Angelique Kidjo ta sha hadin gwiwa wurin yin wakoki da mawakan Afirka da na sassan duniya. /Hoto:   Angélique Kidjo Instagram

Daga Charles Mgbolu

A wannan makon, mawakiya kuma marubuciyar waka ‘yar kasar Benin Angélique Kidjo ta cika shekara 40 da soma wakoki masu tasiri inda ake sa ran gudanar da wani biki na musamman kan hakan a ranar Juma’a mai zuwa a dakin taro na Royal Albert Hall da ke birnin Landan, domin murna.

Bayan kwarzanta ta a matsayin daya daga cikin mata mafi bayar da kwarin gwiwa ta lokacinmu, mawakiyar wadda ta lashe kyautar Grammy sau biyar ta kasance wata alama ta tasirin kida daban-daban wadanda ke tafe da murya mai karfi a duka wakokinta.

An haifi Kidjo a cikin gidan mawaka. Mahaifinta ya kasance mawaki mahaifiyarta kuwa ta kasance ‘yar rawa kuma daraktar rawa ta dabe. A ranar 15 ga watan Satumbar 2021, Mujallar Time ta saka ta a cikin mutum 100 da suka fi karfin fada a ji a duniya.

Angélique Kidjo ta soma waka tun tana 'yar shekara shida. / Hoto: Angélique Kidjo Instagram 

Angelique Kidjo ta tabbatar da cewa ita mai hada kai ce, inda ta hada wakarta da dumbin mawaka na Afirka wadanda suka hada da Burna Boy da Davido da Yemi Alade da sauransu. Wasanta da za a gudanar a birnin Landan, zai samu halartar mawakin nan na Ghana kuma na reggae Stoneboy.

Ta bayyana cewa wannan taron ya kunshi dukkan fitattun wakokinta, wadanda suka samo asali daga kasar Benin a yammacin Afirka. “Saura sati biyu ya rage na tafi Landan! Ba zan iya jira domin murnar cika shekara 40 da soma aikina tare da kowa a Landan,” kamar yadda ta rubuta a shafin X.

Kidjo ta iya magana da harshe biyar: Fon da Faransanci da Yarabanci da Geni (Mina) da Ingilishi. Tana waka da duka harsunan haka kuma tana da harshenta nata na kanta wadanda suka hada da kalmomi wadanda take sawa a wakokinta kamar “Batonga”. “Malaika” waka ce da ta yi da harshen Swahili.

Angélique Kidjo tana gudanar da waka da harsuna daban-daban. / Hoto: Angélique Kidjo Instagram

Shahararriyar mawakiyar nan ta Afirka ta Kudu Miriam Makeba ta kasance allon kwaikwayonta. Kidjo a lokuta da dama ta sha bayyanawa a tattaunawa daban-daban kan cewa ta yanke shawarar bin bayan Makeba ta hanyar amfani da wakokinta domin aika sakonni.

A halin yanzu tana da wata gidauniyua mai suna Batonga Foundation wadda babban burinta shi ne kara inganta rayuwar mata matasa a fadin Afirka.

A daidai lokacin da bikin nata na murnar cika shekara 40 da soma waka ya karato, masoyanta sun rinka aika sakonni na taya murna a shafukan sada zumunta.

“Muna yi wa yayarmu Zogbin murna. Kin kawo mana farin ciki a duniya tare da wakokinki, kin daga matasa a aikin da kike yi. Za mu ci gaba da maki murna a duk abin da kike yi,” kamar yadda Victor Nwaneri ya rubuta a Youtube.

Haka kuma ana sa ran wasu mawakan masu fasaha za su hau kan dandamali tare da Kidjo a lokacin bikin wadanda suka hada da mawakin Senegal kuma marubucin waka Youssou N’Dour da Ibrahim Maalouf da Laura Mvula da sauransu.

TRT Afrika