Wakokin Wegz na daga cikin wakoki 10 da aka fi saurara a Masar.

Daga Charles Mgbolu

Kamfanin Spotify da ke da jiyar da waƙoƙi ya ce wakoki daga Arewacin Afirka sun habaka da kaso 170 a tsakanin 2019 a 2022.

Bayanan da aka fitar a watan Nuwamba a watan Nuwamba sun hada da alkaluman sauraron wakoki daga ƙwararrun mawaƙa masu basira daga kasashen Gabas ta Tsakiya.

A Arewacin Afirka, wakokin da aka fi sauraro sun hada da na mawaƙan zamani na Masar da na al'adun Amazigh na Maroko.

Damar da Spotify ke gabatarwa ta taimakawa dimbin wakoki da ke fitowa daga Arewacin Afirka inda kamfanin ya ce "hakan na bayyana kaifin basirar yankin da yawaitar matasan Larabawa da ke sauraro."

Akwai sabbin mawaka da kuma masu samun shuhura a wakokin zamani na kasashensu da kuma wakokin da matasa ke samarwa wadanda masu sauraren Gen-Z suke ƙarfafawa gwiwa.

Wadannan mawakan na gwamutsa salon wakar yankunansu da na duniya, suna hada wa da kida da waka da ba sa dawwamar da su a matsayin mabiya al'ada guda daya.

Ba lallai su zama sun yi shuhura kamar manyan mawakan Afrobeats na Yammaci da Kudancin Afirka ba, amma kuma sun yi nasara a bangarensu.

A jerin sunayen mawakan, ga wasu da muka tsakuro muku daga Arewacin Afirka, ana sauraron wadannan mawaka a manhajoji daban-daban.

Wegz

Sunan Wegz na gaskiya shi ne Ahmed Ali, jarumin fim ne a Masar kuma waƙoƙin zamani.

Waƙarsa ta Dorak Gai da ya fitar a 2020 ce ta janyo masa shuhura, inda a watanni biyu mutum miliyan 24 suka kalle ta a Youtube.

Mawakin gambara Wegz ya yi casu a wasu wuraren da suka fi kowanne matsayi a duniya. 

Shi ne mawakin da aka fi saurara a 2022, inda ya rike wannan kambi har sau uku a jere.

Duk da cewa yawan sauraren wakokinsa na 2023 bai bayyana ba, uku daga cikin wakokinsa na daga cikin 10 da aka fi saurara a Masar, inda wakar Al-Bakht ta ke kan gaba, sai kuma B3ouda Ya Belady da Keify Keda suka zo na hudu daga cikin goman.

ElGrandeToto

Taha Fahssi dan shekaru 27 ya yi shuhura ne bayan wakarsa ta ElGrandeToto ko kuma Toto.

Mawakin dan kasar Maroko na yin wakar gambara a yaren Darija (Larabcin gargajiya na Maroko), Faransanci da Ingilishi.

ElGrandeToto na daga cikin mafi shawarar mawaka a duniyar Larabawa a yau.

Shi ne mawaki da aka fi saurara a 2021 a manhajar Spotify a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka, inda yake da sama da sauraro miliyan 135 a kasashen duniya 178.

A 2022, Toto ya zama mawaki na biyu da aka fi saurare bayan da Wegz ya yi dabarar hada wakensa da mawakin Nijeriya Ckay a wakar Love Nwatiti da aka fitar a 2019 da ke da masu kallo miliyan 123 a YouTube, wanda hakan ya habaka shuhurarsa a yankin.

Amr Diab

Amr Abdel Basset Abdel Azeez Diab mawaki ne dan kasar Masar, mai rubuta waka kuma jarumin fim. Ya kafa kansa a duniya a matsayin jarumin nadar wakoki kuma marubuci.

Amr Diab ya fito a babban allon talla na World Album Charts

Ya shiga kundin tarihi na Guinnes World Record a matsayin mawakin da aka fi sauraro dan Gabas ta Tsakiya, kuma sau bakwai a jere yana lashe Kambin Wake-Wake na Duniya, sau biyar yana lashe kambin Platinum Records, ya kuma lashe kambin wake na Afirka sau shida.

A 2022, ya zama dan kasar Masar na farko da ya samu masu sauraro sama da biliyan daya a manhajar sauraren wakoki ta Anghami.

Marwan Mousa

Marwan Moussa mawaki ne da ya fito daga Masar, kuma ya yi shuhura da wakarsa mai suna Sheraton.

An kalli bidiyoyin Marwan Moussa a YouTube sau miliyan daruruwa.

Moussa ya fara waka a matsayin mai samar da waka kai, amma daga baya wani abokinsa ya ja hankalinsa kan ya fara wakar gambara

A 2023, wakarsa ta Lost Compass da aka saki a watan Yunin 2022, ta samu masu saurara sama da miliyan takwas.

A watan Janairu, ya lashe kambin mawaki matashi a Afirka, sannan ya lashe Kambin Mawakin Gambara na Afirka (Arewacin Afirka). Kuma shi ne mawaki na uku da aka fi saurare a Spotify a 2022.

Tagne

Tagne na daga cikin mawakan hip-hop na Morokko da ke kan ganiyarsu.

An haifi Tagne dan shekara ashirin da bakwai a Casabalanca, daga uwa 'yar Maroko da mahaifiya 'yar kasar Kamaru. Ya kware da shirya kansa tun yana karami da yin casu a bainar jama'a.

A 2020, ya zama dan kasar Maroko na farko da ya fara gudanar da casu a kasar. Tagne na da masu sauraro sama da 600,000 a kowanne wata a manhajar Spotify, ta hanyar wakarsa ta Ma Colombe: Gambizar Wakokin Morokko da suke da masu sauraro sama da miliyan 37 a manhajoji daban-daban na sauraren wakoki.

TRT Afrika