A matakin kasa da kasa, Djibouti ba ta cika samun kwararrun yankuna da kuma matsugunan soji ba.
Kasar da ke makale a Gabashin Afirka, tana da iyaka da gabar Tekun Tadjoura, har da Bahar Rum da Afirka da Asiya, da kuma kudancin mashigin ruwan Bab Al-Mandeb, waje mai muhimmanci inda kusan kasuwanci na uku mafi girma a duniya yake ratsawa.
Wannan hanyar sufurin teku ta Bahar Maliya, a tsawon tarihi ta sanya Djibouti zama ba wai kawai mai riba ba, har ma da zama cibiyar musayar al’adu wadda ta gamu da cakuduwar mutane mabambanta, kamar yadda ake iya ji da saurare a cikin wannan wake.
Wani sirri ne da aka gada a Djibouti wanda yake a boye har zuwa shekarar 2019, a lokacin da kamfani mai zaman kansa na Ostinato Records ya zama na farko a kasar da ya samu kyautar kasa ta ajiye bayanan rediyo, wanda yake dauke da dukkan wakokin tsofaffin Djibouti.
Yayin tattaunawa da TRT World, wanda ya samar da kamfanin Ostinato Records, Vik Sohonie ya ce “gwamnati ita ce abar daukar ko nadar bayanan”.
Djibouti na da sha’awar kade-kade sosai. Ba wai kida kawai suke yi ba, suna ma fitar da shi zuwa kasashen waje.”
Tun shekarar 2016, shagon Sohonie da ke New York ya fitar da kunshin wakoki daga Haiti da Cape Verde zuwa Sudan da Somaliya.
A lokacin da yake kokarin neman lasisin wakokin, ya ci karo da kunshin na Djibouti, na wakoki biyu da aka saka a Gasar Grammy ta 2017 wadanda suka kunshi wakokin Somaliya na 1970 da 1980, masu taken Sweet As Broken Dates.
Wannan ya sanya Sohonie haduwa da rediyon kasa, Radiodiffusion-Television de Djibouti (RTD), wadda ta jagoranci mahukunta wajen gabatar da shi ga daya daga cikin ma’ajiyar bayanan Afirka mafi tsada, da kuma gidan masu karanta labarai, Groupe RTD.
Bayan tafiya da wani bangare da aka zaba na wakokin, sai Sohonie ya gano akwai kayan al’adu da dama da za a iya fito da su kuma a yada su a duniya. Bayan shekaru uku ana tattaunawa mai zafi, an bai wa Osinato damar dora wadannan kaya na RTD a yanar gizo da kan faya-fayan garmaho inda aka raba kaset-kaset sama da 5,000 a Gabashin Afirka.
Wani bangare na yarjejeniyar da aka kulla shi ne, a nadi Groupe RTD, misali da yake a raye wanda ayyukansu masu kyau suka samar da bukukuwan da ake yi a gwamnatance.
Bayan wa’adin kwanaki uku, da halin da dakin watsa shirye-shirye na gwamnati na tafi da gidanka yake ciki, sai aka saki rukunin wakoki na farko mai taken “Dancing Devils of Djibouti”,-Wakokin farko na kasar da aka fitar ga duniya.
Sohonie na da ra’ayin cewa wannan sauti da aka mika shi ga masu sauraro, hanya ce sabuwa da za a fahimci tarihin duniya.Shin dukkan anyoyi na kai mutum Rome ko Gabar Tekun Tadjoura?
“Daga abun da wakokin ke fada min, mutane da dama kuma daga bangarori daban-daban sun cakudu da juna a wannan waje.”
“Idan muna kara shiga Gabashin Afirka, za mu ci gaba da samun kwarin wadannan wakoki, kuma mu gane ya kamata su zama a tsakiyar duniyar wake-wake, kan rediyoyi da injinan sauti.”
Sautin waka don gina kasa
A wajen masana tarihin wake-wake, Afirka bayan samun ‘yancin kai tarihin wake ce. An zalunce ta a lokacin mulkin mallaka, sai bayan samun ‘yancin kasashe suka tallafa wa wake-wake tare da yin sassaucin kashe kudade, duk a wani bangare na “Aikin kawar da tasirin mulkin mallaka”.
‘Yan siyasa ba su yi amfani da mawaka don yada farfaganda kawai ba, har ma da samar da alfahari ga kasa da al’adu.
Bembeya Jazz National na kasar Gini, Super Eagles na Gambiya da Orchestra Afrisa International na Congo misalai ne kadan.
Haka kuma, shugabannin Djibouti sun yi amanna da cewa kade-kade na bayar da amo ga lokacin bayan samun’yancin kai, wanda za su iya hade kan kasar da ke da rauni saboda kawo karshen mamayar Faransa a 1977.
Tabbas, sunan 4 Mars-Quatre Mars a yaren Faransanci-na nufin 4 ga watan Maris (1977), wanda suka kafa (RPP), jam’iyyar da ta yi mulki tun daga 1979.
RPP ta samar da mawaka da wakoki da dama don kowacce hukuma ta gwamnati. A matsayinsu na mawakan gwamnati, 4 Mars sun zama mawakan kasa domin samar da hadin kai.
A fannin wake, mutum zai iya rajista da sunayen mawaka biyu, na Djibouti da na Somaliya da suke kwaikwayon karin wakokin Bollywood.
Bayan da Ostinato suka hau yanar gizon kundin ma’ajiyar bayanan kasa, sai aka samar da jerin ajiyayyun wakokin Djibouti, tare da kunshin wakoki 3, wanda kowanne zai tattaro wakoki daga sassan kasar daban-daban.
An saki kunshin wakokin “Super Somali Sounds from the Gulf of Tadjoura” a watan Fabrairu, an kaddamar da shi da mambobi 40 na kungiyar supergroup ta Somaliya ta 4 Mars, jerin wakokin na kunshe da wakoki da bidiyon raye-rayen da aka yi a tsakanin 1977 da 1994.
Kamar mawakan “Groupe RTD”, 4 Mars ma a wakokinsu sun nuna kwaikwayon karin sautin wakokin Somaliya wanda aka dakko daga wasu al’adun daban ala tilas, wanda suka kutsa gabar tekun Djibouti tsawon shekaru.
Idan kuna sauraron wakokin, zaku ga karin sauti kamar haka: 4 Mars na amfani da fasalin waka na Sudan, karin sautin Masar da Yaman, kayan busa na China da Mongoliya, kayan kida na Amurka, gogen Turkiye, amon Bollywood da ya yi tasiri a Somaliya da kuma hawa da saukar wakokin Dhaanto na Somaliya.
Sohonie na da ra’ayin cewa wannan sauti da aka mika shi ga masu sauraro, hanya ce sabuwa da za a fahimci tarihin duniya.Shin dukkan anyoyi na kai mutum Rome ko Gabar Tekun Tadjoura?
“Daga abun da wakokin ke fada min, mutane da dama kuma daga bangarori daban-daban sun cakudu da juna a wannan waje.”
“Idan muna kara shiga Gabashin Afirka, za mu ci gaba da samun kwarin wadannan wakoki, kuma mu gane ya kamata su zama a tsakiyar duniyar wake-wake, kan rediyoyi da injinan sauti.”
Sautin waka don gina kasa
A wajen masana tarihin wake-wake, Afirka bayan samun ‘yancin kai tarihin wake ce. An zalunce ta a loakcin mulkin mallaka, sai bayan samun ‘yancin kasashe suka tallafawa wake-wake tare da yin sassaucin kashe kudade, duk a wani bangare na “Aikin kawar tasirin mulkin mallaka”.
‘Yan siyasa ba su yi amfanii da mawaka don yada farfaganda kawai ba, har ma da samar da alfahari ga kasa da al’adu.
Bembeya Jazz National na kasar Gini, Super Eagles na Gambiya da Orchestra Afrisa International na Congo misalai ne kadan.
Haka kuma, shugabannin Djibouti sun yi amanna da cewa kade-kade na bayar da amo ga lokacin bayan samun’yancin kai, wanda za su iya hade kan kasar dake da rauni saboda kawo karshen mamayar Faransa a 1977.
Tabbas, sunan 4 Mars-Quatre Mars a yaren Faransanci-na nufin 4 ga watan Maris (1977), wanda suka kafa (RPP), jam’iyyar da ta yi mulki tun daga 1979.
RPP ta samar da mawaka da wakoki da dama don kowacce hukuma ta gwamnati. A matsayinsu na mawakan gwamnati, 4 Mars sun zama mawakan kasa domin samar da hadin kai.
Sohonie ya bayyana cewa “Manufar wadannan wake-wake ita ce a saka tarbiyya da halayyar gina kasa daga tushe a zukatan jama’a. Yadda za a samu sakon ya isa ga al’uma tare da hade kawunansu, cikin zaman lafiya da walwala.”
“Idan kuka kalli sunayen kunshin wakokin 4 Mars, za ku ga wadannan abu uwa ne kawai suke yawo a cikinsu, suna kuma taimakawa wajen sun dasu a zukatan mutane.”
Idan aka yi kallo na tsanaki a rukunin wakoki 14 dake kunshin, za a ga suna magana ne a kan Kasa, Mulki, Bi Dokoki, Kauna, Godiya da Sannu Zaman Lafiya! Katafaren wajen wasannin nishadi mai wajen zama 800 ne wajen cashewar 4 Mars a koyaushe.
Sohonie ya tattauna cewa “A wajen Yammacin Duniya, suna watsi da hakan saboda farfaganda ne. Amma a ma’anancen sabuwar kasa da al’umu da kawunansu suke a rabe, ku yi tunanin me “farfaganda” ke nufi.”
“Manufa ce babba don gina kasa”
Bayan kasancewa wani bangare na gwamnati, daya daga cikin dalilan da suka sanya wake-waken Djibouti ba su fita zuwa kasashen waje ba shi ne, adadi kadan da mawakan 4 Mars suke da shi, kula da su da mawaka, makada, jarumai da makida ke yi. Kawai an taba samun lokacin da Shugaban Libiya Muhammad Gaddafi ya kai su Tarabulus a 1991.
Ya zuwa 1991, rabuwar kai tsakanin kabilun kasar Djibouti biyu ya tsananta, tsakanin mafiya rinjaye Somali Issa da marasa rinjaye da suka fito daga Itopiya Afars, hakan ya sanya aka fara yakin basasa har zuwa 1994.
Duk da dai yakin bai munana kamar a kasar Somaliya dake makotaka da su ba, amma mawaka sun yi kokarin wajen hada kai da kawo zaman lafiya a kasar.
Sohonie ya kuma ce, Sakamakon yakin, 4 Mars da tasirinsu ya fara raguwa a shekarun 1980 a lokacin da gwamnati ta rasa kudade, sai suka zama ba kamar yadda suke a baya ba.
Amma bayan an dawo da dimukradiya, sai sabon kundin tsarin mulkin Djibouti ya mayar da mawakan jam’iyyun marasa abun yi, suka zama cibiyoyin kasa.
Masu adana al’adu masu kyau
Ma’ajiyar bayanan RTD ta salwanta skaamakon gobara da ma’aikatan da ba su san meye aikinsu ba.
Kayan da aka adana su tun 1977 kuma babu wata hukuma daga kasar waje da ta taba ta, suna nan a waje da yake da na’urar sanyaya daki tsawon awanni 24/7, kuma karkashin matasa masu gadinsu.
“Bayanan na da yawa,” inji Sohonie ”Sunayen wakoki da mawaka ba su da karshe. Kuma ba wakokin Djibouti ba ne kawai, har da na wasu mawakan daga yankn,kamar Itopiya da Sudan da suka zo suka yi wakoki a kasar.”
Sohonie na da ra’ayin yadda ‘yan Djibouti suka nuna juriya wajen adana kayan kasa, na nuni da muhimmancin ajje bayanan da aka gada, kuma wani abu da za a yabawa shi ne yadda hakan ya kasance a lokacin da kusan kaso 95 na al’adun Afirka na a wajen nahiyar.
Ya ce “Suna amfani da karfin ikon kasa wajen kula da wakokinsu,” “Su ke bayar da izini ga wanda zai yi amfani da wakokinsu.”
Kuma wadannan abubuwa na da wahala. “Sun rufe mu da mukulla. Ina da wan, ma’aikacin al’adu dae fada min abun da akeyi da wanda ba a yi.”
“Hakan na nuna yadda bayanan da ba su da alaka da mulkin mallaka suke. ‘Yan Afirka ne ke kula da al’adu da wakokinsu.”
A ra’ayin Sohonie, abun ban sha’awa ne a yiduba zuwa ga abun da gwamnati ke tunani game da raya al’adu da yadda za a tattauna da mahukunta da sakin wakoki, kamar yadda ake yi a kasashen da suka ci gaba.
“Kun ga yadda ake tafiyar da aiyukan hukumomi, yadda shugabanci yake aiki, abun da yake aiki da wanda ba ya tafiya daidai,.”
Ya hada kokarin samun damar isa ga bayana da suka taba samun kyaututtuka tare da halayya mai sauki a sama; abubuwa da suke tafiya a hankali da suka baiwa masu zuba jarin Turkiye da China damaa kasar.
Habakar China da Turkiye, wanda duk suna da sansanonin soji a kasar, ya sanya Beijing da Ankara samun wani matsayi cikin kankanin lokaci.
Sohonie ya yi nuni da yadda matasan Djibouti suke kallon Turkiye a matsayin wajen da ake bukata don a rayu a cikinsa, wani abu da ake iya gani na sauyawar tunaninsu daga Yammacin Duniya.
A tarihi, akwai dangantaka da ake farfado da ita a lokacin da karfin Yammacin Duniya ke raguwa.
China ta taka muhimmiyar rawa wajen farfado da kayan raya al’adu na Djibouti. A kwanan nan ta sake gina dandalin nishadi na kasa da ya lalace, kuma ta horar da ma’aikatan RTD kan fasahar zamani a jami’ar China.
Sohonie ya kara da cewa “A lokacin da muke aiki tare da ma’ajiyar bayanan, gwamnatin China kuma na ginawa Djibouti dakin karatu da kuma babban ginin ma’ajiyar bayanai da aka kammala aikinsu a shekarar da ta gabata.”
Hakan ya sanya shi tunanin dalilin da ya sanya kasashen Yamma ba su taba kokarin aiki da bangaren raya al’adu na Djibouti ba.
“A shekara guda, Ba’indiye da dan China suka je kasar, suka habaka al’adar kasar, suka yada wakokinta, suka kuma gina musu sabon gini.”
Samun ma’ajiyar bayanai mara alaka da mulkin mallaka
A karshe dai, bayanan Djibouti sun bayyana hanyar aiki da ma’ajiyar bayanai a kudancin duniya,abun da Sohonie ya bayyana a matsayin “Tsarin Ostinato”.
Ya ce “Ba wai muna shiga ciki ba ne kawai, mu zamanantar tare da tafiya- muna son samar da dangantaka mai tsayi.” “mun yarda da mika fasaha da wani wajen zuwa wani, da kuma yada ilimi, ta yadda za su adana wakokinsu a yanayi mai kyau.”
Gidan rediyon kasa da ba shi da wajen kunna wakoki da zai ba su damar zamantar da wakokin. Ba a cika samun alkawurra daga Kungiyoyin Yammacin Duniya da dama da kungiyoyin bayar da tallafi bam, idan ma an taba samu din.
A wani bangare na yarjejeniyar zamantar da ma’ajiyar wakokin, Ostinato sun aika da wata na’urar nadar bayanai da aka yi wa kwaskwarima ta yadda za a ci gaba da aiyukan adana bayanan ko da bayan masu taimakawa sun tafi, hakan zai hana a dauke wani abu na al’ada zuwa wani waje.
Abu ne da Sohonie yake ji cewa masu nadar bayanai na Yammacin Duniya ba sa fahimta yayin aiki da wakokin kasashe masu tasowa.
“Ba kawai suna amfani da wake-wakensu ne a Berlin da Paris don mutane su yi rawa ba, suna kokarin rike hujjar sabon tarihi; sabon tarihin da ba shi da alaka da Turai, tarihi mara alaka da Turai dake nuna al’adun kudanci zalla.”
Asali dai, Sohonie na kallon wakoki a matsayin kafar bayar da labari ta hanyar koyar da sabon tarihi, wanda hakan ne ya sana shi gudanar da aiki kan ma’ajiyar bayanan.
Ya ce “Idan muka yi amfani da wakokin, za mu iya amfanar da kawunanmu da su wajen assasa tarihin Afirka, Asiya da Latin Amurka ta hanya mai kyau tare da dasa karfin gwiwa a zukatan kasashe don su kalli wakokinsu a matsayin abubuwan da za a dinga bukukuwansu a fagen kasa da kasa.”
To ta hanyar sauraron bayanai game da tarihin Djibouti, Sohonie na fatan za mu zuba idanu don ganin habakarta a nan gaba.