Mawakan Nijeriya na Afrobeats sun yi kaka-gida a duka bangarorin nau’ukan wakoki wadanda aka gabatar da sunayensu domin lashe Kyautar Grammy, inda Burna Boy yake kan gaba bayan an zabe shi har sau hudu.
An gabatar da sunan mawaki Davido har sau uku domin lashe kyautar ta 2024, wanda hakan ne ya sa ya sake shiga jerin wadanda aka zaba domin lashe kyautar bayan sama da shekara goma.
Mawakin ya wallafa sako a shafin X kan irin dogon hakurin da ya yi domin ya koma cikin wadanda ake zaba domin lashe kyautar: “Zabe sau uku a Grammy! Jinkiri ba hani bane!”
An gabatar da sunan Davido domin zabarsa a rukunin wanda ya fi kokari a waka dangane da wakarsa da ya yi ta ‘Unavailable’ wadda ya yi tare da Musa Keys.
Gabatar da sunan Tyla a karon farko
An gabatar da sunan Tyla a rukunin wakar da ta fi shahara a duniya a wakarsa ta ‘Feel’, inda kundin wakarsa na Timeless ya sa aka aka sake gabatar da shi a rukunin kundin wakoki a karo na uku.
Wakar mawakin na Afirka ta Kudu da aka soma gabatarwa domin lashe kyautar ita ce “Water’ wadda ya yi shi kadai. Shahararrun mawakan Nijeriya wadanda suka hada da Davido da Burna Boy da Asake da Olamide da Ayra Starr duka an gabatar da wakokinsu domin lashe kyautar.
Sai dai Burna Boy ya kasance wanda aka fi gabatarwa, inda aka kira shi har sau hudu a rukunin wakar Afirka da ta fi shahara da wakar duniya duniya da ta fi shahara da kundin da ya fi shahara da kuma rukunin “Best Melodic Rap”.
Dan Nijeriya na farko
Burna Boy ya zama mawakin Nijeriya na farko da aka gabatar da sunansa har sau hudu a cikin shekara guda da kuma mawakin Nijeriya na farko da aka soma zabensa a rukunin “Best Melodic Rap”.
Haka kuma ya zama zama mawakin Afirka na farko da aka gabatar da sunansa a Kyautar Grammy har sau biyar, tun daga 2019 har 2023.
Mawakiyar nan ta Amurka Taylor Swift ita ce ta yi zarra inda ta kafa tarihi a gasar da wakarta ta “Anti-Hero’, wanda hakan ya sa ta zama marubuciya ta farko da aka gabatar da wakarta sau bakwai a rukunin wakar shekara.