinci a asibitin sojoji na Garde Républicaine a Kinshasa ta shaida wa TRT Afrika.

Wasu na so, wasu ba sa so

“Busashiyar gizaka ko wadda aka nika za a iya amfani da ita wajen ciyar da yara wadanda ba sa samun ingantaccen abinci," in ji ta.

Ana samun gizaka ne galibi a dazukan da ke gabar Kogin Kongo.

Duk da kamshi mai dadi da fara take da shi idan aka dafa ta, akwai mutane da dama da ba sa cin gizaka.

Ana samun gizaka ne galibi a dazukan da ke gabar Kogin Kongo. Hoto: TRT World

Sabanin mijinta da 'ya'yanta, Jeanne Kalunga, wanda take shekara 60, ba ta son cin gizaka. Kodayake tana dafa musu abinci da fara a gida.

Lokacin gizaka lokaci ne da kasuwa take bude wa mata wadanda suke shiga dazuka masu duhu don samo fara.

Adèle Mambo tana shiryawa zuwan lokacin gizaka. Kowace safiya, tana tafiyar kilomita 58 a kan babur don zuwa kauyen Wanyerukula, a nan ne ake samun gizaka da daddare.

Tsaraba

"A wasu lokuta ana samun riba biyu ne idan gizakar ba ta rube ba a kan hanya. Misali, na sayi kilogram daya na gizaka a kan francs na Kongo 5,000 (dala biyu), zan iya sayar da irin wannan adadi a kan francs 10,000 zuwa 15,000," kamar yadda Mambo ta bayyana tana murmushi. "Gizaka tana kara mana arziki a lokacinta," in ji ta.

Idan adadin yana da yawa, ana busar da fara saboda a ajiye ta lokaci mai tsawo, wadda za a iya ajiye ta har tsawon wata 12 ba ta yi komai ba.

Farashinta yana ya kan sa a kai ta wasu birane a sassan duniya, inda 'yan uwa da abokan arziki suke jiran tsarabarsu a tsakiyar shekara.

"Ba ni da isashshen kudin siyan kari. Da yake lokacinta kajere ne, zan saye ta da dan kudin da nake da shi," in ji Bahati Kalekele, wani mazaunin birnin Goma wanda ya yi tafiyar kilomita 400 don ya ci kasuwar gizaka.

TRT Afrika