Daga Sylvia Chebet
Marigayi Anthony Bourdain, shahararren marubucin tarihin abinci da al'adu, ya rayu bisa akidar cewa "abinci ba zai iya samar da zaman lafiya a duniya ba, amma zai ya taka wata rawa”.
Domin cike gibin tafiyar dubban mil tsakanin Legas da Landan da wurin sayar da abincinta, Simisola Idowu-Ajibodu – wadda aka fi sani da Chef SiA- na kwatanta duk wani abu da ake cewa kan karfin abincin da aka dafa da kwarewa.
“Yin girki shi ne jin dadi,” in ji Chef SiA a tattaunawarta da TRT Afrika. “Batu ne na yi wa baki girki, da nuna sanayya da kuma tattaunawa wanda hakan zai sa a ji dadi a cikin baki.”
Wurin abincin na Chef SiA wadda ‘yar Nijeriya da Birtaniya ce, ba wai wurin sayar da abinci ne ba na gargajiya mai adireshi.
Ana bude shi ne a rufe a Landan da Legas, kuma ya danganta ne da birnin da take a ranar.
Biranen biyu sun sha bamban ta fannin yanayin cimakarsu, sai dai Chef SiA na da basirar girka abinci iri-iri na yankuna.
Ga wadanda suka samu sa’a aka gayyace su, ba wai batu ne na abinci kadai ba amma wata dama ce wadda za a rinka tunawa da ita. “Ina yawan shaida wa bakina cewa ina tafiya ne da su.
Daga loma daya ta farko na burodina mai dauke da man bota na tafaruwa zuwa kayan zaki na karshe, wanda zai kasance irin su cin-cin da kek, bakina na yawan cika da mamaki da nuna jin dadinsu,” in ji Chef SiA
Abinci iri daban-daban a kwano
Taiwo Ketiku, wadda ke rubutu kan abinci a intanet, ta ce salon yadda take yin abincin na kawata kwanon abinci.
Ta ce sirrin shi ne yin abincin yadda zai yi kamanceceniya da juna. “Ba lallai Kasashen Yamma su ji dadin garin doya ba saboda ba abincinsu bane. Don haka idan ka ba su abinci kamar su ‘shinkafar ofada’ a matsayin ‘ofada crackers’, ko kuna ‘jellof din shinkafa’ a matsayin ‘faten shinkafa, ko kuma milo a matsayin wani abinci a dunkule, mutane za su iya son su,” in ji ta.
“Sai dai ‘yan Afirka za su iya yin ihu su ce ‘abin kunya’ ko kuma ‘ta ya za a mayar da amala abin karas-karas. Ko kuma Iru zuwa gelato? Ta yaya ‘yan Afirka ke shirya abincisu?
“Daga ubangiji ne da kuma kokarin gwadawa,” kamar yadda ta bayyana cikin dariya.
“Akasarin bayanin yadda ake abincina sun samo asali ne daga irin abincin da nake ci ina karama. Na yi aiki a baya. Na san abin da nake so na ji a sabon abinci- tun daga yadda yake zuwa kamshinsa. Da wannan bayanin, zan iya samar da wani abu sabo.”
Godiya ga iyaye da kakanni
Chef SiA ta yi kuruciyarta a Nijeriya, inda a nan aka haife ta, kafin ta koma Ingila tana da shekara 12. Abinci na burgeta tun can asali. “Ina son yadda nake kallon kakata take girka abinci tun daga farko.
Zuwa lokacin da na tafi zuwa makarantar kwana a Ingila, a lokacin ne na samu masaniya kan fasahar abinci, kuma hakan ya bayar da ma’ana.
Na san tun daga lokacin da nake karama, ina son na zama mai girki,” kamar yadda ta tuna.
Chef SiA na yawan kallon shirin girke-girken abinci a talabijin musamman wanda ake kira “Chopped”, inda da take yawan tunani a kwakwalwarta yadda ake abinci, ganin cewa duk wani sinadari na girki yana kusa da ita.
“Ko kafin na tafi makarantar koyon girki, zuciyata na yawan tunanin abinci iri daban-daban, ina kuma tunanin yadda dandanonsu zai kasance,” kamar yadda ta tuna.
Sai dai abin da ya sa take ci gaba da girkin da kuma ba mutane abinci shi ne jin dadi. “Ina son gano yadda za a hada sinadaren girki daban-daban domin su sa a ji dadi. Idan na yi abinci bai sa na ji dadi ba, ba na bayar da shi kwata-kwata,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.
Chef SiA na yawan amfani da sinadarai na Yammacin Afirka a abincin da take yi. Wannan ne ma ya sa ta soma sana’arta ta abinci, wanda aiki ne na samar da wata al’umma ta musamman ta mutane wadanda ke jin dadin abincin da take yi.
“Na soma aikin Chef SiA Roundtable domin baje kolin yadda nake sarrafa sinadaren girki na Yammacin Afirka,” in ji ta. “Ina da burin kai wannan a idon duniya domin gayyatar mutane su dandana abincina.”
Bukatar yin tsokaci
Ba abin da ke sa Chef SiA nishadi irin bakinta su gano irin abincin da ta zuba musu. “Tun daga tambayoyin da suke yi kan tarihin abincin zuwa kan sinadaren abincin, da yadda bakina ke son sanin meye a ciki, yana sa ni nihsadi,” in ji ta.
Sai dai girka abincin Yammacin Afirka a Landan ko kuma saka wani abu na Turawa a abincinta a Legas na zuwa da kalubale a Legas. Babban kalubalen shi ne samun mahadin abincin wadanda suka dace.
“Ba zan iya bayyana muku adadin yadda na rinka neman scallop a Legas ba ko kuma guava nunanna a Landan.
Abin godiyar shi ne a yanzu ba na fuskantar irin wannan kalubalen sakamakon duniyar ta zama wani karamin wuri inda za ka iya samun abu da tafin hannunka,” in ji Chef SiA.
Jiran da take yi domin ganin yadda baki za su mayar da hankali kan irin abincin da ta samar ya kasance wani lamari da take so.
"Ba zan iya daina kallonsu ba a yayin da suke dandana sabbin nau’in abincina ba: ‘Dunkulalen naman akuya da Zobo mai kayan kamshi’.”
“Abincin da ake sayarwa kan hanya mai suna ‘Asun’, shi ya ba ni kwarin gwiwar soma wannan abincin. Duk lokacin da na zuba wannan abincin ga wadanda ba su taba ci ba, suna yawan yin murmushi,” in ji ta.
“Saboda ba su yi tsammanin zai kasance haka a yadda yake ba, kuma da yake ba shi da girma, sai zuciya ta rinka son kari. Ina son shi!”