Daga Charles Mgbolu
Murya mai karfi kuma mai dadin sauraro a salon wakokin Afrobeats a yankuna masu magana da harshen faransanci tana samun karbuwa tare da jan hankalin masoya a duniya.
Mawakiyar Kamaru Libianca ta yi fitowar bazata a watan Mayun shekarar 2023 bayan da wakarta mai taken 'people'' ta shiga jerin wakoki 100 da suka yi fice a ''Billbord HOT 100 Chart'' inda wakar ta kai lamba ta 39 sannan ta samu yabo da karbuwa a wajen masoya wakokin Afirka.
Kawo yanzu, kida ko wakokin Afrobeats sun fi samun rinjaye a bangaren mata mawakan Nijeriya, inda mawaka kamar su Tiwa Savage da Ayra Starr da Tems suke kan gaba a wannan bigiren.
Kasar Kamaru ba ta da wani tsarin salon Afrobeats a wake-wakenta, amma da fitowar Libianca labarin ya fara canjawa, tare da gamsar da 'yan kasar wadanda suka yi maraba da hakan.
"Muna godiya da sanya Kamaru cikin wannan taswirar " a rubutun da @ArthurTsar ya rubuta a shafin Libanca na X.
A watan Satumba, aka zabi Libianca tare da Burna Boy da Davido da Wizkid da Fireboy DML da Rema da kuma Ayra Starr a sabon jerin lambobin yabon bidiyo na MTV.
Duk da cewa a karshe mawakin Nijeriya Rema ne ya lashe kyautar, masoya a shafukan sada zumunta sun yaba mata kan yadda ta dasa Kamaru a idon duniyar wakoki da kidan Gen Z (sabon zamani) na nahiyar.
Libianca dai ta ci gaba da lashe kyautar gwarzuwar mawakiyar Afirka ta Tsakiya a Kyautar HipTV.
Kazalika babbar manhajar watsa wakoki Vevo ta sanya ta cikin jerin 'Mawakan Duniya da za'a zuba ido akansu a 2024'.
An yaba wa Labianca musamman saboda sautin muryarta da kuma sakon da wakarta ke dauke da shi, la'akari da yadda Afrobeats ya shahara wajen nishadantarwa.
"Duba da ire-iren abubuwan da suke faruwa a duniya a yanzu, wannan shine abin da muke bukata," a cewar wani daga cikin masoya Mollymusic, a kafar Instagram.
An saurari wakar Libianca ta 'people' sau miliyan 288.7 a kafofin sauraron wakoki na duniya sannan an kalla bidiyon wakar a fiye da miliyan 200 a kafar Youtube.
An haifi Libianca a shekara ta 2001 a Minneapolis na kasar Amurka, amma danginta sun kaura zuwa Kamaru lokacin tana 'yar shekara hudu.
Daga baya ta sake koma wa Minneapolis lokacin tana shekaru 13, inda a hankali ta fara kafa kanta a fagen wake-wake.
Gogewar da ta samu a wakokinta ta biyo bayan tarihin zamanta a Amurka da Afirka, inda ta hada salon wakokin Amurka da na Kamaru.
Libianca ta ce a yanzu ta fara sauke kayan dake kanta, sannan mayotanta su zuba ido zuwa gaba.
''Ba zan iya jiran nuna muku abubuwan da na sa a gaba ba; ba zai dade za ku gani..'' ta rubuta a shafinta X.