Kilishi mashahurin abinci ne a al'ummar Hausa da ke Yammacin Afirka. Hoto / TRT Afrika

Daga Firmain Eric Mbadinga

Wajen sana'ar Danjoumma da ke birnin Niamye, babban birnin Jamhuriyar Nijar, ya yi kama da manyan shagunan abinci masu nau'uka daban-daban.

Ma'aikatansa sanye da fararen malafa a kansu da takunkumin fuska suna kai kawo cikin hayaƙin da ya turniƙe wajen, suna jera nama a kan teburin gasa kilishin.

Cikin ƙwarewa, ma'aikatan 10 suke reɗe naman suna shimfiɗe shi a kan teburin da aka shimfiɗe a ƙarƙashin rana don ya fara busar da shi. Ana yanko naman ne daga jikin tozon sa, wanda shi ne ɓangaren da abokan hulɗar Danjouma suka rantse cewa shi ne kilishin da ya fi kowanne daɗi a garin.

Mamallakin shagon sayar kilishin, mai shekara 40 yana cikin aiki kace-kace inda yake kai kawo yana sa ido kan dukkan abin da ke faruwa a wajen.

"Ina da ɗumbin abokan hulɗa, kuma yanzun nan za ka ga sun cika wajen nan," ya shaida wa TRT Afrika.

Hausa speakers staple

Kilishi wani nau'in abinci ne da ake yi da nama wanda ya samo asali daga Yammacin Afirka.

Tun kafin zamani ya samar da na'urar firij ƙabilun makiyaya a Nijeriya da Nijar suke da salo na sarrafa nama ta yadda ba zai lalace da wuri ba. Sarrafa nama ya zama kilishi hanya ce ta hana shi lalacewa tsawon lokaci.

"Na fi amfani da naman katara wajen yin kilishin don ya fi daɗi sosai. Da zarar an kammala haɗa naman sai a shanya shi a rana don ya bushe," kamar yadda Danjouma ya yi bayani.

Salon hada kilishi yana bukatar bin mataki-mataki kuma an gaji ilimin da kakanni tsawon karnoni. Hoto / TRT Afrika

Shagon Danjouma yana wani gini ne mai hawa biyu. Ana amfani da hawan farkon ne wajen sarrafa naman da sayar da shi, yayin da aka tsara hanyar gashi na amfani da hasken rana a illahirin ginin.

Abu mafi muhimmancin

Shimfida nama a rana shi ne babban bangare na tsarin. Danjouma da tawagarsa sun kafa kantoci da aka shimfida tabarmar kaba. Bayan an busar da naman, za a masa tsome a mai da kayan kanshi.

Danjouma ya bayyana cewa, "Mataki na gaba shi ne a gasa naman. A sannan ne kilishin zai kammala".

Yayin da wasu suka fi son kilishi ya ji gishiri, wasu sun fi son ya ji yaji, da citta da kuli.

"Idan aka yi kilishi da kayan kamshi yana da nasa dandanon gishiri, amma idan aka sanya masa da yaji, ana kiransa da kilishin yaji," in ji Danjouma.

Dandano kala-kala

Adama Zurkallaini wata 'yar Nijeriya ce wadda take son cin kilishi kuma ta fi son sa ya da yaji sosai.

Ta gaya wa TRT Afrika cewa, "Ina matukar son kilishi. Abin da a baya sai a yankunan Afirka ake samun sa, yanzu ana iya ganin sa a ko'ina a duniya. A yanzu, kana iya samun nau'in kilishi mai dandano daban-daban wanda zai kayatar da kai".

Adama ta kara da cewa, "Za ga ga ana raba kilishi a bikin aure ko suna. Kuma ana sayar da shi kunshe a takarda. Wannan ya nun irin farin jinin kilishi.

Danjouma yana aikinn kwana shida a mako, saboda ya iya cika alkawuran ga kwatomominsa.

Yana mayar da hankali sosai kan inganci da dandanon kilishinsa. Shi ya sa ba ya amfani da kowane nama idan ba sabon yanka ba, saboda ya fi zaƙi.

Kilishi yana da wani nau'in dandano na musamman, kuma yana jimawa bai lalace ba. Hoto / TRT Afrika

Dangi da ke ƙetare

Kwastomomin Danjouma suna yawan dawowa su saya. Wasu na saya ne don kansu, wasu kuma suna sayar wa abokai da 'yan uwansu da ke kasashen waje.

Ya ce, "Na gaji wannan sana'a ne daga iyayena tun ina dan karami. A yau, sai dai na ce, Alhamdulillah. Ina samun kudi da wannan sana'a.Ina iya kula da bukatuna da na iyalaina".

A halin yanzu, kalubalena daya ne, wato rashin tabbas a siyasar kasarsa ta Nijar. Bayan juyin mulkin soji da ya kawar da tsohon shugaban kasa Mohamed Bazoum a watan Yuli, kungiyar ECOWAS da saka wa kasar tarin takunkuman tattalin arziki da ya hada da rufe wasu iyakokin kasar.

Dakatar da harkokin hada-hadar kudi da hana kasar taba kadarorinta a bankuna shi ma ya janyo wa faduwar karfin kudin kasar, wanda hakan ya shafi kasuwanci.

Danjouma ya ce kasuwancinsa yana shan wahala sakamakon takunkumin. Amma hakan bai hana shi cigaba ba, da kyautata fata. Bisa tsarin sana'arsa ta gado ta yin kilishi, haka za a ci gaba da yin sana'ar.

TRT Afrika