Birnin Maiduguri na daga cikin wuraren da aka fi hada-hadar fara a Nijeriya. / Hoto: TRT Afrika

Daga Abdulwasiu Hassan

Ga mutane da dama a Nijeriya, fara ta kasance wani abinci da ake ci mai matukar dadi inda masu cinta ke cewa tana da amfani ga jiki.

Za a iya soya fara ko kuma a gasa ta, inda karar da ake ji yayin da ake taunawa tana sa mai taunawar wani murmushi. Ba shakka shiyasa masoya cin fara suke kiranta da "kifin sahara".

"Idan mutum ya soma cin fara, bana tunanin zai iya dainawa saboda tana da dadi," in ji Maryam Mohammad Kadai, wata mazauniyar Maiduguri da ke arewa maso gabashin Nijeriya.

Kwaron mai ruwan kasa bayan an soya na daga cikin abubuwan sayarwa wadanda aka fi siya a kan titunan Maiduguri.

"Maiduguri na daga cikin garuruwan da za a iya samun fara mai matukar dadi," in ji Maryam.

"Ina cin fara saboda tana da matukar dadi kuma tana kara lafiya. Cin fara na da kyau kuma ba ta da wata illa ga bil'adama," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

Manoma na matukar tsoron fara sakamakon yadda take lalata musu gona. / Hoto: Reuters

"Idan ina cin fara, ina jin kaina a saman duniya sakamakon yadda take da dadi," in ji Bilal, wanda wani masoyin fara ne a tattaunawarsa da TRT Afirka a lokacin da ya sawo kulli uku na farar.

Mutane da dama a wani bangaren kuwa ba su jin dadin cin fara. Sai dai Bilal na ganin fara ta fi abincin da aka dafa sakamakon amfanin da take da ita a jiki.

"Kamar yadda wani ke ji idan an ba shi kaza, haka nake ji idan ina cin fara," kamar yadda ya bayyana a cikin sha'awa

Kakar fara

Ana sayar da kashi daya na fara kan naira 1,500 zuwa 2,000, wanda ya danganta da yadda aka yi oda. Sai dai farar kan yi matukar tsada musamman idan ba kakarta bane.

"Fara ta dan yi tsada a halin yanzu kuma ba ciniki sosai a yanzu sakamakon yanayin gari," in ji Victory Emmanuel, wata mai sayar da fara a tattaunawarta da TRT Afrika.

A halin yanzu fara ta yi tsada sakamakon yadda yanayin gari yake. / Hoto: Reuters

Ta bayyana cewa a rana guda takan sayar da fara ga kusan mutum 100.

Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa fara na da sinadarin gina jiki kaso 40 a cikinta sai kuma kaso 41 zuwa 43 na mai.

Duk da cewa ana kallon fara a matsayin wata barazana ga amfanin gona lokacin kakarsu, amma duk da haka mutanen Maiduguri na son kashe kwadayinsu.

"Muna ganin fari a dajin Mongunu," kamar yadda Mohammed ya bayyana, wanda wani ne mai farautar fari. Ya bayyana cewa suna yawan zuwa farautar fari tun kafin asuba ta hanyar amfani da fitila domin hana su tashi.

An fi samun farar a watannin Nuwamba da Disamba a lokacin sanyi wanda a lokacin ne ake samun iska wanda ke kadawa da kuma kura.

"Kusan watan Nuwamba zuwa Disamba wanda a lokacin ana sanyi, za mu iya samun buhu uku zuwa hudu na fara a rana," in ji shi.

Baya ga Nijeriya, akwai wasu kasashen Afirka da su ma suke son cinta kamar irin su Uganda da makwabtanta.

TRT Afrika